BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi tace “Yayansu ya hanya, maza tashi muje Kaci abinci, gashi can na shirya ma” babu musu ya tashi, saboda yayi missed girkin umman tasa, saboda aturai koda yaushe baida abinci saina gwangwani, Daddy ya kallesu itada Yaron yace “idan kin gama bashi abincin inason magana dashi”

Ummah tace “to Alhaji”

Ita da kanta ta dinga bashi abinci abaki, kowa ya kallesu yasan akwai tsantsar soyaiyar uwa a tsakanin su, Sai shagwaba yake mata abu kadan yace Ummah, ita Kuma Sai lalla6ashi take

Saida ta tabbatar ya qoshi sannan suka koma falon, wajan Alhaji Umar, Babban Yaya ya Kalle shi yace “Daddy nagama, meyafaru?”

Kallan sa yayi yace “menene zai faru banda maganar Aurenka?ai tunda Naga kazo yau nasan kun daidai tane kaida ita Habiban ko? Yaya kukai da’ita?” 😂

Sunkuyar da Kansa yayi yana Sosa girarsa, yama kasa dagowa ya kallesu

Ummah tayi ajiyar zuciya tace “wacce Habiba Kuma Alhaji? Yarinyar da harma munyi magana da mahaifiyar ta awaya sunce sun janye batun auren, nabawa mahaifiyar yarinyar hakuri Amma Sai tace ai habiba tace bazata iya zama da mutumin da bazai bata kulawa ba, to tunda naji haka, kawai saina bata hakuri tunda bansan me suka Tattauna ita dashi a wayar ba, shi yasan meya qulla “tana fadar haka takawar dakanta Gefe tana girgiza qafa

Alhaji Umar ya Kalleshi yace”Naufal”

Ahankali yace “Na’am Daddy”

“bakada lafiya ne irinta maza?”

Maganar tayi masa nauyi, saiya kasa dago Kansa ya kalli mahaifin nasa, Ahankali ya girgiza Kansa yace “A a Daddy”

Daddy yace “okay, iskanci ne yake damunka kenan?”

Nanma yakasa bashi amsa ya girgiza Kansa yayi shiru

Daddy ya ajiye Jaridar hannun sa yace “kaiba 6oyaiyan mutum bane dakake tunanin mutane bazasu saka Maka ido akan aure ba, muna zaune lafiya bazaka ja mana zagi agari ba, zamusa qafar wando daya dakai tunda haka kaza6awa rayuwar ka, Kuma neman aure yanzu muka fara nema Maka, idan ma wani abun daban kake fadawa yaran mutane har suke gudunka kaika Jiyo, mude bazamu fasa nema Maka aure ba, har a wajan Allah muna neman fita haqqin ka ne a matsayin mu na iyayenka akan kayi aure gudun aikata Zina, mutumin banza mutumin wofi, katashi kabamu waje Kuma aure dolen dole Sai kayi “

Runste idonsa yayi, maganganun Daddy sun shige shi sosai, yaji zafin maganar Daddy sosai, tayaya ne zai futo fili yafada musu yarinyar dayake so Bayan tarin matsaloli dakuma qalubalan dazai fuskanta ? Tayaya? Ahankali ya tashi daga gabansu yanufi dakinsa, zuwa yanzu magrib har tayi

Yana shiga dakinsa yaga Waheeda yanda yabarta, gaba daya cinyoyin ta sun sage, Saitayi kamar zata fadi qasa, saita dawo baya taci gaba da abinda take, bacin ran dayake ciki ne yasa yanemi belt yanufeta gadan gadan, tana ganin haka tatashi tsaye tanaja baya, kuka take wiwi tana bashi hakuri Amma idonsa sun rufe saida ya lafta mata belt dinnan ajikinta, qara tasaki tana fadin “Dan Allah kayi hakuri, wallahi tallahi nadena Babban Yaya, Dan Allah kayi hakuri”

Cikin 6acin rai yace “kifadamin waye wannan Yaron dayake neman lalata ki?, harkinashan bakin wani saboda bakida mutunci ko? “

Belt din tariqe idanunta cikeda hawaye tace “Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba, idan nasake Kamin komai ma nayarda”

Fizge belt dinsa yayi yasake zuba mata shi ajikinta, zafin dataji ne yasa batamasan lokacin data tashi ta rungume Shiba,yana jin yanda Albarkatun qirjinta suke tsikarinsa saboda bata saka bra ba, lokaci daya jijiyoyin jikinsa suka kar6i saqon, 🙈Amma tsananin 6acin ran dayake ciki yasa baza’a gane hakan ba
Fizgeta yayi daga jikinsa yasake Dora mata wani belt din, cikin kuka tace “Akofar fada yake, gidan Alhaji Hamza”

Tsaki yasaki tareda wullar da belt din qasa yace “Stupid”

Ummah tana Jiyo kukan Waheeda tata6e baki tace kanku akeji kunfi kusa, Daddy ne yake tambayar ta meta masa, anan ta fada masa komai ciki harda wayar Babban Yaya data daga batare data saniba

Futowa yayi daga Dakin yabarta anan, su Ummah suna zaune har lokacin, suna ganinsa yafuto fuskar sa a daure, yana shirin fita daga falon, anan yaci Karo da Yanbiyu harsun dawo daga islamiya kasancewar anfara Kiran sallar magrib, yanda sukaga fuskar sa sunsan ransa a6ace yake, cikin sauri suka bashi waje yafice daga falon

Suna qarasowa falo suka gaida Daddy, Shima ya tashi yayi shirin tafiya masallaci, Dakin Babban Yaya aka bude ahankali, kamar me koyon tafiya hake take takawa, idanunta sun kumbura sunyi jajir, Sai yarfe hannunta take, hawaye wani nabin Bayan wani, Ahaka tashige cikin dakinsu babu Wanda yace da’ita uffan daga Ummah har Yan biyu, tana zuwa daki wani irin zazza6i yafara kokarin rufeta, kawai zubewa tayi agadonsu taja Bargo tarufa.😂

Da daddare duk suna zaune afalo gaba dayansu suna kallo, har wajan karfe takwas da rabi Waheeda bata futo falo ba
Babban Yaya yana zaune yana danne danne a wayarsa, Sa’eed da Sa’ad Kuma suna gefen sa suna bashi labarin ‘yanmatan dasuka hadu dasu wasu yanbiyun suma, magana suke masa Amma hankalinsa yanakan wayar dake hannun sa, ahankali yake amsa musu, su yanbiyu suna zaune suma, suna Kallan film din da’akeyi, Ummah da Daddy suna can Gefe suna zance qasa qasa, Daddy ya kalli Babban Yaya yasake yin qasa da murya yace “ke baki lura da abinda nafada miki ba? Ki lura dashi sosai qarya yake mana bashida lafiya”🤣

Itama Ummah Kallan sa tayi tace “Aina yarda Alhaji, kunyar fada mana kawai yake, Amma duba fa yanda ‘yan’ uwan suke bashi labarin yanmatan su Amma yayi mursisi, maza dason zancen yanmata Amma shi kaduba kagani fa suna masa magana kamar sunayi da dutsi”

Daddy ya girgiza Kansa yace “dole zan dauki mataki hajiya”

Shikuwa Babban Yaya baisan sunayi Bama 😂Kallan intisar yayi yace “ke tashi ki kira wannan yarinyar tazo tayi kallo”

Intisar tasan da Waheeda yake, ita kadai ce bata futo falo ba, cikin sauri ta nufi dakinsu, tana shiga tahau kan gadon ta yaye bargon da Waheeda tarufa, bude idon ta tayi ta kalleta, duk yanda Waheeda take gane yanbiyu, take banbancesu dukda tsananin kamar dasuke, yau kasa ganesu tayi,🤣 intisar ce tazo kiranta Amma Waheeda tana qare mata kallo cikin wahala tace “Ihsan Dan Allah ki temaka ki taro ruwan zafi a toilet kizo ki gasa min cinyoyina, jikina yayi tsanani bazan iya tashi ba”

Dariya ta kama Intisar, saita danne gudun karsuzo suna fada, tace “Babban Yaya ne yace kifuto kiyi kallo kowa yana falo banda k…..” kafin ta qarasa magana taga Waheeda ta duro daga kan gadon 😂
Kokula sauran zancen batayi ba tafice daga Dakin, tana zuwa falon babu Wanda ta nufa Sai shi, har gefen qafarsa ta zauna, hawaye yazubo daga idanunta, a Hankali tace” Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri kaji…. “

Babu Wanda yasan metake fada masa, saboda ahankali tayi masa maganar, Shikuwa banza yayi yarabu da’ita, hawayen tasake gogewa tace”kaji” memakon yabata amsa saiya tashi daga falon yashige dakinsa, haka ta zauna a wajan tana Kallan dole, saida takusa minti talatin tana kallo Amma bata fahimtar komai, Dan haka tatashi Takoma dakinsu tafara gabatar da sallah

Karfe bakwai daidai afalo tayi masa,yayi kyau sosai cikin manyan Kaya, yanda yaqara cika da kamala zakace yanada aure, agogon hannun sa ya kalla yadubi Ummah yace “kice musu Idan sun gama Ina waje Ummah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button