BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Maya ta Jinjina kanta, tafara wani tunani, ta kalli Waheeda tace”hakane Kam, saikaje ka auri me sikila ma baka Sani ba, Gara kuje din Kam, wanne Asbiti zakuje? “

Zuciya d’aya Waheeda tace”na fad’awa Huzaifan de, yacemin tunda gobe zamuje wajan gyaran jiki,jibi Sai muje asbitin, akwai asbitin da ake duba ‘Yan gidansu, (Al’islah Hospital) private ne, can nake tunanin zamuje”

Maya tace “to shikkenan, Allah yakaimu goben, saina shigo”

Daga Nan sukai sallama, kowa yatafi gida

** *** **

Washe gari da safe Maya a gidan Hajiya Anty tasamu Waheeda, anan sukayi breakfast sannan Waheeda takira Huzaifa yazo yad’aukesu suka tafi

Maya tana gidan baya, Waheeda da huzaifa suna gaba, Sai kashe mata murya yake suna soyaiya, hankalin Maya yana kan wayarta tana daddannawa, a gidan da Hajiya Anty ta fad’a musu yasauke su, sannan yatafi, gidan suka shiga aka fara yimata gyaran jikin yanda ya kamata, tsawon lokaci suka d’auka ana mata abu d’aya,Bayan angama gyaran jiki matar tabata wasu magungunan na mata, ta zaunar da’ita a gabanta, saida taga ta Shanye sannan,wani irin qyalli Waheeda tafara, gyaran yau ma kenan, ita kanta Maya Kallan ta take tana mamakin yanda tayi kyau, to rana d’aya ma kenan idan kuma aka gama gyaran gaba d’aya Yaya Waheeda zata kasance? 🤔

basu gama da wuri ba Sai wajan yamma, sukayi mata sallama saikuma gobe idan sun dawo

Allah ne kawai yakawo su gida lafiya, domin kuwa Huzaifa yana ganin irin gyaran da akayi Waheeda saiya susuce bashida aiki saide yajuya ya kalleta, yana driving yana Kallan ta, Maya ta godewa Allah data ganta a kofar gidansu sunzo lafiya, tana futowa daga motar ta leqasu ta window tace “to wallahi ango kakula da qawata sosai, nide na godewa Allah tunda ankawoni gida lafiya”

Dariya huzaifa yayi ya shafa sumar Kansa, yasan Sarai taga halin daya shiga ne shiyasa tayi masa wannan maganar, Waheeda ma tayi mata murmushi tace “to Sai munyi waya qawata, gobe karki shirya da wuri, saida yamma zamuje, saboda da safe, Asbiti zamuje”

Maya tace “to shikkenan qawata, Allah yakaimu, kikula mana da angon namu”
Ta qarasa maganar cikin tsokana

Huzaifa yaja motar suka tafi, har zuwa lokacin Maya tana tsaye a’inda suka sauketa, saida taga sunbar layin gaba daya,memakon tashiga gidansu sai ta tare adedeta tashiga,tayi masa kwatance sukad’au wata hanyar

** *** **

Tafiya suke cikeda nishadi, kana ganinsu kasan suna cikin tsantsar farinciki, qamshin turaren sa yahad’u da Nata ga Kuma sanyin esi Sai abun yaqara bada armashi
Kallan sa tayi “Bae kadinga sauri muje mana, kana driving kamar baka so”

Kallan ta yayi “so kike nayi sauri Dan muje asbitin mugama da wuri kitafi kibarni ko?”

Murmushi tayi batare da tace komai ba, yasake Kallan ta yace “inason murmushinki Waheeda, yana birgeni, musanman idan Naga wannan dimple din….”

Kallan sa tayi “da gaske? Aikuwa koda yaushe zan dinga yima ka shi, saboda inci gaba da birgeka a koda yaushe, Dan banasan wata Rana kaga wata yarinyar itama ta birgeka”

Kafad’a ya d’aga yace “ai Bana tunanin akwai yarinyar dazata birgeni Bayan ke Waheeda, nifa banga amfanin zuwa wannan text din namu ba, saboda nasan kede lafiyarki kalau, Kuma Nima haka,idan kinada wata cuta ma ai saide in nine nasaka miki, tunda nine nabaki jini batare da angwada jinin nawa ba “

Cikin rashin damuwa tace”dansu Daddy sun matsa ne ai, Amma yanda nake jin ka acikin zuciyata ko wacce irin cuta ce dakai, zan iya zama dakai Bae”

Murmushi yayi ba tareda yace mata komai ba, suna qarasa wa asbitin sukayi wa nurse bayani,dayake tasan Huzaifa tun tuni, Nan asbitin suke zuwa duka family d’insu, cikin qanqanin lokaci aka d’auki jininsu aka basu wajan zama

Basuyi awa d’aya ba, doctor yakirasu zuwa office d’insa, zama sukai ya Kalle su yayi murmushi yace “Huzaifa kace ankusa angoncewa”

Murmushi Huzaifa yayi, “Eh wallahi Doctor, ga madam Nan”

Yace “To Allah yasanya alkhairi, Allah yabaku zuri’ah Dayyiba”

Ahankali Waheeda dake wasa da yatsun hannunta tace “Amin”

Takarda ya miqawa Huzaifa yace “toga result d’inka, Congratulations, baka d’aukeda kowacce irin cuta….”😃

Huzaifa ya kar6a yana fadin “to Alhamdulillah”

Kallan ta Doctor yayi yace “Waheeda”

‘Dagowa tayi ta Kalle shi sannan tace “Na’am”

Yayi ajiyar zuciya yace “Waheeda duk abinda kikaga yasamu Bawa, to anaso ya yarda da qaddarar sa, ita cuta ba mutuwa bace, sannan idan kin yarda da shawarwarin dazan baki Zaki zauna lafiya, sannan Zaki rayu kamar kowa idan nad’oraki akan magani,kuma…..”

“dan Allah dakata Doctor Mahmud, mekakeso kace ne?”

Cewar huzaifa daya dakatar da doctor

Doctor ya kalli idon Waheeda da yayi tsilli-tsilli tana Kallan su duka su biyun, sannan yace “Waheeda kiyi hakuri, Amma abunda bincikenmu ya nuna shine kina d’aukeda qwayar cuta me karya garkuwar jiki”

Lokaci d’aya, Waheeda da Huzaifa suka miqe tsaye

Huzaifa yace “What…? HIV fa doctor, tayaya?”

Gaban Waheeda yayanke yafad’i, tasaka hannu tadafe qirjinta, kanta take girgizawa kwata kwata takasa magana, lokaci d’aya jiri yad’ebeta tazube qasa sumanmiya “

Cikin sauri Huzaifa yabita, jijjigata yafara yi, yana fad’in” Waheeda!! Waheeda kitashi Dan Allah!! “

Office d’in aka turo, wata matashiyar budurwa tashigo, taci Gayu iya Gayu, tana ganin Huzaifa tace”Yaya Huzaifa lafiya Kuma? Meyasame ta?”

Huzaifa ya kalleta baice mata komai ba yasaka hannu ya d’auki Waheeda cancak, yafice daga office d’in

Yana fita matashiyar budurwar ta kalli doctor tace”meyake faruwa ne doctor?”

Kai tsaye yace “ta tsorata ne sakamakon gwajin da muka mata, muka Gano tana d’aukeda cutar qanjamau,but ni banga abun suma ba, kowanne Bawa da irin qaddararsa,Kuma ba lalle saika yi iskanci ne zaka sameta ba, akwai hanyo yi dayawa, wasu a wajan mahaifiyar su suke dauka, wasu ta hanyar hada jini Dame irin cutar, kokuma ayima allura da sirinjin Wanda yake d’aukeda cutar, kokuma sex, ko amfani da wani qarfe kamar su kibiya, to gashi ita tun kafin ma nafada mata magungunan daya kamata ta dinga Sha harta sume”

Cikin razani budurwar tace “mene? Wallahi saina fad’awa Hajiya, Kuma akan me qanjamau din yake wannan rawar jikin?Huzaifa d’an’uwana ne, cousin d’inane, bazamu Bari ya auri me wannan cutar ba, ta shafa masa masifa, ita tasan inda tasamu cutar ta”

Tana fad’ar haka, tafice daga office d’in, Doctor yayi murmushi sannan yabud’e wani file yaci gaba da rubuce-rubuce

Motar ya bud’e yasaka ta aciki,har zuwa lokacin Waheeda bata farfad’o ba, Shima yashiga, dube dube yafara anan yaga wayarta cikin hand bag dinta , Kai tsaye contact d’in wayar ya duba, mutum d’aya ne yafad’o masa, dayake wayar Ummah ce yana ganin Ansa Naufal Son,yakira wayar, Babban Yaya yana gida yana motsa jiki, yaga Kiran Ummah, dayake ringing d’inta daban ne, saiya daina abinda yake ya d’auki wayar

Cikin damuwa Huzaifa ya zayyane masa komai, Babban Yaya yadafe Kansa da hannun sa🤦🏻‍♂️yakasa cewa komai,banda innalillah wa inna ilaihirraji’un babu abinda yake maimaita wa a ransa, lokaci d’aya yarasa a’ina yake, a zaune yake ko a tsaye, gabansa banda Dukan uku uku babu abinda yake,Hiv Kuma? Hasbunallah….. yana jin Yanda Huzaifa yake fad’in “hallo hello, baka jinane?”

‘Dif yakashe wayar, cikin tashin Hankali yazura kayansa yanufi Airport, ko wanka bai tsaya yiba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button