BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace “Okay, kana so kacemin kudi sune abin so fiye da komai arayuwarka?”
“No, ba rayuwa ta kadai ba, harma da rayuwar Wanda yake kokarin shigo wa cikin rayuwa ta, kudi sune gaba da komai awajena”
Tace “to Malam Naufal Umar Arabo, inban manta ba haka kacemin sunanka ko? to Ina ganin Bama Sai kazo ba, kayi zamanka kawai, Allah yahada kowa da rabonsa” qit takashe wayar ta
Baisan lokacin da wani farinciki ya lullubeshi ba, har dimples dinsa suka lotsa, cikin murna yace “yessss” sannan yaci gaba da Jogging dinsa
*** ** ***
Labarinsu
Alhaji Abubakar Arabo,Alhaji Umar Arabo, dakuma Alhaji Usman Arabo, uwarsu daya ubansu daya, ‘Yan asalin qasar Niger ne, buzayen dasuke rayuwa cikin Sahara, sunada mutuqar dukiya da Tarin shanu, sau Tari mutanan Nigeria suna zuwa wajan su siyan shanu domin su kiwata su siyar dasu da tsada, kasancewar inda suke rayuwa babu isasshen abincin dabobi, daga baya sukai hijra suka dawo Nan Nigeria, sukaci gaba da juya dukiyar su har Allah yayi mata Albarka suka zama manyan masu kudi da ake damawa dasu ayau.
Alhaji Abubakar shine Babba, suna kiransa Baba Habu, yana zaune a Jigawa shida matarsa da yaransa maza guda biyu sa’annin Naufal ne Amma sun dade da aure harma sunada yaransu
Saikuma Alhaji Umar shine na biyu, suna kiransa da Dady yanada Yara guda bakwai, NAUFAL shine Babba, Suna kiransa da Babban Yaya, Sai Yan biyu maza,Sa’ad da Sa’eed, Sai Anty Maryam, tayi aure tanada yaro daya,me sunan Naufal, suna kiransa da junior, Sai Yan biyu mata, intisar da ihsan, saikuma yar auta WAHEEDA
Sai Alhaji Usman Arabo, shine Dan qaramin su,suna kiransa da Uncle Usman, Allah bai bashi haihuwa ba, yanada matarsa guda daya, suna cemata Hajiya Anty, ma’aikaciyar Asbiti ce
Dukansu mutum ukun Nan Abubakar, Umar, Usman, suna kyautatawa junansu, matansu na can Niger sune de har yanzu atare dasu, suna mutuqar girmama juna, gaba dayansu kama suke da juna daga matan, har mazan, dakuma yayansu, duk fararene, saide na wani yafi wani, Amma dukansu farare ne, kana ganinsu zaka San buzaye ne na asali, tsabar kyawun dasuke dashi ne yasa ake Kiran Family din nasu da Suna (Arab Family) , Amma dasuka dawo Nan gida Nigeria, Sai Yan Nigeria suke cewa Arabo Family 😃
Kamar yanda nafada Naufal shine babba acikin yaran Alhaji Umar (Dady) shekararsa Talatin da shida, beyi aure ba, iyayen sunaso yayi aure kasancewar sa babba a gidan, yana kula da qannansa yanda me karatu baya zato, shiyasa ko wani abu ne yafaru saide kawai iyayen su fada masa, shikuma zai warware komai, kwata kwata baya wasa da yan’uwan nasa, idan kaga ya ware yana fira wasa da dariya to da abokan sa ne, musanman yayan Baba Habu dasuke jigawa, koda yaushe fuskarsa a daure take, bala’in tsoransa sukeji musanman qannansa mata, kana laifi kadan zai daka Maka tsawa, shiyasa suna ganinsa kowacce take shiga taitayinta, babu ruwansa duk wacce tayi masa laifi zaneta yake, suna komai duk abinda suke so, saide yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, saide Hijab, Kuma suna kiyayewa mutum daya ce take bashi ciwon Kai acikin qannansa, itace auta WAHEEDA, itace tafara kiransa da BABBAN YAYA, daga Nan kowa yake fada masa, babu Wanda zakaji yace Yaya Naufal, saide BABBAN YAYA.👌ðŸ»
Cikakken Dan qwallon qafa ne Wanda akeji dashi afadin qasar tamu ta Nigeria dakuma kewayen ta, lokacin daya gama Degree dinsa na biyu, (Masters) iyayen sunso yayi aiki a qarqashinsu, domin su qara habbaka kasuwancin su, Amma BABBAN YAYA yace inaaa! Shifa harkar qwallo zai fara, saboda Dama can tun yana qarami abinda yake so kenan, daga Alhaji Habu na qauye har mahaifin sa Alhaji Umar Qin bashi goyon baya sukayi, daqyar Alhaji Usman yadage akan su harya shawo kansu suka yarda, da farko Yan kano pillars yabugawa Ball, daga baya wata qasar ta daukeshi, daga Nan Kuma yakoma qasar Spain, Bayan wasu shekaru yakoma qasar dayake a yanzu yana buga musu Ball inda yake daukar albashin sa Mai tsoka duk sati.
Lokacin dazai fara Ball babu sunan daya fad’o masa Arai sai Wanda fitnanniyar qanwar sa WAHEEDA tasaka masa, BIG BROTHER, shiyasa jikin Jessy dinsa, p-cap dinsa,sunan BIG BROTHER ne ajiki, Yan gari, Yan unguwa, fan’s dinsa na ko’ina kowa Big Brother yake ce masa, inde yashiga cikin jama’ah kawai haquri yake, saboda yanada masoya masu dimbin yawa, kawai Yan gidansu ne suke kiransa da BABBAN YAYA, Amma jama’ah kowa da kowa Big Brother ake ce masa,yanmata kuwa kullum cikin kiransa suke, yana alfahri da hakan.
Iyayensa sunaso yayi aure saboda shekaru irin nasa, Amma yace shi har yanzu baiga wacce ta kwanta masa ba, tun yana qarya yana cewa zai kawo wacce yake so aqara masa lokaci, har iyayen suka dawo daga rakiyarsa suka fara hadashi da yaran abokai da Kuma yan’uwa, Amma har yanzu duk wadda aka hadashi da’ita yasan irin dabarar dazai mata Dan su rabu cikin hikima, kamar de yanda ya kasance a tsakanin sa da Habiba Yanzu 🤪
Duk cikin yanmatan da’ake hadashi dasu babu wadda yataba baiyana mata Kansa, inde yakira wayar su yana fada musu cewa sunansa Naufal, baya cewa Big Brother saboda yasan cewa muddin yafadi wannan sunan, to babu Wanda bai sanshi ba, wannan kenan
*** *** ***
Tafe suke hannunta dauke da wani yaro Wanda bai wuce shekara uku ba, Sanye take da hijab pink colour, me hula, ta gaban hijabin kadai zaka iya sanin cewa Allah yayi mata tarin suma da yawa, kasancewar wuyan yayi mata yawa kadan, yarinya ce bazata wuce 18 years ba, ranar datake dukansu itada Yaron yasa ta yatsina fuska, Amma duk da haka kyawun fuskarta yana Nan, duk da babu kwalliya kodaya a fuskar, Sai haki take da alama Yaron yamata nauyi, suna zuwa bakin get din gidansu ta sauke Yaron, kudi tafuto dashi daga cikin handbag taware 5k tabawa Yaron sannan taja hannun sa suka qarasa gida, babu kowa afalon nasu, Kai tsaye dakinsu tashige, mutum uku ne zaune a Dakin, ‘Yan biyu daya tana yiwa daya tsifa, saikuma wata Babba tana duba littafin azkar, gaba dayansu kama suke da juna, kana ganinsu kasan jini daya ne, hijabin jikinta ta cire ta wullar dashi anan, lokaci daya tsantsar dirin jikinta ya baiyana, mace ce har mace, gata yar qarama Amma Allah yamata baiwar kyakykyawan jiki.
Yaron yatafi da gudu wajan mamansa yace “Momy munje Kuma anbamu kudi da yawa, Nima anty Waheeda tabani, kingani?” ya qarasa maganar yana nuna mata kudin hannun sa
Murmushi tayi tace “Lalle Waheeda kice kudi kuka samo keda junior”
Zama tayi a bakin gadon tareda cire ribom din kanta, hakan yabawa dogon gashinta damar zubowa gadon Bayan ta
Tace “eh Anty maryam, dubu goma aka bamu, shine naraba mana”
Kafin wadda aka kira da Anty Maryam tayi magana, daya daga cikin Yan biyu tace “Qarya kike Waheeda, Anty wallahi qarya take, kawai cutar Yaron tayi, kamar bakisan halin Waheeda ba, Allah qwace masa kudin zatayi”
Cikin rashin kunya ta kalli me maganar, duk tsananin kamar dasuke kasancewar su identical twins Sarai Waheeda take ganesu, tace “to Ihsan na qwace din, ai tare aka aikemu da junior din ko? Kiyi abinda zakiyi”
Anty Maryam ta kalleta tareda riqe ha6a, tace “lalle Waheeda wuyanki ya’isa yanka, yayun naki kike fadawa haka?”
Wadda ake yiwa tsifar ce tatashi ta nufi Waheeda tace “Na hanaki daukar min hijabi na Amma kinqi yarda ko, tsabar masifa da naci kinada hijabai bazaki saka ba kin goge su kin 6oye saide ki dinga daukar namu kina sakawa saboda Kin raina mana Hankali, nayi Miki last warning karki sake daukar min hijab, sannan Ihsan ba sa’arki bace karki sake mata rashin kunya “