BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga haka tajuya cikin gida tabarshi a wajan, Shima shigewa yayi ransa a6ace

Tunda yashigo ‘Dakin yakasa sukuni, tunani yayi masa yawa, daga qarshe ma tashi yayi yafara had’a kayansa, gobe da safe zai koma England bakin aikinsa, kwata kwata bayajin zai iya zama yana ganinta tana mu’amula da wani namijin bashi ba

Cikin qanqanin lokaci yagama had’a komai,kawai jiran wayewar gari yake

Kamar wasa Waheeda tana kwanciya bacci ya dauketa marar dadi, sakamakon abinda yafaru tsakanin ta da Babban Yaya , haka Shima anasa bangaren, baiji dadin baccin ba, har yanzu wannan kiss d’in ya tsaya masa aqahon zuciyar sa,washe gari kalau tatashi babu wani alamun zazza6i atare da’ita, ‘yanbiyu basa ‘Dakin Sai ita kad’ai take juyinta akan gadon, doguwar Riga ce ajikinta ta bacci Amma me kauri, bata nuna shape dinta ba kwata kwata, saide kana iya ganin tsayayyun breast dinta yanda suka tsaya a tsaye cak tacikin rigar, brush taje tayi tadawo ‘Dakin nasu taga Maya na kiranta awaya, d’auka tayi tace “uwar ‘Yan Fassara ya akayi?”

Maya tace “ke dalla malama yau babu Fassara,Wai baqi mukai daga Abuja, shine wani daga cikin su yace yanaso na, ya tambayi mama yaushe zan gama karatu tace masa nanda wata shida, nikuma gaskiya Waheeda banason aure yanzu, nafison nayi karatu me zurfi, sannan baki ganshi ba Babba nefa, yakai Babban Yaya girma da shekaru, ko kunya babu waini yakeso, Dan Allah tayaya zan iya Zaman aure dashi Aida kunya”

Waheeda takwashe da dariya tace “lalle ma Maya, to miye abun kunya? Tab wallahi karkiji kunya, ba aurenki zaiyi ba? Aiba haramun bane”

Ummah ce tashigo ‘Dakin zata fad’awa Waheeda taje gidan Hajiya Anty takira mata ‘yanbiyu, Sai tajita tana waya, saboda haka saita dakata tagama wayar sannan ta fad’a mata Aiken, ita Kuma Waheeda kwata kwata bataji shigo war kowa Dakin ba
Daga d’ayan bangaren Maya tace “ke bazaki gane ba, novel damuke karantawa duk fa abinda akeyi a novel idan akayi aure Nima fa haka zanyi, wallahi bazan amince ba babu ruwana, ni kunyarsa nakeji, gashi qato”

Waheeda tasake fashewa da dariya tace “nikuma idan nice keko wallahi amincewa zanyi, tabdi to menene aciki ba mijina bane? Har wankansa zan dinga yi, keni har abar tasu zan kama na wanke, qarshe de kenan…..” 🙊🙈🙆🏻‍♀ï¸?

Hawaye ne ya silalo daga idanun Ummah, innalillahi wa inna ilaihirraji’un yanzu Waheedanta ce take wannan maganar?Har abar zata kama ta wanke? Cikin kuka Ummah tace”Waheeda?”

Gaban Waheeda ne yayi wata irin bugawa, kanta ya Sara, cikin sauri ta kashe wayar jikinta yana rawa,ko’ina na jikinta kyarma yake tama kasa yiwa Ummah magana Sai kanta datake girgizawa alamun Bahaka bane

Ummah tayi kukan kura ta kamata tafara dukanta, ihu take tana neman temako Amma babu kowa a gidan, cikin ikon Allah tasamu tafuto daga ‘Dakin, Ummah ta zauna a wajan tana kuka.

tana zuwa compound adede lokacin shikuma yashiga motarsa kenan zai rufeta, ganinta yayi aguje ta nufoshi, kanta babu ko dankwali Sai dogon gashinta daya bazu agadon bayanta, kana ganinta kasan tana cikin mutuqar tashin Hankali,saboda fuskarta ma kadai gumi ne yake futowa ga hawaye sha6e-sha6e tanayi, duk ta rikice jikinta yana rawa kamar mazari, hakan yabawa cikakkun Breast dinta damar rawa kamar Wanda take kad’asu da niyya, tunawa da tayi jiya ransa ya6aci saboda ita, Sai taja ta tsaya cak a wajan tana waigen Bayan ta ko Ummah zata biyota, saboda tasan cewa Shima tana zuwa wajansa Dukan ta zaiyi.

tausayi ta bashi, lokaci d’aya jikinsa yayi Sanyi, duk yanda akai ba qaramin laifi tayi ba, shiyasa take neman mafaka, dama shine Mai taimaka matan, to Shima yanzu tsoron zuwa take, tana tsoron tunkararsa saboda tasan confirm zaiyi mata hukunci, tunowa yayi da fad’an Hajiya Anty, Kuma yasan idan Yabarta ma zataci gaba da haduwa da wannan Yaron ne, yanzu yana hura mata kiss, to gaba gaba kiss din zaiyi mata a aikace, Gara ma sutafi tare kowa ya huta, ahankali tamkar baya son magana yace mata “shigo mutafi”

Ai kamar jira Waheeda take , cikin sauri ta fad’a cikin motar, yayi mata key suka bar gidan
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: BB

Har sukai Nisa da gidan jikinta bai daina rawa ba, yana Kallanta ta gefen Idonsa, Amma be tambayeta wanne irin laifi ta aikata hakaba, Kai tsaye boutique suka wuce, Yabarta a motar yashiga yasiyo mata doguwar Riga dakuma hijab, kawo mata yayi, yafita daga cikin motar yabata damar sauya kayan, dube dube tafara ganin motar me baqin glass ce saita sauya kayan cikin kwanciyar Hankali, saida tagama komai sannan ta qwanqwasa glass din motar, yashigo suka tafi, kwana kwata ko awa daya basu qara ba, jirginsu ya Lula qasar England, acikin jirgin ma tana kusa dashi, saide har yanzu baice da’ita komai ba, itama haka, saima fad’awa da tayi cikin duniyar tunani, haqiqa Babban Yaya yana kaunarta, laifi nede idan tayi masa tasan cewa babu fashi Sai Tasha duka, yau da ace bai dauketa ba ta tabbatar Sai tafi kwanaki bata iya had’a ido da Ummah ba, maganar tayi nauyi ace itace ta fad’a, Amma Kuma akwai abinda zaka iya magana akansa kaida qawarka, wannan tsakanin kune,babu kunya babu 6oye-6oye, ajiyar zuciya tayi, Tajuya ta kalli Babban Yaya taga Hankalinsa yanakan jarida yana karantawa, matsowa tayi jikinsa tariqe dantsan hannunsa na Dama sannan tad’ora kanta akafad’ar sa ta Lumshe idonta, yanajin yanda hannunsa yake taba gefen breast d’inta, Sai a lokacin yatuna bai sako mata da brezia ba, jaridar hannun nasa ya ajiye akan cinyarsa, yajingina Kansa jikin kujerar tareda Lumshe Idonsa, yanajin yanda numfashin ta ya sauya yasan cewa bacci take, duniyar tunani yafad’a,inama ace wannan tafiyar sunada aure Honeymoon zasu tafi? 🤔
Wani irin haushi yaji daya tuna Didat, dakuma Huzaifa da babansa yakira Daddy akan maganar Waheeda, jiyayi komai ya jagule masa, haka yayi shiru daga qarshe Shima baisan lokacin da bacci ya d’auke shi ba.

Da yamma suka sauka, hannunta yana cikin nashi suka shiga mota, sannan suka qarasa gidansa, yanayin tsarin gidan kad’ai Waheeda ta kalla tazama yar qauye, gidan yayi matuqar kyau sosai, an tsarashi yanda ya kamata kamar baza’a mutu ba, motoci Kala Kala kusan guda shida a ajiye a compound, ga wani waje da aka qawata shi da dutsina ruwa yana gudana daga jiki, tafiya suke Amma hankalin Waheeda yana can tana Kalle Kalle har suka qarasa cikin falon bata Kallan gabanta, suna zuwa ta qwace hannunta ta fad’a cikin kujerun falon masu matuqar kyau da tsari tace “gaskiya Babban Yaya gidannan yayi kyau sosai”

Zama yayi akusa da’ita Amma aqasan kafet, ita Kuma tana kan kujera, Kallan ta yayi yace “idan kinaso ai saiya zama mallakinki”

Kallan sa tayi tace “Dan Allah? To Bani shi zakayi?”

Murmushi yayi, dimple d’insa suka futo, yace “sosai ma, saiya zama mallakinki keda yaranki”

Cikin rashin fahimta tace “Babban Yaya, abar wannan maganar, nasan kawai fad’a kake,tab! wayaga Waheeda da Yara, hmm ni yanzu ma yunwa nakeji”

Babban Yaya ya kalleta yace “laifin me kikayi?”

Shiru tayi tafara wasa da yatsun hannunta, ita de bazata iya fad’a masa magana me nauyi irin wannan ba, tayaya zata kalli idon yayan Nata tabashi labarin komai? Aida kunya, qarshan ta shima idan yaji yasaka ta a jirgi yau d’innan ya maida ta gida
Kallan sa tayi tace “babu komai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button