YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Da wajen qarfe goma sun gama shirin tafiya sun hada akwatin kayan Abrar da komai Sallama suka je yi ma su Innar mu, Su suwaiba da Salihu suka shigo, cike da fara’a suka gaggaisa, Abrar na ganin Suwaiba ta ko hau qoqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu da Abrar din ta dauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take, irin na yara, wata kwalla Juwairah ta share ta son yar ta ta amma tabbas haka zata bawa Addan nata ita, miqa mata akwatin yarinyar tai tace” Addan daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer ya miki kyautar ta gaba dayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga tanan, dama ita ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kk bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya raya maku ita da imani,” ta ja baya Suwaiba da Salihu tare da Innar mu Baba Balarabe ne ya katse shirun” a gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri’ar mu baki daya, tabbas Qanina da Bilkisu sunyi matuqar qoqari na baki tarbiyya managarciya, wannan shine dalilin da ya sa kk zama haka, Allah ya muku albarka, kai ma Jabeer naji dadin wannan kyauta da kai, duk da nasan ita zata saka ka, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba,” godiya sukai innar mu tace” Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau, yanda zata tashi abar so ga kowa” Suwaiba da Salihu kuwa kukan farin ciki ya hana su magana sai gyada kai, wanda hawaye ke kwarara a idanun su, zuwa tai ta rungume qanwar tata, da durqisawa a gaban Jabeer, dago ta yai ya na buga bayan ta, yana kada mata kai, Salihu ne ya je ya miqa mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna” Na gode na gode baku kula da rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu albarka kuma,” Ameen kowa ya amsa sannan suka tafi, suna tafiya Juwairah ta saka kukan rabuwa da yar ta, hannun ta ya kama shima yana jin wannan kewar, amma ba yanda zasui, Allah ya basu ladan hakan, a haka har tai bacci.
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Page 34:
Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaiba ba inda bai shiga ba a dangin nasu baki daya, inda kowa yake farin cikin irin wannan kyautar da ba kowa ke iya ta ba, ( mutane in baka haihu ba sun iya maka tereren baka haihuwa ko kalmar juya ta shiha tsakanin ka da su, musamman dangin miji daga sanda aka ce basu da cikakken ilimi, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga dan su me? Aa kawai ki haihu kamar ke zaki bawa kan ki haihuwar, sun manta cewar komai nufin Allah ne, Allah shike bawa duk wani wanda muka gani da da, shi bai isa qoqarin shi ya bashi ba, komai himmar shi a gado kuwa, ko sune Ayu qarewar making love ba zai haihu ba sai da izinin Allah, to me zai hana mu tane su zama irin Juwairah, da ka zo kana ma wanda bai da da gorin haihuwa, mai zai hana kai tinda ka samu Allah ya baka kai ma ka dauka ka bawa wanda kk tinanin juya ne bazai taba haihuwar ba? Ba zaka iya ba? To karka shiga hurumin Allah, matsalar nan ta fi faruwa a tsakanin mu mata, yayyab miji , qannen miji, da surukai, to ki sani ke yar uwata mace, ko wacce mace dangin miji ce wataran, in kikai a gidan ku kika je wani gidan wata ce zata shimfida maki nata ikon, wataqila ma wanda yafi naki, dan haka ki mai kyau kiga mai kyau, kikai sabanin hakakiga abinda ya fishi, ko daidai shi, in kina kyautata wa ana munana maki,ki hakuri jarabawa ce daga Allah zai maki magani zai kuma baki lada mai yawa, Allah ya sa mufi qarfin zuciyar mu) .
A sati biyun da suka koma Juwairah ta shiga kitchen da yamma, a lokacin ta gama komai na girki, gyaran gida, wanka, da kuma tsaftace ko ina na jiki da muhallin ta tana jiran Haerbeebeen ta ne, miqa hannu tai ta dakko wata roba da ta cika ta da niqaqqen garin ridi, a hankali take jin jikin ta ba kwari tin kwana biyu da suka wuce, cup din da ke hannun ta ta matsar jikin robar domin diba, tana budewa taji qamshin kantun da take so na neman ya zama mata wari, amma ta daure a haka ta saka spoon ta diba, zuwa tai tukunyar da ta dafa madarar shanu, wadda Jabeer ke nemo mata a cikin wani qauye anan Abujan, ta dibi yanda zai ishe ta, zumar ta asalin mai kyau mara hadi ta diba ta saka, yanda take buqata, palo ta koma ta zauna, bayan tai bismillah ta riqe cup din da hannun ta na dama ta kai bakin ta ne, wani irin amai ya yunquro mata, da gudu ta miqe zatai hanyar dakin su taje toilet,karo taci da shi yana shigowa, wani yunquri da tai sai anjikin shi, jikin ta har rawa yake yi, dan azabar da take ji a jikin nata, aje jakar shi yai hankalin shi a tashe matuqa, ya kama ta tai ta kwarara amai, sai da ya zamana bata iya fitar da komai sai yunqurin azaba, sannu kam ta shata har bata iya amsawa,idon Jabeer sunyi jaa saboda tausayawa matar tashi,tabbas in hasashen shi gaskiya ne wannan karon da alama mai wahalarwa ne, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan wahalhalun, ga zazzabi dake addabat ta, haka ya jata suka tafi toilet,kayan su ya cire masu,ya saka su a bathtube,ruwa ya cika masu suka dauraye jikin su sannan ya tsiyaye ya saka wani, wanka ya musu suka fito, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a agado yaje ya shirya shima,zuwa yai kusa da ita ya kwanta ta bayan ta” Honey kaje kaci abinci everything is ready at the dinning area” ” I know,but i can’t eat when u are like this, me ke maki ciwo, me kk so, dan daga ganin ki da kuma aman da kikai,bakici komai ba in ba wainar flour din da kikai mai manja ba da safe,” turo baki tai daga baya ta kwabe shi irin na shagwababbun nan, shi kuma yana jin yanayin saukar nunfashin ta ya san na kuka ne, saurin juyar da ita yai, ” What is wrong my love,pls tell me ur problem,or what you want, i will provide you with anything i have inshaa Allah” kukan da take son yi ne na shagwaba ta fara, rungume ta yai yana kissing wuyan ta a hankali yana shafa bayan ta,sai da tai ya ishe ta tai shiru tana ajiyar zuciya, a hankali ta fara magana” Yah Jabeer banda lfy, kwana biyu jikina ciwo yake sosai, ga zazzabi da amai, abubuwan danake so sai naji vana son su,” sai ta qara saka kuka, ” Shhhhhhhh, yi shiru my bby, ki daina kuka, ko zaki gwajin ciki a gida ne, tinda muna da abin yi” jimmmmm tai kafin ta wuntsila daga gadon cikin doki da zumudi, binta yai a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam, sai yanzu, zuwa tai tai gwajin ta fito, layukan na farko ya fito radau na biyun ga shi nan dai, amma tabbas akwai shi, kwabe fuska tai tace” ni ban gane komai ba,” ” to ko asibiti zamu?” ” ehhhh haka za ai ina zuwa” fita tai da hanzari taje ta sake kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin da zai rufe har mazaunan ta, bayan ta gama ne ta juyo taga shima shiryawar yake, a tare suka fita, sun isa wani makeken asibiti, a unguwar tasu ta Jabi, suna zuwa sukai mata gwaje2 inda suka dau wasu yan lokuta, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki ne na sati biyu, wata irin murna ce ta kama su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai dariya take, kissing din ta yai kadan sannan ya aje ta, godiya ya hau ma Doc da bakin shi ya qi rufuwa shima, yana mamakin irin soyayya ta wadannan mutane, bayanan yanda zasu kula da cikin ya musu, wanda sun riga sun sani,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wanilallaba ta kamar kwai, ” Babe me kk so ki ci kinga kar kina barin kan ku da abinda zaki haifa mana da yunwa” kada kai tai a hankali tace”ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu,” aiko ba wata wata ya saka ta a mota sukai gida, suna zuwa ya shiga kitchen, ya hau mata wainar, daukan, abinda ta kasa sha yai shi kuma bayan ya gama mata, tana ci yana sha,”lallai babyn nan, da qoqarin shi,da gaske so yake kar ana shan abubuwan da zasu qara mai kuzari” dariya suka saka dikkan su” ko kuma abubuwan da zasu qara ma Abban shi kuzari ba” qara fashewa da dariya sukai( hadin kantu da madara ko da nonon Raqumi hadine tested and trusted dake saukar da ni’ima sannan yai maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu).