YAN ABUJA HAUSA NOVEL

‘YAN ABUJA kuwa bayan sun isa wani katafaren hotel suka sauka mai suna Chelsea hotel……………..
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????
BY HAERMEEBRAERH
Hey guys, i want u to know that i really and truelly apriciate ur love, Allah ya barmu tare, as for those of u that ar requesting for this novel ta prive dan Allah kui hakuri na kai page 5 as u can see wayata riqewa zatai in ina tura novel da yawa abun ba mutum daya ba, so dan Allah ai hakuri da ni.Tanx.
I dedicated this page to all it’s fans, and WATA UWAR’s fans. ANA MUGUN TARE. ME LOVE U XOXO❤
Page 5:
Tinda suka je farfajiyar wajen bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suka gani, wasu sai a American movies suka taba gani, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba, ( abun ku da masu idon cin nera) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su, sun shiga wajen da ake gabatar da dinner, inda suka qarasa wajen hight table din su hudun su, iya ganin su iya ganin jajayen hulina ne, sai fararen kaya da sirkin ja, daga matan har mazan shigar kenan, sune kadai suka saka baqin lace da ratsin baqi, mazan su ma farin shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su, wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakim ce a wata qatuwar kujera, suma tashi sukai suka kai mai gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gidanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yake yai serving kan shi abin da zai ci wajen maza daban wajen mata daban, wani irin nama ne na daban da aka zo dafawa aka mai dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba, matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sunci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi ya kafa kai tas suka shanye, suka aje kwalbar, bayan an yanka cake ne da sauran bidi’o’i aka tashi daga wajen inda angwayen suna shiga mota suka bama matan wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su da su sai naga sun dauki wata hanya kamar za a bar garin, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba sukai a hannu suka shiga da su gidan a wani qaton falon nan anan suka aje su kan kujeru suka juya zasu fita, ji sukai wata qatuwar murya tai magana, kai min ko wacce daki, ka hada su a gado daya, wani turmusheshen mutum ne ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, i have been wondering were on earth do they found his size???? God he is huge???? ga tsaho ga qiba, ga tumbi, ga sanqo, ga gashin baki, ga hammatar nan cunkus, ga idonnan jawur, ga ga ga……. my goodness, i can not describe this guy, kawai gashi nan dai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalle su suka duqa, alamun gaisuwa, daga masu kai yai ya ce” kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba” yana lashe baki, daga kai sukai suka amsa da ” to oga zaks, fita sukai kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos.
Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar yai ya kunna bed sid lamp, cire masu kaya yai ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu ????????♀????????♀????????♀????????♀.
Ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa yai wani bangare ya shiga wani daki, waya yai naji yana ” ku shigo, ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwai ba suke nan suka shiga, gyara su suke, suna tausaya masu, amma dayar tace” hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka hadu da su, ai kinga ban ga laifin su ba kwadayi mabudin wahala” haka ne kam” tafiya sukai bayan sun kammata, a palo suka hadu da shi yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki, ” daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai daku matana kuma ta inda baku tsammata ba tana zan na amfani da ku, munafukan banza da wofi” jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su yai ya barke da wata mahaukaciyar dariya.
Salma matar me saida mota kuwa, wani qaton gida aka kaita a wata unguwa a gwarinpa, wani qaton gida ne mai kyau, ya tsaida motar, fita yai ya je ya bude gidan da kan shi, ya dawo ya shigar da motar fitowa sukai yana riqe da ita a jikin shi, bayan sin shiga ne take ta zare ido ganin dukiyar dake gidan, wani daki ya kaita mai kyau, suna shiga ya janyo ta ya fara aika mata saqinnin shi, dan shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma ba laifi tana tare da budurcin ta, ba sallah ba salati ba godiya da Allah na daren farko na ma’aurata ba adduar komai haka ya maida ita mace, yasha kuka da zagi, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne yai ta rarrashin ta, qasan zuciyar shi yana ” zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya” amma a fili wani lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta” tab haka rayuwar Abuja take dama, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwaira a baya ina tausaya ma rayuwar ta” ” tinanin me kike haka ?” ” ba komai, ina tinanin ka ne kawai” ta fada tana wani karairaya ta haye cinyar shi, ” woww karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki” dariya tai tana shafa jikin shi tana limshe ido, ” da gaske Alhaji na?” Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa” hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki” ( yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena) amma a fili cewa yai shirya muje na kaiki ki siyo kayan” da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dau jakar da tazo da ita ta fito, tsaf ta ganshi a tsaye yana mata shegen murmushi, fita sukai suka dau hanya, suna tafiya taga suna barin gari,” ina zamu ne sweety?” Wani waje zan kai ki in kk ga wajen zaki ji dadi sosai” wooow u ar so romantic babe, i love u” I love u more dear” kiss yai wa hannun ta, a haka yana tuqi tai bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take, ” babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake ne?” Hhhhhhhh ba mafarki kk ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway , karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?” Ya fada yana wani shu’umin murmushi, ita ko ta dade da fara kuka harda majina, kuna take tana bashi hakuri ya maida ta ma Goggon ta ita ta fasa auren, wanka mata mari yai,” dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudadeb nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ku tabbatar kin biyo ni in ba haka ba gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace” daga kai tai dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin tq in yai dubu to ya tafi yawo, musammab da ta shiga taga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledat daki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma, biyo ta yai yace ta biyo shi daki mai kallon nata, amsawa tai ta abishi kamar raquma, wani daki ne mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci ma an yi fari ta fuska an dashe har fuskar tayi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannu, manyan yayan shi ne, a qauyen da Talle aka san shi, mijin marka, markan ce ta fito kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da zanin ta, ido yai jawur, alamun girki take kenan, duk qauri da warin hammatar ta ya bude wajen, ” dalla malama ki sauri yau zan koma ni” shigowa tai tana bin salma da mugun kallo, “wannan fa Talle?” “Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan , kuma haka” sa kai yai zai fita, ” ina zaka rabon ka da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zakai ba zaka wuce” ” jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har gabam yayan ki sai kin nema ba” eh naji din muje” a gaba ta sa shi sukai daki yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta taja tai dakin da yake nata,gado ta fada tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so cannda wata qazama yana mu’amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kanta???????????? Oh Yau meye ranar kwadayin na ta? Kuka take sosai taji an banko qofar” Malama kije ki qatasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su” shewa sukai yaran suka tafa, “Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss ” suka fada a tare, miqewa tai ido yai mata jawur tace” ni na sa uwar taku shigewa daki da ubam naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?” Ke malama yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu nan gaba mu zane matan baba muke ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika fada ba” dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo dauke da bokiti akai na markaden koko, kallon su tai ta kauda kai , ” ke jummala je ki qarasa abinci marka bata kusa,” ” ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai” wucewa zatai huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana” Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci kui wanka in su yaya Baban gida sun zo suita lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?” Shiru sukai suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, a hankaki tai shiru ta daga kai taga Salma ” laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?” Daga mata kai tai ta shige daki, shigat ta ke da wuya Talle ya fito daga daki………..[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????