BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sauri ta zayyano masa sunayen, wayarsa ya dauka ya turawa principal din makarantar sunayen sannan yayi masa qarin bayani aqasa, dago Kansa yayi ya kalleta yace “saboda ke mahaukaciya ce, ashe a makarantar ma zuwa kike kina nuna musu jikinki ko? Ban hanaki yawo babu hijabi ba?”

Girgiza kanta ta farayi cikeda tsoro tace “Allah Ina saka hijab dina”

“qarya kike bakya sakawa, idan kina sakawa ma to cirewa kike, yanzu inda da abokina muke tafe haka Zaki budemin nagani agaban sa ko? Kinaso ki kasheni kiga bayana kihuta, ai haka kike so ko?”

Hawayene suke zuba a’idonta, wani nabin wani, ta girgiza masa Kai tace” Allah Babban Yaya bazan nunawa kowa ba, kaima bansan na nuna Maka ba, Kuma babu wani namiji danake fatan yagani a yanzu”

Cikin 6acin rai yace “koma de menene, karki sake min maganar wani agabana, nafada miki”

Haka Waheeda taja bakinta tayi shiru, har suka qarasa school dinsu ta da bai qara mata magana ba itama bata masa ba, Kai tsaye office din director sukaje, yasaka Waheeda ta tsugunna tabasu hakuri, Sannan yaroqi alfarma abarta Taqarasa karatun ta, kasancewar yanzu sun huce da laifin data musu, dakuma yanda suke ganin qimar Yayan Nata, shiyasa babu 6ata lokaci suka kar6eta, yawancin malamai suna aji shiyasa wannan Karon bai tsaya sauraren mutane masu masa magana ba, dakuma irin yanayin dayake ciki na 6acin rai.

Waheeda tana bayansa,zata rakashi wajan motar sa, Maya ta hango tana tahowa wajan su, Waheeda tace “Babban Yaya kaga qawata Maya”

Yana kokarin shiga mota yajuyo ya kalleta yace “Sunanta kenan?”

Tace “Yes, Maryam Ahmad, Yusuf Amin, shine muke ce mata Maya”

Kafin Yayi magana ta qaraso, cikin murna ta rungume Waheeda, tasake ta ta gaida Babban Yaya cikin ladabi, Nan da Nan yayaba da Hankalin yarinyar, yasan idan Waheeda tana tareda ita, zata qara Hankali, amasawa yayi yace “kudinga karatu sosai”

Dariya takama Waheeda Amma saita danne, Wai kudinga karatu sosai, wannan shine fadan da akewa dalibai, Maya tace masa “insha Allah Babban Yaya”

Ta kalli Waheeda tace “Waheeda zan tafi gida, Sai wani lokacin”

Waheeda tace “Naga ba’a tashi ba, meyasa Zaki tafi?”

Idanunta ne suka kawo ruwa tace “Waheeda kudin School fee’s ne baba bai kawo ba, shine sukai kora”

Tausayinta yakama Waheeda, tasan Maya da naci akan karatu, tanason karatu sosai, cikin sanyin jiki tace “kiyi hakuri Maya karkiyi kuka”

Babban Yaya yata6e bakinsa tareda ajiyar zuciya, Yara qanana suna wani Iyayi saika ce Wanda suka San ciwon kansu 🤣
Motarsa yabude ya Dauko kudi dami biyu yan dubu dubu, aqalla zasu Kai kusan dubu Dari biyu, yabawa Waheeda yace “kibata”
Daga Nan yashige mota tareda ficewa daga makarantar

Maya ta kalli Waheeda suka rungume juna cikeda murna, daga Nan suka tafi Class dinsu

Tafiya yake amota yanaso yaje gidan hajiya Anty tun kafin ta masa qorafi baya zuwa, wayarsa ce yaji tana ringing, dauka yayi tareda karawa a kunnansa, daga d’ayan ban6aren principal yace “Kayi hakuri yalla6ai, abun baikai da Sai ansako hukuma aciki ba, insha Allah zansa Akira yaran a yimusu hukunci daidai da abunda suka aikata, sannan dole iyayensu zasu San abunda suke aikata wa, ni bazasu 6atamin makaranta taba”

Babban yace “Yarage Naka, Amma muddin baka dauki mataki akan yaran nan ba, to zaka ganni a cikin makarantar ka” yana fada masa haka yakashe wayarsa

Wata wayar ce tasake shigo wa, yayi tunanin principal ne yasake kiransa, cikin masifa ya daga yace “Wai ya akayi ne Kuma?”

Daga d’ayan bangaren akace “babu abinda akayi Saide wadda za’ayi yanzu, Naga alama baka gane me magana ba, to Abubakar ne yayan mahaifin ka Umaru” 😂

Babban Yaya yadafe Kansa, ya tsaida motar agefe titi yace “Baba Ina kwana?”

“daban kwanaba zaka ganni ne Naufal balle harna kiraka awaya?”

Babban Yaya yace “kayi hakuri baba”

Baba Habu yace “Magana nakeso muyi dakai ta fahimta, nasan idan ka 6oyewa iyayenka Toni bazata 6oyemin ba, tunda nasan cewa akwai alkunya tsakanin d’a da mahaifi, Naufal kafadamin gaskiya idan kasan bakada lafiya munan damuke qauye akwai sassaqe yana Nan Kala Kala saina had’o Maka shi na aiko kafara gwadawa ko za’a dace “😅

Girarsa guda d’aya ya Sosa da key din Motarsa , yace”Baba lafiya ta kalau”

“to idan lafiyarka kalau meyasa kake gudun aure?”

“Akwai wacce nakeso Baba”

Yafadi hakan Kansa tsaye

Baba Habu yace “to Alhamdulillah, masha Allah, to kokai fa, a’ina yarinyar take? Yar wanne Gari ce?”

Shiru yayi, yakasa Bawa yayan mahaifin nasa amsa, Sai can yace masa “Baba Nima bansan inda take ba”

Cikin masifa Baba Habu yace “zancen banza zancen wofi, wannan ai shirme ne, tunda haka kake so ai shikkenan, ka shirya kaje kaga Nadiya yar gidan abokin uncle dinka Usman, Usman yacemin yarinya Tariga tasanka, saboda haka Sai kaje kaganta kaima” dif yakashe wayarsa, yabar Babban Yaya da waya Akunne

To koyaya zata Kaya tsakanin sa da Nadiya?

Masoyan BABBAN YAYA Ina godia sosai, nayi tunanin bazaku sayi littafin ba ☹️☹️
Amma abun mamaki tun kafin free page yaqare masu turo 400 sunfi masu 200 yawa, nagode Allah yabar zumunci

Amnah El Yaqoub ✍�

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:49 – Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

9&10

Bakomai ne ya tsaya masa Arai ba Sai yanda yace yarinyar tariga tasan shi, hakan yana nufin idan yaje zata soshi tunda Dama tariga tasan shi, shine bai Santa ba, duk yanmatan da ake had’ashi dasu babu wadda ta sanshi, koda sun ganshi ma baya fadar sunan da aka sanshi dashi saide yace musu sunan sa Naufal, Amma ita wannan ta wacce hanya zaibi yarabu da’ita? Bashida burin auren mace biyu, kamar yanda ya tashi yagani a gidansu Ummansu ita kadai ce, Hajiya Anty ma ita kadai ce, to ita da bata haihuwa ma mijinta yayi hakuri ya zauna da’ita, to shida ba mazauni ba tayaya zaiyi ta aurar ‘ya’yan mutane yana tafiya harkar qwallo?

Ajiyar zuciya ya sauke, yanufi gidan Hajiya Anty, gidan yayi kyau sosai,tsarin gidan komai da komai irinna Ummah ne, saide furnitures dinne kawai suka banbanta

Tana Sanye cikin atamfa, tariqo mayafin a hannunta, wuyanta da yatsun hannunta duk sunsha gold,tayi kyau sosai abinka da mace yar Gayu, Car key ne a hannunta tana kokarin fita sukaci Karo da Babban Yaya, tace “A a, yaushe agari?”

Bai bata amsa ba Sai kokarin shigo wa falon da yake, bayansa tabiyo suka dawo falon suka zauna, Kallan ta yayi yace “Anty fita zakiyi ne?”

“eh zan fita, akwai meeting din da zamuyi karfe daya”

Ajiyar zuciya yayi “ke Anty babu ruwanki bakida damuwar komai”😔

“Kai din damuwar menene a ranka?”

Goshinsa ya dafa yace “gatanan dayawa Anty, yau matsalar Waheeda gobe matsalar ku”

Dariya tayi tace “To Waheeda matsalar ta ai takace, kaida ita ai qawaye ne, Kuma inda Sabo kun saba, qanwar kace babu yanda zakayi da’ita, mukuma tamu matsalar ai bazaka kirata da matsala ba, tunda mune akan gaskiya, Naufal har wanne lokaci zaka dauka babu aure? Ko so kake Sai yanbiyu maza sunyi aure sannan zakayi? Maryam fa tayi aure harda takwara anyi Maka, kaikuma gaka Nan gemai gemai dakai babu aure “

“Anty shi aure lokaci ne”

yafadi hakan cikin damuwa

Tace “Hakane, Allah ya nuna mana Naka lokacin, yaushe kazo qasar?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button