BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya yayi, sannan ya bud’e idonsa yatashi yanufi qofa
Ummah tace “Ina zakaje Kuma?”

Cikin damuwa yace “Zanje ayi bincike akan Yaron ne”

Sa’eed dake danne danne awaya yad’aga Kansa yace “Babban Yaya Dan Allah ka rabu da yarinyar Nan, kaje ka huta”

Wani irin kallo yayiwa Sa’eed ba tareda yace komai ba yafice daga falon, Ummah tayi ajiyar zuciya tareda miqewa, tana mamakin irin wannan shaquwa ta Naufal da Waheeda, tasan bazai iya barinta acan ba,haqiqa yana kula da qannansa yanda ya kamata, Albarka tashiga saka masa acikin zuciyarta, tasan cewa tayi sa’ar samun sa acikin a matsayin Babba, koda babu ransu, zai iya riqe qannansa sa.

Yana zuwa compound driver ya d’auke shi suka fita, saboda yagaji

Kai tsaye mtn office suka nufa, yasa aka rufe layin Nata, sannan sukaje police station sukai report,sannan yayiwa d.p.o magana akan abinda yake faruwa,d.p.o ya basu wani ‘Dan sanda suka nufi banki dashi, acan banki ma Kai tsaye yanemi ganin manajan bankin, yayi sa’ah kuwa yana Nan, saide yana shirin fita ne, kasancewar sa sananne Sai kowa yake Kallan sa acikin bankin, suna qarasa wa office din manaja, yafad’a masa abinda yakawo shi, manaja yanemi account din da gayen yake turawa, sukayi bincike akan account din, anan aka Gano asalin sunansa, da sunan iyayensa dakuma sauran bayanai, Babban Yaya yayi masa godia sannan yasa driver yakai shi inda aka Kai Waheeda, suna zuwa aka basu wajan zama, d’aya daga cikin ma’aikatan yace “yalla6ai yarinyar Nan fa tunda mukazo take kuka, daqyar da lallashi muka samu tabamu amsar abinda mukeso”

Babban Yaya yace “Baku daketa bane, inda taji duka zata muku bayani ai”

Murmushi yayi yace “ai hakan ma mungode sosai wallahi, ta fad’a mana itama damfarar ta yayi, yanzu zaku iya tafiya,mukuma zamuci gaba da bincike, idan wani abun yataso, insha Allah zamuyi Maka waya”

Babban Yaya yabashi wata takarda yace “ga wannan, abinda na bincika ne Nima, nasan insha Allah Shima zai taimaka muku”

Cikin farinciki yad’ago kansa yana Kallan Babban Yaya Bayan yagama ganin bayanan dasuke jikin takardar yace “taimako kuwa, sosai da sosai, godia muke yalla6ai”

Kawai d’aga masa kai yayi batare da yace komai ba, Dan muguwar gajiya yakeji, bacci kawai yake buqata,gashi magrib har tayi

Wata matace dake Sanye da uniform din kaki, tazo tareda Waheeda, ta rissina ta gaida Babban Yaya Sannan tajuya, Babban Yaya bai kalli inda Waheeda take ba yayi wucewar sa gaba, driver ya Mara masa baya 🤣

Gashi de shine Babban yayansu, Amma muddin tafiya ta had’ashi da’ita shine yake bude mata mota, tarasa dalili, Amma baya barinta tabude mota da kanta, yau kuwa yana zuwa yashiga baya ya zauna, yasa hannu yarufe motar, Waheeda ta tsaya tayi shiru tana ganin ikon Allah, wato in taga Dama ta6ude kofar ta da kanta kenan, yau ba mutunci, batayi gigin bude gefen dayake ba, tayi sauri ta zagaya daya gefen tabude tashiga, tana shiga wani Sanyi da qamshin turaren sa ya bugeta, tasa hannu tarufe motar, driver yaja suka tafi
Lumshe idonsa yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya, lokaci d’aya wata irin nutsuwa take shigarsa wadda baisan dalilin taba, Waheeda ta Kalle shi da jajayen idanuwanta, cikin sanyin murya wadda take nuna tayi laushi, ta zubar da makaman yaqinta tace “Sorry Babban Yaya….”

Yana jinta yayi shiru, hannunta dake rawa saboda tsoro ta ‘Dora akan tsintsiyar hannun sa wadda take cike da gashi, cikin fishi yasa hannu yabige hannun ta yajuya mata baya yana Kallan window, lokaci d’aya ta rushe da wani irin Kuka
Driver ya d’aga murya yace “kiyi hakuri Waheeda, ba gashi kin futo ba, gaki ga yayanku, ai kuka yaqare”😃

Waheeda tayi shiru tana goge hawaye, Amma kamar ruwa tana gogewa wanine yake sake sakkowa, har cikin ransa kukan ta yana ta6a ransa, Amma dole ne ya nuna mata kuskuren ta

Suna zuwa gida ma kafin a dedeta parking yafice daga motar yayi ciki,itama tafuto tana goge idonta tabi bayansa jiki a sanyaye, gaba d’ayansu family din na Arabo suna falon, daga kan iyayen har ‘ya’yan, yana shiga qannansa suka fara yimasa sannu da zuwa daga mazan har matan, fuskar sa a d’aure yake amsa musu, yanemi waje ya zauna yana gaida su Hajiya Anty da Uncle Usman, saikuma Daddynsa, Waheeda tana shigo wa ‘yanbiyu da Anty Maryam sukayi kanta suka rungume ta, cikin farin ciki suke fadin “Thank you Babban Yaya”

Saida suka saketa, sannan ta kalli kowa na falon, bata nufi kowa ba Sai hajiya Anty, tana zuwa ta fad’a jikinta tasaki wani irin kuka, Hajiya Anty ta rungume ta aqirjinta, tanajin soyaiyar yarinyar har cikin ranta, kasa bata hakuri tayi, Sai Bayan ta datake bubbugawa, Ummah ta Kalle shi tace “sannunku, ai jinake acan zata kwana”😅

Daddy yace “Nima abinda naso kenan, tunda bata jin magana”

Uncle Usman yayi murmushi baice komai ba, Ummah tajuya ta kalli Waheeda datake kuka a jikin Hajiya Anty tace “kitashi kije kisaka muku abinci keda yayanku”

Har zuwa lokacin fuskar sa a daure take, cikin sauri yace “A a Ummah tabarshi kawai”

Waheeda tanajin irin amsar daya bayar tasake riqe hajiya Anty tana fashewa da sabon kuka, Hajiya Anty tayi qasa da muryarta tace “sorry Baby na menene Kuma na kukan? Ba gashi kin dawo ba?”

Cikin kuka tace “To ai Babban Yayan yaqi ya huce”

Anty tayi murmushi tace “rabu dashi, anjima kije d’akinsa kibashi hakuri”

‘Daga mata Kai tayi, sannan tatashi daga jikinta ta wuce d’akinsu domin watsa ruwa.

Sai a lokacin ‘Yan falon suke fara’ah, kana Gani kasan akwai had’in Kai dakuma jituwa a tsakanin su, anan sukaci gaba da zama Bayan mazan sun iyo sallah sun dawo,’yanbiyu ne suka had’a abinci, suka kawo falon aka baje anacin abinci, uncle Usman ya kalli Sa’ad yace “Kai jeka kiramin yayanku a d’akinsa”

Sa’ad yaje yakira shi, yana Sanye da jallabiya fara qal, daga Gani kasan Sai mutum Ma’abocin tsafta ne zai saka ta, tsugunna wa yayi agaban iyayen nasa, uncle Usman yace “munyi waya da Yaya Habu, yanata tambayar ku, to tun kafin yafara korafi, yakamata ka shiryawa qannanka tafiya,suje suyi masa kwana biyu”

Wani irin farinciki ne yakama Babban Yaya, yaji dadi da Uncle Usman yace ya shirya wa qannansa tafiya,hakan yana nufin banda shi kenan, dama damuwar Waheeda duk ta isheshi, Gara su tattara sutafi subar masa gidan dagashi da ummah 😇

Kafin yabada amsa
Daddy yace “Usman yakake cireshi daga ciki? Yashirya su tafi gaba d’aya kawai, Sai suyi sati d’aya,su huta saisu dawo”

Uncle Usman yace “ba aiki yake ba Yaya? Yaje qauye ya zauna har sati d’aya?”

Daddy yace “wanne irin aiki? Ai yayi retired, d’azu dayazo yace bazai sake komawa ba, saboda idan yakoma ma matsalar Waheeda zata dawo dashi, to idan ya zauna anan ma babu abinda zaiyi, Gara suje qauyen”

Uncle Usman yayi Daria yace “a a, suyi kwana biyar de, idan sukaga dangi saisu dawo”

Yana jin yanda suke tattaunawa yaji ransa ya6aci, baya son zuwa wajan baba Habu, saboda idan yaje ya dinga masa maganar aure kenan, shikuma ba auren yake soba, lallausar sumar Kansa ya shafa yace “zamuyi kwana biyu uncle, ya’isa, saboda aiki na” 😂

Daddy yace “zaka koma aikin kenan”

Babban Yaya duk ransa babu dadi a taqaice yace “eh”

Ya tashi zai nufi d’akinsa, Ummah tace “bazakaci abincin ba? Kowa yana zaune shine zaka koma d’aki ka zauna kamar sabuwar amarya?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button