BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda sukazo gidan bai leqo d’akin datake ba, itama bataje inda yake ba, ko kitchen d’inma bata shiga ba bare yasaka ran zata dafa musu wani abun, damuwa tataru tayi masa yawa yarasa ta’ina ma zai fara lallashin ta? Ada yana lallashin tane a matsayin ta na qanwar sa wadda yakeso, yanzu Kuma zai bata kulawa da lallashi ne a matsayin ta na matarsa, to gashi tana cewa bata sonsa, Yaya zaiyi ne?

Da tunani yafara yimasa yawa saiya dauki waya zai kira Ummah ya fad’a mata a aiko musu da abinci, yana kira Ummah ta d’auka tace “Yayansu yagida”

“lafiya Ummah, Am… Ummah idan yaran Nan sungama abinci, sutaho mana dashi”

“to zasu kawo muku, zanzo Nima nasake ja mata kunne nasan Waheeda batajin magana, karka fita ko’ina ka zauna agida ka huta Sai anjima…”

Babban Yaya yariqe wayar yayi shiru, yanaso yace mata Kozai dawo da Waheeda gidane idan tagama hucewa Saisu kawo ta, to Amma yaji kwata kwata Ummah taqi bashi wannan damar ma bare yayi mata doguwar magana, kashe wayar zaiyi, saiyajiyo muryar Anty tana cewa “Amma Yaya da kun Bari yarinyar Nan tad’an sake dashi kafin sutafi, kwata kwata bamu yi mata shirin komai ba, kamar batada gata?”

Ummah tayi tunanin Naufal yakashe waya, shiyasa tana cewa Sai anjima kawai ta ajiye wayar, Babban Yaya kuwa fasa kashe wayar yayi, yayi shiru yana jiran amsar da Ummah zata bayar

Ummah ta kalli Hajiya Anty tace” wanne irin sakewa Kuma Antynsu? Yau tafara zama da Naufal d’in? Tafi kowa sanin halinsa acikinsu, taje tayi ta kukan idan tagaji zata daina, yanzu Hankali na ya kwanta tunda tana d’akin mijinta, kwanaki kamata nayi tana waya da Maya, bansan de kan zancen nasu ba, Amma saina ji ita Waheeda tana hurewa Maya kunne Wai wallahi ta yarda ayi mata auren, inda ace itace yarda zatayi, ai har wanka ma ita zata dinga yiwa mijin, har abar zata kama ta wanke…. “

Babban Yaya yazaro Idonsa 😳, dariya ta kamashi cikin sauri yakashe wayar kar Ummah ta d’auka taga waya a kunne

Hajiya Anty tace”mun shiga uku Yaya, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, to ai yanzu saitaje ta wanke ta yayansu” 😂

Ummah tace “shiyasa na dage akan ayi mata auren, Hankali na zaifi kwanciya”

Babban Yaya yadinga dariya ad’aki shi kad’ai,yana mamaki Waheeda ce tafad’i irin wannan maganar? 🤔Shiyasa daya tambayeta laifin me tayiwa Ummah tayi shiru taqi fad’a masa?

Ummah bata Bawa yanbiyu abincin sun kawo ba, Sa’eed tabawa yakai musu,Bayan tafiyarsa Babban Yaya yaje yayi nocking d’akin tanajinsa taqi bud’e masa haka ya haqura yajuya

Abu kamar wasa kwata kwata Waheeda taqi bud’e d’akin, inde taji alamun yana gida saita rufe d’akin ta, babu abinda take a gidan, tanajin yafita, saita futo tayi harkokinta Takoma d’aki, abinda tasa aranta shine itade bazata iya wannan rashin kunyar da Babban Yaya ba, domin kuwa rayuwar aure daban, rayuwarsu kafin aure daban, Gara suci gaba da tafiya Ahaka

Babban Yaya tun yanabi takanta harya dawo ya share ta, yau tanajin qaran TV afalo tafuto daga d’akin, lemo ne a gabansa dakuma computer yana typing, d’agowa yayi ya kalleta sau d’aya yamaida Kansa ga rubutun dayake

Zama tayi aqasan kujerar dayake zaune, ta sunkuyar da kanta qasa, batare daya kalleta ba yatashi daga wajan zai wuce d’akinsa, cikin sauri tatashi tabi bayansa, d’akinsa yashiga zai rufe kofar saigata kamar an jefota, d’aure fuska yayi yace “menene Kuma? Inace gudu na kike?”

Wasa tafara da yatsun hannunta, idonta yaciko da qwalla tace “Dan Allah Babban Yaya ka temaka ka sakeni….”

Cikin sauri ya kalleta, Kansa ya Sara kamar an doka masa guduma, cikin sauri yace “meyasa?”

Hawaye ne yazubo mata, tace “haka Nan…”

Yace “hakanan? To kiyi hakuri, bazan iyaba, because…. I luv you, sannan karki kuskura kisake min wannan maganar”
Yafad’i hakan tareda juyawa zai shige d’akinsa, kuka tafashe dashi tace “Dan Allah Babban…..” kafin ta qarasa maganar Tata yajuyo yahad’e bakinsu waje d’aya

Lumshe idonta tayi, hawaye masu zafi suka silalo daga idanuwanta, tanajin yanda yake tsotsar lips d’inta kamar yasamu sweet, daga baya yakama harshen ta yana musu wata irin tsotsa kamar ba Babban Yaya ba, bud’e Idonsa yayi yaga yanda take hawaye kamar anbud’e famfo, ahankali yasaka Hannunsa yakama kanta yariqe,ya Lumshe idonsa yacigaba da kissing d’inta, abunda yadad’e yana mafarkin samu Sai gashi yau yayi mata shi, tana cikin hayyacinta Kuma a matsayin matarsa

saida yasha bakinta sosai sannan yasake ta, yana sakinta Tajuya d’akin ta da gudu tana kuka, Shima jingina yayi da jikin kofar d’akin yana sauke numfashi, ga wata irin sha’awa datake taso masa, jiyake kamar yaje wajan Waheeda

Mararsa ce ta murd’a yasaka hannu yadafe, ahankali ya qarasa kan gadon, tareda d’aukan wayarsa, yarasa wazai kira Ummah kokuma Hajiya Anty? Wazai fad’wa matsalar sa? Ummah de da’ita yasaba, yasaba fad’a mata komai, Dan haka yanzun ma ita zai nema, Ahankali yayi Dialing number ta, tana d’auka ya Lumshe Idonsa yace “Ummah, Waheeda taqi hakura har yanzu, Ummah me zanyi mata tasoni?, Ina sonta Ummah, yanzu cemin tayi insaketa fa Ummah… “ya qarasa maganar cikin rawar murya

Ummah tayi murmushi tace “kashirya katafi England, zanyi maganin komai son”

Kai tsaye yace “to Ummah” sannan yakashe wayar

Waheeda ma anata 6angaren cikin kuka takira Hajiya Anty, saboda tasan Kota kira Ummah ba goyon baya zata samu ba 😃

Anty tace “Daughter lafiya?”

“Anty Allah nagaji….” abinda tace kenan, tafad’i maganar cikin kuka

Anty tace “subhanallah, meyafaru ne? Kimin bayani Waheeda duk Hankali na yatashi”

Hawayen tashare tace “Anty ni bazan iya zama dashi ba, haka kawai saiya dinga min wasu irin abubuwa, aishi Yaya nane, meyasa zaimin haka”

Anty ta dafe kanta🤦🏻‍♀️tareda murmushi tace “to kiyi hakuri yadena, zanyi masa magana karya sake 6ata miki rai, kinji Daughter”

‘Daga kanta tayi kamar ba waya take ba, sannan tace “to” tareda kashe wayar

Kamar yanda Ummah ta bashi shawara rabuwa yayi da Waheeda, washe gari da safe ya shirya zai koma bakin aikinsa

Driver ne yad’aukeshi, Kai tsaye yace “muje gidansu Maya”

Suna zuwa driver yafuto da sari yabud’e masa motar, yaro yatura Akira masa Maya, babu 6ata lokaci kuwa Sai gata tafuto, tana ganinsa ta qarasa wajansa tace “Babban Yaya Ina kwana”

Idanu yazuba mata yace “Lafiya Maya, zuwa nayi inyi miki godia”

Murmushi tayi tace “babu komai wallahi, Allah yabada Zaman lafiya”

Envelope yamiqa mata cikeda kud’i yace “ga wannan ki kaiwa mamanku, sannan ki shirya Bayan qawarki tagama fishi zaku tafi Saudia tare insha Allah”

Cikin murna Maya tace “Babban Yaya mungode, Allah yasaka da alkhairi”

Yace “Amin, idan kinsamu lokaci kije gidan ki lallasheta, kibata shawara” yafad’i hakan yana Sosa girarsa d’aya 😃

Tace “to insha Allah zanje”

Murmushi yayi yashiga motar, yana fatan ace ta fahimci shawarar dayake nufi abawa Waheeda, fatansa d’aya Allah yasa tabata shawara irin wadda Ummah taji suna fad’a awaya 🙊🙈🙊🙊

Kafin su qarasa Airport yaga text yashigo wayarsa daga Ummi naban haquri, shareta yayi baiyi mata replay ba, ya goge number ta daga wayarsa, ya tabbatar taji labari ne cewa Waheeda lafiyarta kalau, shiyasa takeso ta lalla6o tadawo 😂

** *** **

Sai wajan azahar Maya takira wayar yanbiyu suka kwatanta mata gidan da Waheeda take, sannan ta shirya tatafi, tana zuwa megadi yatareta yana mata tambayoyi tayi masa bayani sannan Yabarta tashiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button