BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannun sa takama tacire daga kan takalmin nasa dayake so yacire, ta qarasa cire masa takalmin kamar wani mijinta, sannan tacire masa safar tana cusata cikin takalmin, takama dogayen yatsun kafarsa masu laushi tanaja ahankali sannan tace “ai nasan kudi ne aciki, Dan Allah Babban Yaya ka temaka kabani kudi ko dubu hamsin ne”

Ba tareda tunanin komai ba yace “bude ki d’auka”

Kafarsa tasaki tabud’e jakar, da daloli tayi tozali, cikin mamaki ta d’ago ta Kalle shi tace “Kai kai Babban Yaya ashe kudin ne aciki? Allah jinake ba kudi bane, kawai fad’a nayi”

tafad’i hakan tana rufe jakar, sannan tatashi Takoma kan gadon ta zauna kusa dashi

Babban Yaya ya kalleta yace “ki d’auka duka nabaki”

Cikin mamaki tace “me? Wai kudin?”

Yace “Emana, kid’auka nabaki”

Kanta ne ya d’aure tace “Babban Yaya, daloli ne fa aciki, me zanyi dasu?”

Juyowa yayi yana fuskantar ta, yace “tome kike so? Idan kud’in kike so kitafi dashi, saiki saka cikin account dinki”

Murmushi tayi, dimple dinta yafuto kamar nasa tace “Babban Yaya kana magana kamar ranka a6ace, please kasaki ranka mana”

Murmushi ne ya qwace masa ba tareda shirya ba, yace “naji, tashi kibani waje, Ummah nah tace na kwanta nahuta”

Bakinta ta turo gaba, cikin shagwa6a tace “Babban Yaya Dan Allah mu ‘Dauko anko? Wallahi Dama kud’in danace inaso d’in sonake naje kasuwa mu ‘Dauko anko”

Dariya ce ta kamashi yace “kuma anko da dubu Hamsin?Bari kiji, babu wani anko da zakuyi, tunda bason auren nake ba, Kuma ta shafeku”

Tace “Dan Allah Babban Yaya kaji, wallahi muna so, Dan Allah muyi? To wai Kai meyasa baka son auren?”

Cikin damuwa yace “nafad’a miki Bana burin zama da wadda banaso, karki sake min wannan tambayar, Sai me Kuma kike so Bayan wannan?”

Lallausan Hannun sa takama tariqe cikin Nata, Kallan ta yayi cikeda mamaki ya kasa magana haka Kuma ya kasa qwace hannun sa, cikin nutsuwa tafara yimasa magana tace”nikam ai nagama samun abinda nakeso a rayuwa Babban Yaya, iyayena suna sona, Babban Yayanmu yana sona, sannan Huzaifa yana sona, Bana tunanin komai akansa, nasan ko Bayan munyi aure zai riqeni Amana kamar Babban Yayanah, saide Kuma naso ace nasamu me kama dakai Babban Yaya”

Gabansa ne yake Dukan Tara Tara, tunda tafara yimasa wannan maganar, kwata kwata yafita haiyacinsa, zuciyar sa ce take zigashi akan yafad’a mata komai, karyayi wasa da damar sa, karya Bari abinda yadad’e yanaso yakufce masa

Cikin sauri kamar Wanda aka mintsineshi yace “koda nine….?”

Kallan idanunsa tayi, cikin rashin fahimta tace “kamarya?”

Shima Kallan qwayar idonnata yayi yace “Zaki iya auren me kama Dani, meyasa ni bazaki aure niba….?”

Kuyi hakuri Dan Allah 🙏🏻🙏🏻
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: SM

BB

Cikin sauri ta d’ago ta Kalle shi, tsananin mamakin abinda yayan Nata yafad’a ne yasa takasa rufe bakinta, gabanta yafara fad’uwa ganin yanda fuskarsa ta nuna kamar da gaske yake, wata zuciyar tace da ita ke mahaukaciya ce? Tayaya hakan zata faru tsakanin ku?yayanki uwa d’aya uba d’aya tayaya?
Dariya ta kwashe da’ita tace “Babban Yaya aure Kuma? Tayaya? Tayaya zan aure ka? Please Mekake so kace? Nasan inajin sonka acikin raina fiyeda yanda nake jin huzaifa acikin zuciyata, saboda Babban Yaya ubane, Kuma ba’a sauya uba,shi kuwa Miji Ana sauya shi”

Kansane yasara har saida yariqe goshinsa, lokaci d’aya ya dawo cikin haiyacinsa, yatuna irin kato6arar da yayi, cikin sauri yace “lokaci ya quremin, Sorry….kuje kuyi ankon tunda Kuna so, tashi kije”

Cikin murna Waheeda ta rungume shi tareda manna masa kiss agoshi, tafice daga d’akin

Tana fita yazube akan gadon nasa, duk yanda yake jin dad’i idan jikinsu yahad’u yau baiji komai ba kasancewar yasan cewa akwai Babban aiki a gabansa, idan yarinyar ta amince da auren sama Tofa bata sonsa, soyaiyar jini take masa,ba soyaiya ta masoyi da masoyiya ba

wani irin huci yayi yafitar da iska daga bakinsa,kwanciyar da baiyi ba kenan, ya wuce toilet duk da safiya ce, ya d’auro alwala yafara kaiwa ubangiji kukansa.

Washe gari da safe Bayan sun gama break fast, compound suka fita buga ball, kowa yana Nan banda Waheeda data tafi makaranta

Sun dad’e sunayi sannan suka koma ciki, abinci sukaci kowa yakama harkar gabansa, Babban Yaya kuwa shirya wa yayi zaije wajan abokinsa mashkur, Wanda Dama can shine de abokinsa guda daya, sun dad’e tare, hatta 6angaren sana’ah ma Shima mashkur ball yake bugawa, saide kowa da Club d’insa, Amma duk a England suke rayuwar su, yana barin d’akinsa anan falo yaga baqi maqota suna shigowa gidan nasu, Sai a lokacin Ummah take fad’a masa kayan lefen Waheeda ne za’a kawo, ba qaramin kokari yayi ba wajan saita Kansa, daga qarshe yafice yabar gidan, domin kuwa abubuwan qara ta6ar6are masa suke 😖

Baidawo gidan ba saida yamma, a lokacin baqi Wanda sukazo aka kar6i Kaya dasu suntafi, daga Sa’ad da Sa’eed Sai ‘yanbiyu da Hajiya Anty da Ummah ne a falon, ga akwatunan Nan agefe hajiya Anty tana duba kayan da aka zuba aciki, Sai kuma uwar gayya wato Waheeda tana zaune kusa da Hajiya Anty tana shan tea da waya a hannun ta tana karanta saqon Huzaifa Sai murmushi take, gabansa ne yafad’i, ganin da gaske de ankawo kayan lefen Nata, lokaci d’aya ransa yayi baqiqqirin

Shigowa falon yayi duk da yanda yake ganin duhu-duhu kamar Idonsa yana son rufewa 🙆🏻‍♀�

Adede lokacin daya qaraso tsakiyar falon yaji hajiya Anty tana cewa “Hajiya yaushe zamu saka rana akai na Naufal ne? Tunda sunbar mana komai a hannun mu ai yakamata mukai musu kokuwa?”

Cikin sauri yayi hanyar d’akinsa, Babu Wanda ya lura da yanayin sa Sai hajiya Anty, ta Kalleshi cikin tsananin mamaki, yashigo falo babu Wanda yayiwa magana Kuma ya wuce cikin d’akinsa da wannan sauri haka,tasake juyawa ta kalli Waheeda, kanta ta jijjiga tareda cizon lips d’inta, yau d’aya de yakamata ace tayi wani abu akan wad’anan ‘ya’yan nata a matsayin ta na uwa 😳(tofa)

Kallan Waheeda tasake yi, tana jin qaunarta acikin zuciyarta, koda wasa bata son abinda zai ta6a lafiyarta balle yasaka ta cikin wani Hali, Amma Yaya zatayi…..?

Ahankali tatashi tabi Bayan Naufal, tana tura kofar ‘Dakin tana shiga ta ganshi a tsaye yana Kallan p.o.p din d’akin, Kansa ne yaji yasara lokaci d’aya jiri ya d’ebeshi zai fad’i, cikin sauri hajiya Anty ta qarasa tatareshi yafad’o kanta

“subhanallah….Naufal lafiyarka kuwa?”

Idonsa ya runtse, yasaka hannu yadafe goshinsa, but kwata kwata yakasa magana, janyo shi tayi ta kwantar dashi akan gadon, itama ta zauna sannan tad’ora Kansa akan cinyarta

Lallausar sumar Kansa take shafawa, saida taji yad’an nutsu sannan tasake tambayar sa
“meyake damunka?”

Hawaye ne yafuto daga idanunsa, mamaki yakama hajiya Anty, Naufal ne da Kuka yau? 🤔
Tun yana hawaye harya dawo yana kuka harda shashsheka,bata hanashi ba, rabuwa tayi dashi bata hanashi ba, saida yayi me isarsa, sannan yayi shiru Sai Jan zuciya yake, ajiyar zuciya tayi akaro na biyu tace “meyake damunka?”

Cikin rawar murya tamkar ba Babban Yaya ba, yace “Allah idan na rasata mutuwa zanyi…..”

Gaban Hajiya Anty yayi wata irin fad’uwa, cikin sauri ta Kalleshi tace “what….? Wacece?”

Sai a lokacin Babban Yaya yatuna abinda yafad’a, hawaye ne yazubo masa, Sannan yace “Anty ni bazan iya rayuwa da wadda banaso ba, bazan iya Zaman aure da’ita ba….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button