BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wayar tamiqawa Hajiya Anty, Anty ta share Hawayen idonta, sannan takar6i wayar tace “sannu Naufal, yajikin naka?”

Ahankali yace”jiki da sauqi Anty, kikulamin da Waheeda nasan Hankalinta yatashi “

Anty batayi magana ba, saita Bawa Waheeda wayar, saboda tasan yana jin nauyin ta bazai iya cewa tabawa waheedan waya ba, Waheeda kuwa tana kar6ar wayar Takoma Gefe, kuka take sosai takasa magana, cikin sanyin murya yace”kiyi shiru…, ba sosai bane ciwon”

Cikin kuka tace “kayi hakuri nadena, daga yanzu nadena hanaka komai, naji tsoro sosai, jinake kamutu”

Wani irin dad’i yaji ya ratsashi, yanzu Kam yagama tabbatar wa Waheeda tana sonsa, saboda haka wannan ciwon Koya warke bazai nuna mata hakan ba, yasamu mafaka ta yanda zai dinga zuba mata shagwa6a son ransa

Ahankali yace “I luv you so much…….muahhhh,, muahhhh” 💋💋

Yasakar mata kiss har biyu ta cikin wayar, sannan yaci gaba da fad’in “kimin addu’ah kinji, insha Allah zanji sauqi, jeki kaiwa su Daddy wayar

Tace”to” sannan tatashi takai musu wayar, Sai a lokacin Hankalinta ya kwanta, Sai ajiyar zuciya take, jikin Hajiya Anty Takoma ta lafe kamar wata mage, bata Jima da kwanciya a jikin nataba bacci yasoma d’aukarta

Yana gama wayar dakowa acikinsu harda junior, sukai sallama Bayan yagama kwantar musu da Hankali, Kiran mashkur ne yashigo wayar tasa, d’auka yayi tareda sallama, mashkur yace “friend mutanan nanfa sun hanamu shigowa Dakin, sunce har yanzu kana buqatar hutu, Sai lalla6a ka suke kamar qwai”😂

Murmushi yayi yace “rabu dasu mashkur, zamu hadu ai idan nafuto insha Allah, ciwon fa Bana kirki bane, kawai tsagewar qashi ne, da niyya na langwa6e musu, nagaji da ball d’in Dama hanyar guduwa wajan amarya ta nake nema, to Kuma Sai haka tafaru…..” 🙊

Mashkur ya kwashe da dariya yace”wato me jiran kukane aka jefeshi da kashin awaki, banga laifin ka ba Abokina,Naga ma sun sanar katafi injury, Kasha Amarci lafiya….”

Babban Yaya yayi murmushi yace “thanks Friend”

Pls kuyi hakuri Dan Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
1/28/22, 20:52 – Ummi Tandama😇: FQ

Juyowa yayi ya kalli Waheeda, rage murya yayi yace “ya zanyi?”

Cikin shagwa6a tace “ba saida tace katafi ba kaqi, yanzu gashinan zakasa naji kunyar ta, wallahi nide babu ruwana”

Daga baqin kofa Hajiya Anty taji shirun yayi yawa tasake nocking tareda fadin “Daughter”

Tashi yayi cikin sauri yabud’e kofar, yayi wuf yafad’a cikin toilet, Hajiya Anty tashigo Dakin fuskarta d’aukeda mamaki, ga Waheeda a kwance,Kuma taga Anja kofar toilet anrufe, to waye aciki?🤔
Zama tayi agefen gadon ta’ajiye mata, yanda qamshin turaren Babban Yaya ya cika Dakin shine ya tabbatar mata da cewa yana Nan betafi ba, cikin ranta tace wannan yaro da jaraba yake kamar ubansa 🙊

ta kalleta tace “tashi kici”

Waheeda tatashi tad’auka tafara ci ahankali,tana tunanin Babban Yaya, gaskiya maza basuda kunya, yanzu Babban Yaya harya iya Kallan Anty, Bayan Antyn tasan abinda yamata, ta tuna yanda yashige toilet da gudu, Sai abun yabata dariya
Tayi murmushi kawai, Hajiya Anty ta zauna a Dakin tana jiran taga ta inda Naufal zai futo, idan ba tsawatar masa tayi ba, yarinyar Nan saita shiga ukunta, shiru shiru har tsawon minti Goma bai futo ba, data gaji da jira saita daga murya tace “jiranka nake kafuto Naufal”

Dariya takama Waheeda, bata iya 6oyewa ba saida ta Dara
Ahankali yabude kofar toilet din yafuto Kansa aqasa yana Sosa qeyarsa,kunnansa takama ta riqe da qarfi, cikin jin zafi yad’ora hannun sa akai yace “Auchh!”

Cikin rashin wasa tace “Naufal, meyasa bakajin magana ne? Nahana ka zuwa wajan yarinyar Nan daga Nan har tsawon kwana Goma”

Cikin azaba yace “to Anty”

Sakinsa tayi, cikin sauri yafice daga d’akin.

tajuya ta kalli Waheeda tace “kekuma harda dariya ko?”

Waheeda ta sunkuyar da kanta qasa, Hajiya Anty Kuma tajuya tafita falo ta zauna, tareda kunna kallo tana gadin Waheeda

Baidawo gidan ba saida daddare, Bayan yagama rufe musu ko’ina na gidansu, falon yashigo zuciyar sa daya, yana d’ago Kansa tareda sallama sukai ido biyu da Ummah, cikin sauri ya sunkuyar da Kansa,yana tunanin meya kawo ta gidan itada bata zuwa? Anya kuwa ba Anty ce ta fada mata komai ba tazo ganin Waheeda? Zuciyar sa ce tabashi cewa Ummah tariga taji komai, lokaci daya ya tsinci Kansa da kunyar ta, ahankali yaqara so ya tsugunna agaban su yagaida Ummah

Mamaki yakama Ummah, tace “yanaga kana sunkuyar dakai yayansu?
Kuma ga jaka ko tafiya zakayi? Baka gajiya da yawo daga dawowarka zaka sake tafiya? Ko kewata bakayi ko? “

Waheeda dake Gefe tayi murmushi, Kansa ya shafa yace”Ummah Ina Nan, Nan gidan muka dawo ne”

Ummah ta Kalle shi, Kallan rashin fahimta, Hajiya Anty tace “kuka dawo Kota dawo?, itace tadawo Nan, Amma Kai ai kasan hanyar gidanku, konan gidanku ne?”

Ummah tace “me yayi ne kike wannan fadan akan gida? Zamu bar miki gidan”

tajuya ta Kalle shi tace “tashi mutafi”

Kansa ya shafa yaqi tashi, Kuma yaqi d’ago Kansa ya kalleta, tunda yake da’ita, Bai taba tunanin akwai ranar da zaiji kunyar Ummah ba, Amma yau gashi shine yake kunyar ummah saboda Waheeda

Hajiya Anty tace “wallahi danaji dadi, yabiki kutafi, dama ban gayyace Shiba, idan yazo nanma takura mata zaiyi da naci”

Ummah tanajin haka tad’auki haske, Sai yanzu ne tasan dalilin kunyar, ashe shiyasa yaqi hada ido da ita, ashe dannata ya girma, murmushi tayi tamiqe tsaye tace “to saiki bashi matarsa tunda bakya son naci”

Hajiya Anty tamiqe tabi Bayan ta zata mata rakiya, yana ganin fitarsu yamatsa kusa da Waheeda ya zauna aqasan kafet din, lips dinsa yad’ora akan Nata ya sakar mata kiss, sannan yakoma ya zauna yad’auki remote kamar bashine yayi ba, zaro ido tayi cikin mamaki, kafin tayi magana Anty tadawo falon, ganin Naufal a zaune aqasa kansa yana kan TV yasa ta share shi itama ta zauna, har qarfe goma suna zaune kowa yana kallo, goma da rabi nayi Uncle yashigo, dariya yayi, ganin Yanda Anty tasasu agaba takafa ta tsare, Sai yanzu ne tasan abinda yafaru kenan zata takurawa yaro, aishi tunda safe daya ga anshigo da’ita a hannu yasan akwai abinda yake faruwa, yasan dannasa ya angonce

Zama yayi Shima, yanadan Jan Naufal din da zance harya sake suke zancen su kamar ba d’a da uba ba

Sai dariya suke kamar ba dare ba, anty tana Gefe tana Kallan su, Waheeda kuwa bacci take akan kujera, Anty jira take taga Naufal yaje ya kwanta sannan tatafi da Waheeda daki, to taga alamun ba tafiya zaiyi ba, danhaka tatashi Waheeda suka tafi dakinta, babban Yaya yana kallonsu qasa qasa jiyake kamar ya kurma ihu, koba komai yakamata ace yaji dumin matarsa kafin taje ta kwanta, saida suka gama zancen su shida uncle sannan yayi masa saida safe yatafi dakinsa ya kwanta, Sai yau yake baqin cikin rashin wayar Waheeda, koda muryarta yaji yasan zaiji dadi, haka ya dinga juyi akan gadon, idan ya runtse Idonsa ma ita yake Gani, Sai tsaki yake saki shi kadai 😖

Anty kuwa tare suka kwanta da Waheeda akan gadon ta, Sai wajan qarfe daya ta shirya tatafi wajan Uncle, yana zaune akan sallaya,addu’ah ya shafa yahau gadon tareda janyo ta jikinsa yace “yakamata kibar Yaron Nan yahuta da matarsa, Sai kallanta yake kin tafi da’ita daki, Ina masa magana Amma hankalin sa yana wajan matarsa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button