BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

yau su yanbiyu sukai candy Sai abun yahad’u ya zama kamar wani ‘Dan qaramin biki ake, har zuwa lokacin Babban Yaya yana d’a kinsa a kwance, duk abinda yake faruwa hajiya Anty ta fad’a masa ta waya saboda taje ‘Dakin nasa taji shi a rufe,saide duk text din data masa babu guda d’aya da yayi mata replay

Acan makaranta kuwa, Waheeda saida ta jira su ‘yanbiyu suka gama party a school sannan suka taho, yau driver bai d’auko suba, da kansu zasu taho, suna futowa daga get din makarantar, wani matashi me cikar kamala da kyau, gashi ‘Dan Gayu, ya doko musu sallama, Ihsan ce ta amsa masa, yajuya yana Kallan Waheeda yace “qanwata idan babu damuwa Dan Allah inaso kibani number ki”

Waheeda ta tuna karonta da Babban Yaya saita qi bashi amsa tajuya masa baya, murmushi yayi yace “haba qanwata, kamar Wanda zan sace ki?”

Intisar tayi murmushi tace “Gaskiya Yayanmu yahanamu kula samari, Amma zamu baka number sa, idan ya amince shikkenan”

Murmushi yayi yace “gaskiya kun birgeni, daga Gani daga gidan tarbiya kuka futo, insha Allah zan nemeshi, yabani Dama indinga zuwa muna gaisawa da qanwata”
Yaqarasa maganar yana Kallan Waheeda, itade ba tace masa komai ba, saboda idan ta tuna Babban Yaya da police station din dataje, da 6atan wayarta, saitaji duk samarin sun fice mata Arai

Number Babban Yaya Intisar ta bashi, sannan suka tafi, duk inda sukabi Sai an Kalle su, kyawawan yanmata su uku, kana ganinsu kasan ba hausawa bane, napep suka Hau yakaisu har ‘kofar gida, suna shiga falo suka tarar da Hajiya Anty taci kwalliya, wuyan ta da kunnanta Sai qyallin gold suke, matar ta’iya daukan wanka na fitar Hankali,yar Gayu ce ta qarshe, raba Goro da alawa take, ga Kuma kudi Nan agaban ta dami dami, zama Waheeda tayi akusa da ita, jikinta yana gogar Nata.

Tad’auko alawar guda d’aya tana sakawa a bakinta, sannan tacire hijabin jikinta, dogon gashinta ya baiyana,kwanciya tayi tareda d’ora kanta a cinyar hajiya Anty,sannan tace “Anty kayan me kike rabawa”

Ummah tace “bansan yaushe zakiyi Hankali ba waheeda, kin sameta tana aiki memakon ki temaka mata, saide kihau cinyarta”

Bakinta ta turo gaba cikin shagwa6a tace “Ummah Anty cefa”

“eh saboda Anty ce saiki kashe mata cinya”

Hajiya Anty tayi murmushi tace “Goron saka ranar Yayanku ne, yau ansaka masa rana,su Sa’eed Kuma ankai musu gaisuwa”

Da Waheeda da ‘Yanbiyu lokaci d’aya suka matso kusa da Hajiya Anty sukace “Babban Yaya?”

Hajiya Anty ta d’aga musu Kai, haba ai da gudu Waheeda tayi d’akinsa, tura kofar tayi tashiga ta ganshi a kwance, ya rungume Fillo a qirjinsa, cikin murna ta fad’a Kansa tana sakin ihun murna, yana jin yanda aka fad’o Kansa yasan ba kowane zaiyi masa hakaba Sai ita, yatsina fuska yayi sannan ya tureta daga jikinsa yace “Yaushe zakiyi Hankali ne?”

Cikin farin ciki tace “Babban Yaya, Dan Allah da pink colour da blue, dakuma green wanne ne yafi kyau?”

Cikin mamaki ya daga Kansa ya kalleta batare daya tashi ba, yace “meyafaru?”

Dantsan hannun sa takama ta riqe, tace “sonake kafadamin wanne ne yafi kyau saimu dakko ankon bikinka”

Wani irin baqin ciki ne yakama shi,cire hannunta daga jikinsa yayi,ya maida Kansa fillo cikin damuwa yace “ni banason auren”

Bata lura da yanda yake rabata da jikinsa ba tasake matsawa jikinsa tace “Meyasa Babban Yaya?”

Juyowa yayi yana Kallan ta, yace “Akwai yarinyar danake so”

Cikin farinciki tace “wayyo Allah, Babban Yaya Dan Allah wacece?”

Kallan ta yayi yakasa magana, zuciyar sa ce take zugashi akan yafad’a mata, to Amma tayaya zata dauki maganar?, qalubalen dayake gabansa dangane da fad’a mata wannan maganar ba qarami bane
Waheeda tace “Babban Yaya nikake kallo, wacece yarinyar?”

Ajiyar zuciya yayi yace “Sunanku d’aya, kamar ku d’aya”

Wani irin fari tayi da idonta tace “Dan Allah Babban Yaya kakaini wajan ta mugaisa, ka nuna mata ni, kafad’a mata nice qanwarka wadda kafi so”

Lumshe idonsa yayi yabud’e, sannan yace “zan kaiki, Amma karki fad’awa kowa wannan maganar, sirri”

Dariya tayi tace “bazan fad’a ba, Babban Yaya kasan me? Wallahi inaso kayi aure, sonake Naga matarka ta haihu, muga dawa yaran zasuyi kama”

Tashi yayi zaune ya kalleta yace “ke har farinciki kike da bikin ne?”

Tace “sosai ma, wallahi inaso kayi aure”

Cikin wata irin gigitacciyar tsawa, wadda bata ta6ajin yayi mata irinta ba yace “tashi kibarmin dakina, tunda farinciki kike da aure na”

Tace “Babban……”
kafin ta qarasa yatashi tsaye cikin fishi kamar zai rufeta da duka, tana ganin haka tatashi tsaye, jikinta yafara tsuma saboda tsoro, qwalla ce tataru a idonta, tafuto daga Dakin cikin sanyin jiki

Ayi hakuri da wannan ba yawa, muna tayaka murna Babban Yaya 😂

Bazanyi zagi ba, Amma duk wacce ta karanta batare data biyaba, nabarta itada mahaliccinta, saboda babu yafiyata aciki

Amnah
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: Tana fita daga d’akin ya zauna akan gadonsa tareda dafe Kansa da hannun sa🤦🏻‍♂ï¸?
Ita farinciki ma take, meyasa bazata fahimceshi ba? Yace sunansu d’aya, yace suna kama, tayaya zai futo fili yafad’a mata gaskiya? Tayaya zata fahimce shi? Mezai fad’awa iyayensu idan suka ji daga inda maganar tafuto?

Kansa ne ya Sara, yazube akan gadon yana fadin “hasbunallahu wa ni’imal Wakeel”
Bayajin zai iya rayuwa batare da Waheeda ba, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, ya cusa Kansa cikin fillo yana kuka babu me lallashi kamar ba Babban Yaya ba 😂

Tana barin ‘Dakin nasa, d’akinsu tashige, ta zauna agefen gado tana Kallan p.o.p din ‘Dakin,
‘yanbiyu ne suka shigo, intisar tace “kekuma lafiya kikayi wani iri kamar marar lafiya?”

Cikin damuwa tace “Babban Yaya ne”

Ihsan da intisar sukasa dariya, Ihsan tace “to me yamiki Kuma?, kema da rawar Kai daga jin ansa masa rana kika d’iba da gudu kikaje”

Kallan su tayi cikin damuw tace “Wai baya son auren ne”

Inti tace “to yanzu ke menene naki aciki? Hanawa zakiyi? Mema za’ai da wannan Ummin, ni wallahi Bana sonta, kullum kaganta tana magana da maza”

Ihsan tace “wallahi kuwa, inajin su Daddy basu Sani bane shiyasa, nifa shiyasa banyi murna ba danaji ance itace, Amma Waheeda uwar rawar Kai harda tafiya wajan sa da gudu, dama yasani yamiki shegen duka”

Waheeda tayi shiru tana tunani, tana so tace musu yafada mata yarinyar dayake so to Amma Kuma data tuna yace mata sirri, Saitayi shiru, tayi ajiyar zuciya tace “nikam Ina sonta, tunda Babban Yaya zata aura, mutumin dayake taimako na aduk halin Dana kasance tayaya zanqi matarsa?”

Ihsan tace “to Allah yabada sa’a Waheeda, ke kikaga Zaki iya”

Daga Nan sukai shiru kowa da abinda yake saqawa Aransa

Ita Waheeda tana tunanin Babban Yaya, duk yanda zaiyi mata fad’a tana shiga damuwa muddin ta ganshi acikin damuwa, saboda Shima baya barinta acikin matsala, ta damu da damuwar sa sosai, batasan meyasa ba, wani lokacin zai mata hukunci akan laifin da tayi, gashi de shine ya6ata mata rai ta hanyar yimata hukunci, Amma Hankalinta baya kwanciya Sai ta bashi hakura taga ya haqura tukunna, gashi yanzu yana wani Hali saboda auran Ummi, batasan ta wanne Hali zata taimaka masa ba,zuciyarta tabata shawara akan tatayashi da addu’ah, haka ta dauki shawarar zuciyarta

Haka Babban Yaya ya wuni ad’aki yaqi futowa, Ummah Kota Kansa batabi ba, saboda tasan fishin nasa akan aure ne, Kuma aure Kam babu fashi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button