YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

7- kar ki zama mai kwadayin abun hannun namiji, komai qanqantar shi komai yawan shi, in kk kasance mai kwadayi tabbas zaki wahala, wataqila ma a kwadayin qima da darajar ku ta zube son ki a hankali ya fita daga zuciyar shi, sannan qataqila in bakinda rabon zama da wani sassa na jikin ki ki rasa shi in d process of kwadayi, da roqo, kamar dai irin na Saudat mahaifaless.

8- A rayuwa kullum Namiji shine jagora shine uba shine yaya ko da kuwa qani je yana zama shugaba, ko abokin shawara, dan haka in baka kasance mai tausayi da tallafawa mace ba ka aje sunan ka a namiji ka daura dankwali ka bi layin matan aita buga cinya da kai, ku duba rayuwar Yah Jabeer da Abban su Salma , Yah Jabeer ba abinda bai taya matat shi, har da gyaran jikin, shaving, gyaran gashi, wanka, wanki, wajen haihuwa ma tare sukai komai, da ace mazan mu na zuwa dakin haihuwa suga azabar da mata ke sha, wataqila da sun rage ma mata rashin mutuncin da suke masu, sun tabbatar matan suna ta mata, suna matuqar qoqari, suna jarumta, da tausayi da sadaukarwa ya shiga zuqatan maza, da sun tarairayi abinda aka haifa masu da kyau da mutunci. Ta wani bangaren kunga yanda Abban su Salma ya dabbaqa sunnar Rasulullah yake kiran matan shi da suna masu dadi, kamar Gimbiya Da kuma Sarauta, wannan sunna ne ko mai tsufan ku soyayyar ku karta gushe,SO baya tsufa sai dai masoyan su tsufa ju jeme, amma soyayyar su na nan.

9- mace kar ta zama mai zazzafan kishi, zai lalata mata rayuwa da tarbiyyar yaran ta, zai sa miji duk son daya ke maki ya fara raguwa, sanan mutane ma masu hankali zasu fara tsanar ki, kuma daga baya kizo kina dana sani, lakin kar ki bari kishiya ta zama tana cin kashi akan ki,dan ko islam bai yarda ka zama mai sako2 yanda mutane zasu raina ka ba,kamar Mama Bilki, ta riqe zaman auren ta da amana ba mummunan kishi, tana da sanyin hali da hakuri,amma me bata yarda a taba yaran ta ba, ta tsaya masu, sannan kuma bata tsayawa ai hayaniya da ita in abu yai yawa action ta dauka, ???? amma ban ce mace ki zama sarkin fada ba fa in dai tabbas zaki dau halin Mama Bilki sak to ratuwar ki da kishiya zaki samu sassaucin zama.

10- Qofofin Allah a bude suke ga bayin shi da suka yarda akwai shi kuma shi mai rahama ne, to duk zunubin da suka aikata ko da shirka ne, har dai in basu mutu akai ba suka tuba to Allah zai yafe masu,kamar yanda misali ya tabbata akan Kallah ya ce akwai lokacin tuba a gaba amma me yana fita mota ta mai lalata, ta dauke shi a duniyar, ai kunga ba lokaci kenan, mutuwa tana jikin skin din ku, at anytime zata iya cika mana aiki da izinin Allah dabularnin mala’ikan mutuwar, take za a zare ran mu, sannan shi Salihu daya tuban ga shi kudin dai yaoe dasu a bayan na haram daya tuba ya gyara ya sha wuya na dan lokaci na sana’a wan da a da bai san ya zai ba, daga baya kuma yai kudi ta hanyar halal.

11- Matan da basu taba haihuwa ba sui hakuri, Allah na sane da mu baki daya, ki zama kina wa kanki wannan adduar yar uwa” Ya Allah Ya rabbi ya khaliqu kulli shai’in Allah ina riqon ka, indan haihuwa alkairi ce a rayuwata da ta mijina da al’ummar musulmi da musulunci Allah ka bani, idan sabanin haka ne Allah ka samin hakuri da juriya tare da dangana, Allah kar ka bani, ka shiryar mana da sauran yaran musulmi su zama masu albarka” wallahi damuwar eashin haihuwa na maki alqawai in dai kinyi adduar nan da ikhlasi Allah ba zai barki haka ba sai ya maki zabij da kk nema.

12- Ta bangaren maza kuma in matar ka bata haihu ba ba shi zai sa ka juya mata baya ba, dan mace bata bawa kanta haihuwa, wataqila matsalar daga wajen ka ne, to misali ace ma daga wajen ka ne mace zata iya hakuri ta zauna da kai a haka, ka duva ka gani ba ta da wani namijin bayan kai amma zata zauna da kai, kuma ba shi zai hana kai ta maya rashin mutunci ba, amma kuma in ita ce mai matsalae wataqila ka sake ta, in ka barta kuma ka ce aure zakai ba zaka zauna da juya ba ita daya, ka gani mata ko yaushe su ake tauyewa duk inda aka je aka zo, me zai hana mazaje ku dage ku dabbaga sunna, ku kuma qoqar ta ku tabbatar ma duniya ba addinin da yaiwa mace martaba da qima sama da ISLAM?

13 – ko wanne stuation dayan ma’aurata ya shiga dayan ya nuna mai i am by ur side no matter what, duk daci duk zaqi ba zan barka ba tare muke a ciki.

14- soyayyar yan uwantaka abu ne mai matuqar mahimmanci sai da hadin kai bawa ke zama sarki, sai d hadin kai mayaqa kan samu nasara, in kanku a hade yake zuriar ku zata zama abin tsoro da kwarjini ga kowa, za ai tsoron taba dayan ku, za a na ganin ku as ka tabo daya goma ta shafe ka wa zai so?

15- mace ana son ku zamo mai iya tarairayar miji, mai bashi haqqin shi na auratayya a koda yaushe, mai iya salo kala daban daban, ba tare da kauce hanya irin na matan yanzu da suka maida kallon turawa suna zina ya zama wai suna koyon style na auratayya wa’iyadhubillah, me ya kai ki ko me ya kai ka? Me suke da shi da mu bamu da shi, zuciya ce da kwakwalwa, muma muna da ita,a rana in kin so zakui style kala biyar ko fi, ku gamsar da juna,ba tare da kowa ya koya maki ba, to ku sani ni a nawa duk namijin da zai saka mana wani shirme mu kalla kafin sex ba namiji bane, rako su yazo in sun gama sabgar su ya bisu su koma, dan ba rashin zama na mijin da ya wuce ka kasa dagawa mace sha’awa sai kun ga wasu awaki na yi sannan ka samu ka take matar ka da ya fi wannan, ga illoli dake tattare da hakan, fushin Allah da tsinuwar shi akan ku dika, haihuwae yaran da ake cewa yanzu sun kashe iyayen su, sannan kuma ciwon makanta, sai mai wannan hali ya shirya masu in bai daina ba. Sannan illar kallon nan yanzu ta shine aka yawaita mata yan lessbians da maza gay dan musiba da qazanta Allah ya kare mu da zuriar mu.

16- Sadaukarwa, ka sadaukar da farin cikin ka dan wani musulmi ko dan uwan ka ya samu farin ciki shima, ga lada ga qarin arziqi da zai same ka, zaka samu da yardar Allah Allah ya mayar maka abunnan da ka sadaukar har da fin shi ma, kamar yanda Juwairah ta sadaukar da Abrar ma Suwaiba nonoless.

17- kowacce mace dangin miji ce ki kula da yanda zaki tafi da dangin mijin ki kema naki dangin mijin su kula dake in kika qi yin da kyau zaki ga ba kyau kema.

18- kula da tarbiyyar yara a tsakanin dangi, musamman cousens a wannan zamani, cousens sun ja an aurar da zawarwan yammata da yawa, ba tare da an sani ba, zaki ga suna wasan banza ba za a hana ba ace wai ai yayan ta ne, ba aure tsakanin su? Ke ko da aure yanda zamanin nan ya baci akwai limit na komai, ko kiga ya damu da ita da yawa,ko yaushe suna tare mamat2 ace ai suna matuqar shiri,kin tintibi dalilin shirin? Sannan kuma wajen bacci a bar yara sakaka ta nam wallahi cousens ke dada bata mana yara da qanne, dan haka mu kula dan kin tsaya akan yar ki baki laifin komai ba a duniya da lahira.

18- ina ma mata nasiha da qamshi, da kwalliya,tsafta girki iya magana musamman da yawan mu bamu iya kalamai ba da magana komai yabawa muke, ki iya kwanciya, kirsa, kwarkwasa, iya saka qananan kaya,da daura zani, iya kallo,shagwaba, wayyo da mata sun san me ke cikin ta da wataqila har makarantar koyar da ita an fara bude masu, ki iya girki, macen da ta iya girki mai aji ce ki ba ta da aure, ba raini tsakanin ta da kowa, ki zama mai sassauqan halin da kowa zai so mu’amala dake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button