YAN ABUJA HAUSA NOVEL

BAYAN SHEKARA BIYU
Salma ce ke zaune da jaririya a hannu da suke kira da suna Faiha, gefe Juwairah ce tana riqe da hannun yaron ta qaqqarfa mai kuma barna, Salim, Sai Suwaiba da ke ma Abrar kitso a lallausan gashin ta mai tsaho, gefe kuma a kwance a kujera Saudat ce ke latsa waya tana ta doka murmushi, Maganar Juwairah ce ta katse shirun nasu” In baka tsaya ba Salim zan kira Daddyn ka ya dauke ka ku tafi kona huta,” da sauri yaron ya zauna a cinyr ta ya nutsu, dan a cewar shi Daddy is no fun to be with, amma Mummy, yana son zama da Mummyn shi ko da duka zatai mai in yai halin nashi na barna, ‘ Yan biyu ne sika shigo da gudu, suna haki” Mummy Daddyna yace wai ki bada Faiha, Salim da Abrar mu je park” kowa a cikin su daidai lokacin da kowa yace Daddyna sun kalli juna da harara,ba su fada a tsakanin su sai akan abu biyu, chocolate da kuma Daddyn su, sai kace kaya haka ake rabon shi a tsakanin su, wannan yace nashi ne wannan yace nashi ne, fatima ce tace” kaiii wannan Muhammad din sai son yi min kwace kk kullum for how long zaka gane cewa Mummy ce taka ni kuma Daddy nawa” ” Fateema ke ce baki san komai ba hat yanzu” ya fada yana mata kallo wai shi harara, dan kwata2 bai kaita wayo ba, ga shi fadan ma bai iya ba” kai ni ku karbe ta sarakan rabon iyaye,kada Allah yasa ku zaben din ga Faiha in ta girma zata zaben ai” miqa masu ita tai suka karbe ta,dariya saudat tai sosai tace” Mummy ar u jelouse ?” Dariya dika suka dauka, Juwaira ta sauke Salim ya bisu,daidai an gamawa Abrar kiston ta, miqewa tai tace” Tanx Mum” tai kissing kuncin Suwaiba ta fita a guje, murmushi tai mai nuna alamun jin dadi ta bita da”ku dawo lfy kui adduar fita daga gida kan ku fita, kar a manta da yin addua in zaku dawo,” daga nesa ta amsa mata da” inshaa Allah mum, i love u,” ” i love u too baby” nan ma Saudat ce dake ta Chatting da mijin ta ta sake dagawa tace” lovers kenan” nan ma dariya sukai, juwairah ce ke kallon ta da Yan uwan ta cikin farin ciki da nishadin da Allah ne kadai yasan iyakar shi,” to ya kamata mu ma muje Shopping, akwai wasu abubuwan danake so mu siyo yau” ta fada tana kashe masu ido, Saudat ce ta diro da sauri ta dage hannaye sama tana murna” Yeeeeehhhhh shopping” ” u always act like a kid Saudat,” inji Salma, pilon kusa da ita ta wurga mata, ” eh din anyi,my husband always treat me like one,” ta qarasa tana murguda baki, dariya suka saka, Juwairah tace” yeh u ar always his baby” ” and u ar more like baby to me than she is always my love” juyawa tai taga Jabeer ya shigo cikin qananan kaya, tare da mijin Saudat, tsallen murna Juwairah ta daka taje ta rungume shi,wanda dama yana fada hannun shi is open, rungume ta yai kamar su kadai ne a wajen,gyaran murya mijin Saudat yau yace,babban Yaya muje ki, tinda shi wancan Baban yaran ya debe su muma mu kai su shopping din kawai, kallin juna sukai matan, ba haka suka so ba, akwai dan abubuwan su na mata da suka so kwasa, amma ba damuwa sun taya su zaba ma, dakko hijaban su sukai,Juwairah har da Niqab Yah Jabeer yake sata sakawa, haka suka fita, gwanin sha’awa, waya sukai ma mijin Salma ya same su a Sahad dake can ABJ din, aiko Salma da tana jin ta out of place sai murn,sa riya sukai mata, a can suka hadu da yaran da mijin Salma siyayya sukai sosai kafin kowa ya nufi gidan shi, Suwaiba gidan Jabeer zata kwana kafin wase gari mijin ta yazo su tafi.
Arziqi ya wadata a zuri’ar gidan Abba Baballiya, gidan kuma ‘YAN ABUJA, albarkar Allah ta sauka masu, ko ta ina,inda a tsakanin Jabeer da yake dan su da surukan su, kowa qoqarin yi ma iyayen abun da zasuji dadi suke, an canja fasalin gidajen iyayen daga na qasa zuwa na cement, da kayan alatu kala2, ga shaguna da suka bude masu, na saida kayan masarufi suka saka amintattun yara suke kula da wajen, shiko Yah Jabeer kasuwancin shi yana nan da kamfanin jakunkuna na AF2 dake malaysia, abun ba a cewa. Komai sai godiyar Allah,makaranta mazajen dika ke tinanin maida iyalan nasu nan kusa su ci gaba da neman ilimi har sai sun ce ya ishe su, Suwaiba nonoless tin bata son saka bra din acuci maza irin ta Cutie har ta fara, mijin ta ya masu gini a unguwar Kabuga, qaton gida, yanzu harkar gwanjo ta bude sosai, Talle arziqi ba laifi, ana nan an zama manyan ustazai masu ma wasu wa’azi musamman da basu misali da rayuwar su, Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su, na rashin haihuwa, ba sa damuwa a ransu ko adan, tin ana zuga mijin ta yai aure har an gaji, domin soyayyar su suke sha, da shaquwa ga fahimtat juna dake tsakanin su.
Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya.
Masoya novel na ‘YAN ABUJA ku dakace ni gobe domin jin wasu bayanai da sharhi da zan akan wannan novel da inshaa Allah nake saka ran zai amfanar kuma zakuji dadin shi da yardae Allah, ina roqon ku da kuma fatan duk abinda na fada daidai kuma kuka san abin koyi ne da ku qoqarta saka wa a ayyukan ku, sannan wanda nai kuskure ku yafe ni akai, ina jiran gyaran ku akai daga yau zuwa gobe inshaa Allah na gode. Me love u XoXo❤
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Assalamu alaikum Jama aree bandi raabe am, yidibee novel ‘YAN ABUJA, mido yetta on masin,beyeddi on holli am haa dow defteream, mido yeela ko end jangi pat end habdai end naftira bemai koo na pat ba end habda ko sedda on, mido usa mido yetta on walama bana fulbe haa on woni fu ha duniya do miyetti, walama bana yare IBRA, end doo woondi inshaa Allah, mido yidimon❤
Ina kuma riqon duk wanda Allah yasa ta fara bin wannan novel daga farko ko ta riski wannan page din koda bata bi daga farko ba ta daure ta karanta wataqila ta samu koda abu daya ne mai amfani a ciki
Page 36:
Zan yi sharhi ne akan wannan novel namu na yan abuja, inna gama nawa wataqila ba zai yu na fidda komai ba ina son kuma makaranta ku fiddo man da naku hakan zai sa naji dadi maybe gaba na sake mana wani novel din????
1- da farko dai gaba daya a kuma dungule nai magana akan iyaye da tarbiyya ne, yanda iyaye in Allah ya basu yara ya zasu saka su akan hanya mai kyau wace tarbiyya zasu basu, me yaka mata su saka masu a zuqatan sh saboda gudun kar su tashi ba akan tarbiyya mai kyau ba.
2- sannan nai magana akan kwadayi, mahaifiyar su Suwai nonoless ta taso da su akan kwadaryi sa burin zuwa inda ba lallai ne arziqin su na can ba, unlike Juwairah da suka raina ta akan auren Yah Jabeer.
3- Ana son mace ta zama mai tarbiyya mai kyau, wadda ko ina ta shiga za ai sha’awar ta da halayen ta in bata nan ai kewar ta, ki iya zama da kowa da kyakkyawar mu’amalat, ki kasance wadda ko minti daya miji yai baku tare zaiji damuwa da tashin hankali, da duk wanda kk tare da shi ma.
4- Ana son mace ta zama mai tattali mai dabara in ba wannan a gida ta san ya zata hada wancan ya bada outcome mai kyau mai dadi, yanda ba mai gane ma rashi ne ya jawo hakan, sannan ta zama tana qoqarin dasa kowacce hanyar da zata kawo masu sauqi a gidan ta, kamar yanda Juwairah tai lambu a cikin gidan ta.
5- Mace mai rufawa mijin ta asiri a kowanne lokaci abar so ce ga kowa, ba namiji ma kadai ba ga kowa.
6- Mace ki zamo mai tsari, ya zamana kina da lokutan yin abubuwa, in kina haka za a same ki mai tsafta, baki kwaba wannan da wancan, misali, kina girki wannan bangaren zaki iya ci gaba da gyaran daki, sannan ko ya za ai mace in zaki wanki ki fara gyara dakin ki da gidan ki sai ki zuba wankin ki tayi, akwai wasu dana kula ko nace da dama, taqamar zasui wanki sai kiga gidan kamar bola da kin magana ace wanki zan shiyasa, yana daga cikin tsari ki ware ranar da zaki na ma gidan ki gyaran tsaf misali muce a qarshen sati ko sati biyu ko wata daya ki fitar da komai daga mahallin shi ki share ki wanke ko ki goge, sannan yana daga tsari ki ware ranar zuwa kitso da qunshi, sannan ranar yin gyaran jiki irin dai na Juwairah, in Allah yasa gidan ki kina da halin yin lambu kin yi to ki ware mai lokacin duba shi, in baki da lambu a sameki dai da wata shuka da kk kula da ita ga lada ga huce takaici ga amfani,musamman ZOGALE.