BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tayi tace “ai qwazon nasa awaje yake, yanzu kwanaki dasukayi da Yara ai kasawa yayi”

Ummah tayi shiru tana tunani, itade bata tanka ba, domin kuwa a cike Takeda Waheeda, Daddy ne ya dauki wayarsa yakira Babban Yaya, tana shiga yace “idan kun gama 6oye 6oyen naku kakawota gida, muna son ganinta, sannan kaima ka tabbatar kataho lefenka yana Nan angama hadawa yakamata kazo kagani, idan kagani komai yayi yanda kakeso Sai akai musu, su tsaida mana ranar auren”

Jikinsa ne yayi Sanyi, cikin ladabi yace “to shikkenan Daddy” daga Nan yakashe wayar ya kalleta yace “kishirya gobe Zaki wuce gida”

Kallan sa tayi tace “Babban Yaya kaifa?”

Shiru yayi yana tunani, shide bayajin zai iya zuwa haka kawai saboda ganin kayan lefen Ummi, to waye ma yace su hada masa wani lefe? Kansa yadafe da hannun sa yace “nikam bazani ba”

Yanda taga yabata amsa ransa duk adagule kawai Saitayi shiru karta sake magana yahuce akan ta

Haka suka wuni ranar babu walwala atare dashi, tana so tace masa yakaita yawo Amma bataga fuska ba, haka tayi shiru tana gudun aikata laifi yahuce akanta, washe gari da safe tare suka tafi club dinsu da’ita,tana Sanye cikin doguwar Riga Abaya, saita yafa mayafin abaryar akanta, idan ka ganta bazaka taba cewa tanajin hausa ba, saita zama kamar wata balarabiya, hannun sa cikin Nata suka futo daga motar da aka kawo su, yana futowa mutane suka yanyameshi yanmata turawa Sai rungumeshi suke, wasu Kuma suna shaking din hannu, yanda yake murmushi dimple dinsa na futowa Sai hakan yabawa Waheeda haushi, suna zaune gida daya kullum yana daure musu fuska Amma Jiba yanda yake sakarwa yanmata jikinsa da fuskarsa, saida yagama photuna dasu sannan sukayi ciki, Waheeda de nemanta ma yayi yarasa, tun tuni wasu daga cikin masoyansa suka janyeta, dressing room dinsu yayi, Bayan Dan wani lokaci suka futo aka fara buga ball, tun tanajin haushinsa tana Kallan yanda yake buga ball din harta dawo ta daina ganin yanda dubban mutane suke murna idan Dan’uwan Nata yajefa qwalla araga

Saida suka gama sannan yayi abinda zaiyi ya dauketa suka wuce airport, a Airport dinma Gani tayi yayi shiru kamar akwai abinda yake damunsa, kasa hakura tayi tace “Babban Yaya meyafaru?”

“banason tafiyar kine”

Baisan lokacin da wannan maganar tafuto daga bakinsa ba kamar Wanda aka qwatota, Kallan sa tayi cikeda farinciki tace “Allah?”

Wayancewa yayi yace “ke wasa nake miki, banason shirme, kawai…. Kawai de… Banji dadin yanda Daddy yamin maganar lefe bane”
Ya qarasa maganar a rarrabe fuskar sa cikeda fishi

“nikuma Babban Yaya banga abun fishi anan ba, zaka iya auren wadda kakeso daga baya”

Cikin 6acin rai yace “Kina tunanin zan hada abinda nakeso dawani abu daban? Kinga banason damuwa, muje kunfara shiga jirgi”

Kanta ta gyada masa batare datace komai ba suka tafi, saida yaga jirginsu yatashi sannan yakoma gida

Jirginsu yana sauka taga driver yana jiranta, mamaki ya kamashi ya kalleta dakyau yace “Waheeda yanaga kin sake kyau? Me yayan naku yake baki?” 🤔

Harararsa tayi tace “shafa kaji, ka bude min mota kawai, Kuma gidan Hajiya Anty zaka kaini”

Jinjina Kansa yayi, yasan rashin kunyar Waheeda, zatayi yafi haka, jakar hannunta ya kar6a sannan yace “lalle Waheeda idan kikai shekara a qasar waje bazamu ganeki ba, cikin abunda baifi ‘Yan kwanaki ba kikai irin wannan kyau haka?”🤔

Tana jinsa tasaki wani Dan qaramin tsaki, damuwar ta daya yanzu shine Ummah, bata Isa taje wajan Ummah ba, Gara ta gudu gidan Hajiya Anty yafi sauqi

Suna hanya ta turawa Babban Yaya text cewa ta sauka, Saukarsu gidan Hajiya Anty keda wuya taci Karo da wasu akwatuna masu shegen kyau guda ashirin da hudu, dozin daya pink colour, dozin daya blue, akwatunan ne suka dauki hankalin ta, tafara ta6a jikinsu tana qwalawa hajiya Anty kira, futowa tayi daga d’akin ta tayi mutuqar kyau cikin atamfa dinkin Riga da siket, kullum cikin Gayu take bata gajiya

Tana ganin Waheeda tace “Oyoyo daughter” tafadi hakan tareda bude hannayenta, babu musu Waheeda tashige jikinta, Hajiya Anty ta rungume ta tanajin qaunar yarinyar acikin zuciyar ta

Zama sukai akan kujera Waheeda tasake Kallan kayan tace “Anty lefen Babban Yaya ne wannan?”

“lefensa ne, Uncle dinku ne yayi order su daga Dubai, abubuwa kad’an muka qara anan, Amma ba’a saka mata pant da brezia ba, zan Mai magana saiya tambayeta size dinta”

Waheeda tayi ajiyar zuciya “Anty Babban Yaya fa baya son auren Nan, kukuma Naga kun dage”

“zaiso ne Idan akayi, ai kinsan qiyaiya tana komawa soyaiya”

“to Anty, Allah yarufa asiri”

Anty tace “Amin ya Allah, kibude kigani mana”

“a a Anty, basai nagani ba, Allah ya basu Zaman lafiya”

Hajiya Anty tayi murmushi, takasa gane yanayin yarinyar, shin kishi take, kokuma kawai 6acin raine Dan taga yayan Nata ma baya son auren? 🤔

A gidan Hajiya Anty tayi Zaman ta har kusan sati daya da dawowar ta, koda wasa bata nufi gidan Ummah ba, sauqin ta daya, suna cikin hutu

Ranar da tayi kwana Tara, ranar su yanbiyu suka dawo daga Saudia, murnar dawowar yan’uwan Nata ne yasa tatafi gidansu, Hajiya Anty tarakata suka tafi tare, lafiya kalau suka gaisa da kowa, anan falon aka baje Ana hira, Ihsan ta kalli Waheeda tace “shikkenan Waheeda kin luser bakije Saudi ba” tafadi hakan cikin sigar tsokana

Waheeda ta yatsina fuska tace “ai zuwa makkah Kiran Allah ne, dama can banda ni yakira, Nan da lokaci kadan kunaji Kuna Gani zamu tafi nid Babban Yaya” tana fadar haka tatashi ta wuce dakinsu

Sa’ad da Sa’eed suka bita da kallo, Sa’eed yace “Sa’ad kasaka yarinyar Nan acikin addu’ah kuwa da mukaje Saudia?”🤔

Kafin Sa’ad yabawa dan’uwan nasa amsa, Ummah tatashi taciro wayar charger tabawa Sa’eed tace “jeka zanemin yarinyar can”

Babu musu kuwa Sa’eed yanufi Dakin nasu, adede lokacin Waheeda tacire Kaya zata shiga wanka, daga ita Sai towel, lokaci daya taji saukar duka ajikinta, ihu tasaki, su Ihsan suka qaraso Dakin suna temakon ta, memakon ya qyaleta, saiya had’a dasu yakama duka, aikuwa babu shiri suka futo kowacce tana Sosa jiki

(duk Wanda ya karanta min littafi be biya ba shida Allah)

Saida yayi mata lilis sannan Yabarta, yana futowa daga d’akin Daddy yashigo, ya zauna a kujera, cikin ladabi hajiya Anty ta gaishe shi sannan tayi musu sallama tatafi, Kallan Ihsan yayi yace “jeki kiramin qanwarku”

Dakinsu tashiga, Waheeda tana kwance aqasan Dakin tana kuka, duk jikinta yayi ja inda wayar tata6a ta,idanunta har sun kumbura gashi sunyi jajir dasu, fada mata saqon Daddy tayi, cikin kuka Waheeda tace “Dan Allah Ihsan d’agani, wallahi bazan iya tashi ba”

Ihsan ta kamata tatashi zaune har towel din yana kokarin cirewa, hijabi tabata tasaka, sannan suka futo falon, zama tayi aqasa tana sheshshekar kuka ahankali, Ummah ta kalleta tace “marar mutunci Ina wayata take?”

Cikin kuka tace “Dan Allah Ummah kiyi hakuri, wayar tana daki, Dan Allah karku fadawa Babban Yaya”

Daddy yace “Waheeda zancen Babban Yaya aiya qare, kifada wa shi wannan Yaron dayake zuwa wajanki yafuto ayi muku aure inda gaske yake, idan Kuma bakya sonsa to akwai huzaifa Yaron Abokina zaizo Shima ki ganshi idan yamiki shikkenan, bazaki gama karatu kamar yan’uwan kiba, aure zan miki “

Waheeda najin haka ta rushe da Kuka tafara Bawa Daddy hakuri, Amma mursisi haka Daddy yatashi yayi daki Yabarta anan, intisar ce ta kamata suka koma daki harda Ihsan ma, suna zuwa Dakin suka fara bata haquri, Amma Inaaa Waheeda Sai kuka take har kanta yazo yafara ciwo, daga qarshe, wani irin zazza6i me zafi yarufe ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button