YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Ahj Salihu ya iso kano da kyar ya gane gidan su suwaiba….
.
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Page 30:
Alhj Salihu ya iso gidan su Suwaiba da wajen bayan la’asar kadan, dai dai su kuma suna dawowa daga gidan Juwairah, daga nesa ta bayan da ya juya Suwaiba ta gane shi, ya rasa dan aike, kuma yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce karba za a mai, shin dalilin kafa kai da yai a jikin motar, wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ke bin kuncin shi, ga rashin abokin shi da yai, kuma kusan a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, what if shima ya biyo shi? Ga Suwaiba da iyayen ta da ‘yan uwan ta, maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake, he was trying to walk away, when he hered her voice, calling out his name in a passionate way” Baby? kai ne? Kai ne da gaske nake gani? What are u doing here?” Qarasawa tai da gudu ta fada qirjin shi tana kukan missing din shi da tai, shima rungume ta yai kamar wani zai kwace mai ita, gyaran murya Salma tai masu,” Adda a waje kuke fa, kn san halin mutane, ba za ai tunanin mijin ki bane, za a fara qananan maganganu” janyewa sukai daga yanda suke taja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take, ina nata mijin? Ya akai suka rabu yau? Bayan ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da tai gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar tata sukai ciki, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi daya ba nata mijin abun ya qaru mata, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa taqi komawa, what could possibly happen to him? Sun riga sunyi Sallah gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Abban su sukai Salihu yazo ga kuma a yanayin da suka gan shi, a da Abban was furious, amma da Mama Bilki ta taishe shi, akan ya tafi cikin nutsuwa ya bude ma Salihu zuciyar shi yaji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo, ta bashi goyon baya ya mao duk abin da yaso, kada kai yai cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara, Sallama ya mai ya miqa mai hannu amma Salihu ya noqe, ya durqusa qasa yana mai kuka mai ban tausayi,” Abba ni mai laifi ne ba a wajen ku ba har a wajen Allah, babban mai zunubi ne,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda nai wa Suwaiba, ka yafewa abokina diban jinin Saudat da yai domin ya mutu, a dazu kan na iso nan, ta hanyar hatsarin mota” wani qarar kwanuka da qarar Saudat ne ya dawo da su daga maganar da suke, faduwa tai a wajen a sume, da gudu Abban su yai kanta, ya daga ta yai ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata, a hankali take bude idon ta, ya sauka kan Salihu da ya shigo ba izini, kuka ta saka ta kai mai naushi a baki, ” mugaye azzalimai, kashe shi kuka ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dade, shine kuka kashe shi?” ” Saudat you have to calm down, u get it all wrong, ni da kk gani ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shigeni, amma Kalla ya qi, ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba, na mai wa’azi da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita yai hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta…….” ” Stop it ! Stop it !” Saudat ce cikin tsawa take hana shi qarasawa, tare da fashewa da kuka mai ban tausayi, a nan dai ya qarasa labarta masu komai daya faru har a wajen Oga Zaks, Goggo dake gefe da ta fito cikin bala’i taji komai, sai jikin ta yai sanyi, ta koma kwallar tausayin yaran ta, ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taba sanin Saudat na son mijin ta haka ba, kawai ta gudar wa mutuwa ne sai yau, daga ta Mama Bilki ta sa Abba yai ya kaita dakin su, ya kwantar da ita, kuka kawai take, Mama Bilki ce ta shiga bayan Abban su ya fito” Saudat ki hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addua, tinda bai sake ki ba kk qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon wata 4 (hudu) da kwana 10 ( goma) dan haka har abada mijin ki na buqatar adduar ki, baya buqatar kukan ki, kinji” ta qarasa tare da shafa kanta, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa saga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata addu’a, mama Bilki na amsawa, haka har ta samu sauqin zuciyar ta itama, Salma na maqale tana tina nata mijin tana hawaye, ga tausayin Addar nata da ya dame ta. Bayan yayi alwala yai salla ne ya kuma ci abinci Abba ya ce suje gidan Yayan shi,( gidan su Juwairere) tafiya can sukai, a motar da ya zo da ita, sukai wa Yaya Balarabe bayanin komai, ya gamsu sannan ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer su koma Abuja sai su su zauna a bangaren su, Abba godiya yai wa yayan nashi, ya koma gida, in da Yaya Balarabe yace, zai fara koya mai ilimi na addini dan ya na da qarancin shi, godiya yai sosai, Nafee Abban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida mai yaloluwar katifar da wankakken zanin gado da pilo, sai yar sallaya, da buta, da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe, Abban su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya yai ta musu kamar zai kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi.
Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah, anyi suna, suna ya qayatar, dan Jabeer ya yi qoqari sosai, ga akwati nan biyu da yai ma mai jego da jaririya, daya babba daya qarami, gobe suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer, sun gama kwasar duk wani abu da zasu dauka, sauran kayan zata barwa Addan nata da mijin ta, a haka taje gida taiwa Saudat ta’aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole, da kyae suka lallashe ta, sai da taga Jabeer ran shi ya baci da kukan ta sannan ta hakura, sun dawo gida bayan Isha’i Nafee idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innar mu ma ba a barta baya ba wajen matse kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da sukai a baya, Baba Balarabe ma jikin shi sai da yai sanyin rabuwa da Juwairah, dan yarinya ce mai shiga rai matuqa, da kyawawan halayen ta, da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi.
Washegari da sassafe, Jabeer da Juwairah dauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar Jabeer zasu tafi, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace” My little sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ran da fa Saudat zata fita takaba ranar za, a fara bikin ki ko kin manta, dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta haihu kafin nan zamu zo, kinji Sweery,” hawayen ta ta share, tai masu adduar tafiya lfy su da samun sa’a da nasara,Innar mu sa Baba Balarabe ma haka, sai mijim Adda Suwaiba dake gefe shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar sukai gaba, cike da kewar juna, Salihu gaba daya ya canja, fatar shi tai duhu, tumbin nan ya sauka,sai kyaun shi ya fito, ashe yana da kyau yaci kudin haram ya gina tumbi tulele ga kumatu kamar nawa( lols just kidding nawa mai kyau ne????????)???? tausayin shi ne ya kama Baba Balarabe ganin yanda ya koma a qasan ran shi kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wanjen gwanjon su da shi ne? Bayan su Innar mu sun shiga gida ne ya same shi ya mai wannan tayin, cikin jin dadi ya amsa da zai yi ko meye in dai halal ne ba damuwa, qasa yai da murya da kan shi” to Baba ai ban da jari kuma” ” kar ka ji komai, akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani” godiya yai ta zubawa kamar me, Baba Balarabe da yaga ba zata qare ba dariya yai ya shige cikin gidan ya bar shi anan,.