BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

idanunta Babban Yaya yake kalla a zahiri, Amma abad’ini yayi Nisa cikin tunani, inama zata soshi kamar yanda yake sonta?koda yaushe zuciyarsa tana fad’a masa cewa, bashida mata Sama da’ita, ita din tasa ce shi kad’ai, but tayaya hakan zai kasance?

To Alhamdulillah free page yazo qarshe 🥱

Gashi zan Dena yimuku posting Baku fadamin suwaye iyayen Naufal da Waheeda ba😂😂

Dama nafada muku BABBAN YAYA na kudi neko?
Ina Wadanda suke buqatar jin qarshan labarin? Kwamacala tana gaba aradu, yanzu aka fara wasan 💃💃💃

Da abaka labari gwara ka bayar 👇🏻

200 posting daya a rana

VIP 400 posting biyu a rana

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaku turo shedar biya ta wannan number👇🏻
08033300034

Ga masu kira, text message, whtsapp, duk ku nemeni ta wannan number👉🏻 08033300034

Next Novel SHAHAB…..

Salonsa daban yake, zaizo muku bada dadewa ba 💃💃💃

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: Jikinsa ne yayi Sanyi Bayan tunawa da irin qalubalen dayake gabansa akan hakan, ahankali yakawar da fuskar sa Gefe, sannan ya tashi zaune yakama hannunta yariqe yana kokarin tashinta, jitayi kamar bashida qarfi, taga jikinsa yayi Sanyi, shi kuwa Babban Yaya yanayin daya shiga ciki ne bai gama sakinsa ba, ashe haka akeji? Kokuma de shine yaji dadin sosai saboda wadda yake soce yayiwa kiss din? Tashi tayi zaune, har zuwa lokacin hannunta cikin nasa, tana ‘Dan qaramin Tari kad’an, a taqaice yace “Sannu”

‘Daga masa Kai tayi tace “Babban Yaya da yanzu na mutu, nide mubar Garin Nan, tsoro nakeji”

Fuskarta yariqe yana Kallan qwayar idonta yace “kidena cewa Zaki mutu, banaso”

Murmushi tayi masa, kafin tace wani abu su Yahya suka qaraso,’yanbiyu suka jata zuwa gida,tafiya suke a hanya gaba d’ayansu suna jajantawa juna akan abinda yafaru

Da daddare kasa bacci yayi, haka ya dinga juyi akan gado hannun sa yana kan mararsa datake masa wani irin mugun ciwo, yana tuno laushin lips din Waheeda saiyaji kamar yaje yaqara😳🙆🏻‍♀ï¸?, Sai gab da asuba yasamu bacci ya d’auke shi Bayan ya kwanta rub da ciki, saida ya makara sallar asuba, baida tsarki, saida yayi wanka sannan yayi sallah sakamakon wani irin mafarki da yayi na Waheeda me dadi.

Sai wajan shad’aya
‘yanbiyu suka kawo masa abinci, yanaci kuwa yafuto tsakar gida d’aukeda kayansu, koda ace Waheeda batace tanajin tsoron Garin ba, ya zama dole sutafi, bazai juri rashinta atare dashi ba, idan ta mutu a wannan qauyen shi waya kama kenan? 😂🤔

Baba Habu yace “a a, ya naganka da Kaya? Ina zakaje”

Kasa yayi da Kansa yace “baba anmin waya ne a wajan aiki, Ana nemana, shiyasa zamu tafi”

“to Amma tafiya babu shiri Naufal? Meyasa bazaku Bari Sai goben ba?”

Murmushi yayi yace “baba zamu sake dawowa”

Haka yahad’a kan qannansa kowa yahad’a kayansa, suna saka kayansu cikin booth din motar wasu samari suka qaraso wajan Babban Yaya suka bashi wata latter, dubawa yayi sannan yayi murmushi, ya Kalle su yace “inde kayan Ball ne, zan turo muku dashi, harda takalma”

Ihu suka Hau yi kowa yana qara yimasa godia, inna Haajara tacika su da kayaiyakin qauye su manshanu da Kuka, dakuma kindirmo, haka suka tafi cikeda kewar ‘yan’uwan su su Yahya.

Washe Garin ranar dasuka dawo daga qauye, Daddy da Ummah da Uncle Usman suna zaune afalo suna kallo, Sa’ad da Sa’eed suka shigo falon kansu aqasa, agaban Ummah suka zauna, uncle Usman yace “to ‘yanbiyu mekuke sone Naga Kuna sunkuyar da kanku?”

Sa’eed ya Sosa qeyarsa yace “Uncle Dama… Dama uncle…” saikuma yayi shiru yana zungurin Sa’ad

Daddy yayi dariya yace “tunda kaga haka ai zancen bazai wuce na neman kudi ba zasu sauya mota, aikinsu kenan, kuje wajan yayanku yabaku, shine me kudi”

Murmushi sukayi, Sa’eed yace “Daddy Bahaka bane, dama gidansu Hassana ne akace muturo akai kudin gaisuwa”

Uncle Usman ya gyara zama yace “a a, babbar magana, kuce abun yazo” 😃

Sake sunkuyar da kansu sukai cikin kunya

Daddy yayi murmushi yace “Kundage de Kuma yanbiyu zaku aura kamar ku,kuje ku kiramin yayanku, ai dashi yakamata kufara magana, shikuma saiya fad’a mana”

Tashi sukai suka nufi wani daki kusa da ‘Dakin Babban Yaya, babu komai acikin ‘Dakin Sai kayan Ball, dagashi Sai qananun Kaya da ball, yana bugawa shi kadai, zama sukai suna Kallan sa, daina abinda yake yayi, ya dawo kusa dasu ya zauna yace “twins ya akayi ne?”

Sa’eed yace “Babban Yaya mun dade bamuyi Ball bafa”

Kallan sa yayi yace “shine matsalar?”

Sa’ad yace “Babban Yaya wallahi ba’ita bace, gidansu Hassana da Hussaina sunyi magana, mu turo akai gaisuwa, Dan Allah Babban Yaya kacewa su Daddy a saka harda ranar ma gaba daya”

Babban Yaya ya saki murmushi yace “um Um… Ashe aure kukeso shine kuka qi magana?”

Dariya sukayi dukansu, yace “to shikkenan, idan nagama zanyi magana dasu Daddy”

Godia sukayi masa sannan suka fice daga Dakin, yana ganin fitarsu yazube a wajan, yafada duniyar tunani, Sai yaushe ne matsalar sa zatazo qarshe ne? 🤔

Ko awa d’aya bai qaraba yanufi wajan su daddy Bayan yayi wanka yagama shirya wa, Kansa yana qasa, Bayan yagama yimusu bayanin abinda yakawo shi, uncle Usman yace “yanzu Kai haka kaza6awa rayuwar ka? Maryam qanwar ‘yanbiyu tayi aure, abar wannan maganar ma, ita mace ce, toga ‘yanbiyun suma sunyi magana, Naufal, yakamata ace ka nemawa kanka mafita, zamanka haka bazai iyu ba, musuka fara fad’awa maganar, muka turo su wajanka, munyi tunanin hakan zaisa kaima ka kawo taka Sai ahad’a ayi gaba d’aya, ashe har yanzu kana Nan kakasa tsaida magana d’aya, maganar gaskiya bazai iyu su Sa’eed su Riga ka aure ba, muna so Kai kafara saboda kaine Babba, tayaya zasu auri Yara sukawo su gidan Nan, Yara su dinga gaisheka a matsayin yayan mijinsu suna ganinka babu aure ba?, saboda haka mun yanke shawara, bazamu hanasu Kai gaisuwa ba, Amma babu maganar sa rana, saka rana Sai Bayan bikinka, kaikuma za’a saka ranar ka yanzu, Kai saka rana, sukuma Kai gaisuwa, Bayan bikinka Sai ayi nasu, akwai yarinya me Hankali sunanta Ummi, kama Santa, Nan maqo tanmu take, Bama saikaje ganintaba bare Asamu matsala, kawai za’a saka ranar, tashi katafi “

Tunda Uncle Usman ya fara masa magana yarasa gane Ina yake zaune? Jiyake kamar a mafarki Wai shi za’a had’a da ummi, yarinyar da kowa ya Santa batada kunya, sude burinsu shine yayi aure Amma babu ruwansu da yarinyar ta dace dashi ko bata dace ba, tasa qaddarar kenan kullum idan yazo Nigeria Sai anyi masa maganar aure, Bai iya cemusu komaiba Sai “to Uncle” daga Nan yatashi yanufi d’akinsa yana tafiya yana had’a hanya, domin kuwa wani irin baqi-baqi yake Gani, yana bude kofar d’akinsa yana kokarin shiga har bige goshinsa yake, Amma baidamu ba, abinda yake ji acikin zuciyar sa yafi bige goshin zafi,kulle Dakin yayi yafad’a kan gadon sa, wani irin hawaye me zafi ya silalo daga idanunsa, lokaci daya yaji duk duniyar tafita a ransa
Bashida wata sauran dabara illa ya kar6i ummi a matsayin matarsa, basu bashi Dama yaje ya ganta Bama bare yayi wata dabarar daya saba yarabu da’ita, tabbas yasan Ummi, yarinyar akwai muni ba laifi, ga rashin kunya, jikinta ne kawai me kyau, tsakanin gidansu da gidansu Babban Yaya gida uku ne a tsakani


Abu kamar wasa washe gari aka saka ranar Babban Yaya da Ummi ,wata uku kacal,Amma ba’a saka date din Daurin auren ba, Sai ankai lefe,duk wani hidima da akeyi na al’ada Daddy ne dakansa yayi ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button