YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Nafee tace a fada maku tana godiya da zuwa biki, amma ‘yan maermue group da suka je sukai ta dibar kaji suna boyewa, su raba da sauran wanda basu je ba, musamman Mum Sultan Bizzy Aisha, da Roumio, a canja hali malamai????
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

      BY HAERMEEBRAERH

I dedicated this page to all my Kebbi state people, i heart u guys, u are wonderful, and kind, wish to came back soon inshaa Allah, Missing you bahut bahut❤❤❤❤

Page 32:

‘Yan kai amarya basu tafi ba sai wajen qarfe 12 na rana, Innar mu ta sha kuka, Nafee mai son gida kamar me, ranar tun tana kukan sai da yakai ta gaji ajiyar zuciya kawai take lodawa, sai kace wacce za ai wa auren dole, kowa sai da ta bashi tausayi, Salma ba ta samu zuwa ba haka ma Suwaiba, Saudat ita aka wakilta a madadin su, sai Mama Bilki, wadda cancanta ce ta sa aka zabe ta a masu zuwan, tinda ita Goggo Sarai har yanzu bata da tinani masu kyau a kanta banda wauta tai mata yawa, sai girman shekaru da jiki kawai ta aje, tana jin zafin rashin tafiya da ba ai da ita ba amma haka ta jure, Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata, tayi kuka kamar me, amma haka ta hakura ba yanda zatai, wasu mata suka dauka biyu daga bangaren su Abban Suwaiban wato Goggo Karima da Goggo mero, sai ta bangaren Innar mu, suma biyu, Innar Fateema, da Inna Aishe, sai wata aminiyar Innar mu wato Baba Maryam, ba su isa kebbi ba sai takwas na dare, gaba dayan su jikin ta qaura yai la’asar, tun Nafee na irin abun amaren nan a mota tini ta janye mayafin a fuska ta sake, tambaya ko tafi nawa tana ma, abokin angon dake tuqi, dan motar daga ita sai abokin angon dake tuqa su sai wani a gefe sannan ita da angon, mota uku sukai, janyo ta mijin ta yai jikin shi ta kwace a kunyace tin suna Gusau, da wahala tai wahala da kanta ta dora kanta jikin shi ta sha baccin ta, ko da ta farka ta zaci zataga sun kusa isa amma taji shiru, kai na taqaice maku sai da Nafee ta matse kwalla, tinanin ta daga Kebbi Nigeria ta qare,lokacin da suka isa ana ta kiraye2n sallar isha’i ne, suna zuwa gidan dake unguwar Alieru Quaters, a bangaren Three bed rooms a nan aka aje ta, fasalin nasu gidan daban ne dana sauran, ya tsaru iya tsarin zamani, kana kallo zaka san gidan masu hali ne, yan uwan ta kam sai san barka suke, da mata addu’ar Allah ya zaunar, kwanan su biyu aka tashi juyowa da su, Saudat kuka tasa data tuno hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya” a gaskiya zan fada ma Umar farouq ya shirya matat shi raguwa ce” ai tana jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga mai harara” inji wa? Ni kar ka wani fada mai mu tafi” dariya aka saka dukka wajen banda Nafee da take rabe a gefen mijin ta tai kalar tausayi, ai ko suna sa kai ta fashe da nata kuka, bayan sun fita ne suma suna cike da tausayin ta angon ta ya dauke ta cak yai ciki da ita yana lallashi, su Saudat sun kama hanya sun baro nafi, wajen mijin ta mai matuqar so da kulawa, tare da tausayin matar shi, dake tashin qarfe bakwai da rabi sukai sun iso kano qarfe wajen uku na rana ne kowa sai da aka aje ta gidan su, drivern daya kawi su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, ” ba daban Farouq ya rigani ba kuma yana matuqar son ki, tabbas dana kawo kaina nima, amma ba zan iya tafiya bam sanar dake sirrin dake raina ba, na kamu da son ki a kwanakin nan da mukai kusan wuni a tare daku, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuria mumina saliha” taji dadin fahimtar shi da kuma yabawa da hankalin shi sosai dan haka ne ma yasa tace mai,” na gode sosai da siyayyar ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya,” murmushi sukai sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi.

Kwana biyar tsakani, bayan waya da musayar saqwanni dake tsakanin masoyan hudu, sai gashi wata lahadi da yamma, wasu dattijai suka zo gidan Abba Baballe, da nemawa Farouq da Salmanu auren su Saudat din, a wasu maka2n motocu suka zo, wanda yasa Abba jin tsoron kar a maimaita yar gidan jiya fa, amma saka makon bayani da suka samu shi da Baba Balarabe, da kuma shaidu sun tabbatar da cewar tabbas mutanen kirki ne, a nan take suka roqi arziqin a daura auren in ba damuwa, saboda ba a kusa suke ba, kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne, sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Abba Baballe sawa yai a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba, nan take aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Salmanu, akan sadaki dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Salmanu zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izini, su Abban Suwaiba sun yarda amma sun qara da cewa in ba takura, suka jaddada masu, cewa shi Salmanu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika, Abban Suwaiba yaji dadin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjeje niyar sanda Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su ayi tarewa.

Bayan wannan daddadan labarin ya iske su Juwairah ne ta roqi Jabeer akan ya barta har tagama batun tarewar Yan uwan ta kan ta koma, ya amince amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aiki, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai su koma tare, kudi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi, tin kan tafiyar kuma sai tai tajin ba dadi zai tafi ya barta, bata son abin da zai raba ta da mijin ta , musamman wannan bata san kwana nawa ba zai dauka, shima gaba daya bai som rabuwar tasu amma dole ya qarfafa mata guiwa , haka suka rabu kowa na kewar dan uwan shi. Ta dawo daga raka shi ne taji wayar ta na ringing dake kan fridge din ta, dauka tai taga Nafee ce, bayan sallama da gaisuwa ne tare da tambayar bayan rabuwa Nafee tace” matar yaya kunyi min mntuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba” ” Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, ba damuwa ai kinga yanda na hada maki wancan, ki hada wani wannan na ba su Adda Saudat, keee an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu” cikin murna Nafee ke addu’a, bayan gama murnar ne tace” nifa matar Yaya na manta wasu abubuwan dan sake fadan mana pls” ” kai Nafee ko angon ya kwashi romo har da basirar ki ne?” Dariya sukai Nafee tace cikin shauqin son mijin nata” matat yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin maza” ” Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama fada maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama.zama yar hannu ma abin ki, ” dariya sukai tayi kafin Juwairah ta lissafa mata kayan hadawar da suka qunshi” kanin fari kadan zaki saka ba mai yawa ba saboda masu magungunan gargajiya sun tabbatar da shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kadan sai citta mai dan yawa, minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan fa da wannan ruwn raken iya adadin yawan dakk so da shi zaki amfani, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga yai kauri kadan ma’ana bai irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka yai kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an bata zuma, na ba su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha” ” na gode matar yaya sai an jima ki shan fan bbyna, ina gaida yaya” nima ina gaida angon ki” .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button