BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hajiya Anty tayi murmushi tace “tana d’aki kishiga mana”

Maya ta sunkuyar da kanta qasa tace “A a Anty, ai wajanku nazo gaba d’ayanku”

Babban Yaya yajuya ya kalleta, shide yarinyar tana birge shi, saboda tanada Hankali sosai ga nutsuwa, shiyasa ma ya aminta da qawancen su itada Waheeda, yasan Waheeda zata koyi abubuwa dayawa a wajan yarinyar

Ihsan tace “to Bari nakira miki qawar Taki”

Tana zuwa d’akinsu taga Waheeda a kwance da waya a hannun ta, tace “kizo Maya tazo”

Cikin sauri Waheeda ta miqe, dama tana so taga Maya, tana so ta fad’a mata abinda yake damunta ko zata bata wata shawarar

Cikin sauri kuwa ta iyo gaba Ihsan ta take mata baya, suna zuwa falon ta ganshi a zaune tareda su Sa’eed, gabanta ne yafad’i, cikin sauri tayi qasa da kanta, Shima yana ganin futowarta gaba d’aya saiya Rasa nutsuwar sa, yama manta yana zaune ne da iyayensa da Kuma qannansa a falon, yazuba mata ido yakasa d’auke Idonsa akanta, Hajiya Anty datake gyara Zaman inner wears acikin akwati ta Kalle shi tayi murmushi, dama de tana tunanin da niyya Naufal yasiyo wannan Brezia d’in manya daidai Waheeda, kamar yasan da’ita za’ayi auren.

Sa’ad da Sa’eed suka kalli Babban Yaya suka had’a ido suna Daria qasa-qasa, Sa’ad yayi qasa da murya yanda Babban Yaya bazai ji ba ya cewa Sa’eed “sainaga kamar Dama yana ciki…” 😂

Sa’eed yace “nima tunanin danake kenan, Sai yanzu nake ganin alamun hakan”

‘Dagowa sukai daga gulmar suka fuske kamar basu ba😎

Har Waheeda ta zauna kusa da Maya Babban Yaya bai daina kallon ta ba, ahankali yad’auke Kansa daga gareta, yana juyowa suka had’a ido da Uncle Usman daya zuba masa ido tun d’azu yake Kallan sa 😂
cikin kunya yafara shafa lallausar sumar Kansa tareda sunkuyar da Kansa qasa

Waheeda ta kalli Maya tace “Sai yau kika ga damar zuwa qawa”

Maya ta kalli Waheeda tace “qawa Ina tsoron zuwa wajanki ne, nasan namiki laifi, bansan tayaya zan miki bayani ba…”

Cikin rashin damuwa Waheeda tace “menene yafaru?”

Maya ta kalli kowa na falon tahad’e hannunta biyu waje d’aya🙏🏻
cikin rawar murya tace “Daddy, Uncle, Ummah, Anty, Babban Yaya, Qawata, Dan girman Allah ku yafemin, haqiqa nasan na aikata muku laifi, nasaka ku cikin wani Hali, Amma ba komai ne yasa nayi hakan ba Sai saboda taimakon da Babban Yaya yata6a yimin lokacin da muka shiga cikin wani hali nida iyayena, yatemaka mana a lokacin da muke buqatar temakon,…. “

Jin wannan furucin Nata yasa hankalin kowa ya dawo kanta, Sai kowa yazuba mata ido yanaso yaji abinda zatace, Daddy yace”menene yafaru Maryam, fad’amana muji”

Kanta ta sunkuyar tace “Gaskiya Waheeda bata d’aukeda kowacce irin cuta, lafiyarta kalau, tun muna ss2 nafahimci cewa Babban Yaya yana sonta, tundaga lokacin naci d’amarar temaka masa akan Waheeda, Ina bata shawara sosai akansa duk Dan naja ra’ayin ta, to Amma Naga hakan bata samu ba, saboda koda yaushe abinda take fad’a min d’ayane shid’in yayanta ne, Ina tunanin mafita saina ji har ankawo mata kayan lefe, narasa yanda zanyi in rabata da Huzaifa, kawai rannan Sai take fad’amin zasuje Asbiti ayi musu text, da wannan damar nayi amfani nasamu family Doctor d’inku wato Doctor Khamis, na fad’a masa komai, anan Shima yabani goyon baya, ya tambaye ni Dame nakeso ya temaka min, Kai tsaye nafad’a masa tunda shi Babban likita ne nasan yanada alaqa da wasu hospital d’in dayawa, inaso duk asbitin da Waheeda taje a fad’a mata cewa tana d’aukeda cutar qanjamau, ta wannan hanyar ne kawai zan gane wannan Huzaifan datake rawar Kai akansa shin yana mata soyaiyar Gaskiya ne kokuma ta qarya? Idan soyaiyar gaskiya yake mata to zanji dad’i nasan koda qawata ta aure shi zaici gaba da sonta, idan Kuma duk qarya ce, to lokaci zai nuna, Doctor khamis yabani goyon baya sosai, Kuma Alhamdulillah yanzu gashi gaskiya tayi halint…… “

Kafin Maya ta qarasa magana Sai ganin Waheeda sukai tatashi tsaye tashaqe mata wuya😂🙊🙆🏻‍♀�

Sosai suka kama dambe, Maya tana kokarin qwatar kanta Waheeda kuwa idonta yarufe takama Maya Sai dukanta take
Su Ummah ne suka tashi da Anty da Kuma yanbiyu suka fara rabiya, Amma Waheeda tayi wa Maya wani irin ruqo kamar ba qawa da qawa ba 😂😂

Cikin kuka Waheeda tace “daga yau babu ni babu ke, karki qara zuwa inda nake, dama can kema nasan bakya sona, tun tuni nagane take takenki…”

Wani irin murmushi Babban Yaya yayi,haqiqa dole ya kyautatawa Maya, tayi masa abinda bazai ta6a mantawa ba,dama ta dalilin tane Waheeda bataje Saudia ba saboda Ummah taji suna waya, yanzu kuwa yayi alqawarin had’ata da qawar Tata sutafi Saudia tare, saisuci gaba da damben acan 😂

Ummah ta kalleta tace “bazaki saketa ba?”

Cikin kuka Waheeda tace “to Ummah meyasa zatasa a aura min Wanda banaso? Ita uwata ce?”

Uncle Usman ya kalli Babban Yaya yace “Kai tashi kaja matarka kubar gidannan”

Ummah ma tace “eh wallahi, ni nagaji da fitinarki Waheeda, memakon ki godewa Allah bakida cutar komai, saide ki kama dambe? Wuce kibishi kutafi gidanku mun yafe zamanku a gidannan, Allah yabada Zaman lafiya”

Ahankali yatashi yanufeta, har zuwa lokacin hannunta yana jikin hijabin Maya Wanda taqi saki, yana zuwa yasaka hannu yacire mata Nata hannun, sannan yajata zasu bar falon, ihun kuka Waheeda tasa tana fad’in ” Ummah dan Allah kuyi hakuri, ni wallahi Bana sonsa, daku zan zauna, Ummah!, Anty!!”

Ummah ta d’aga murya tace “Nayafe Waheeda, kuje can ku qarata”

Haka suka futo daga falon har zuwa wajan motar sa, yana zuwa yabud’e mata tashiga, sannan yarufe Shima yashiga, fita sukai daga gidan suka d’auki hanyar gidansa, tunda tashiga motar takifa kanta acinyar ta tana gunjin kuka, yanajinta bai hanata ba, sunyi Nisa da tafiya yayi tunanin zatayi shiru Amma yaji shiru yarinya Sai kuka take masa, mamaki ya kamashi, Wai shine yau Waheeda take gudu. 😖

jikinsa ne yayi Sanyi, ahankali yafaka motar agefen titi yakifa Kansa akan sitiyarin motar, Waheeda tana kuka taji sun tsaya, batareda ta d’ago kanta taga dalilin tsaiwar tasu ba taci gaba da Kuka, Ahankali takejin wata shashshekar kukan tana tashi acikin motar, cikin mamaki ta d’ago kanta tazuba masa jajayen idonta, mamaki yasake kamata ganin Babban Yaya yana kuka da Idonsa, abinda bata ta6a ganiba a tarihin rayuwarta, lokaci d’aya ta nemi Nata kukan tarasa, cikin zuciyarta tace “Kuka?”

💃💃💃
1/28/22, 20:51 – Ummi Tandama😇: WN

Rikicewa tayi tarasa Yaya zatayi? Babban Yaya da Kuka? Tome aka masa dazai kama yimata kuka? Ita yanzu Yaya yakeso tayi ne? Bata ta6a ganinsa yana kuka ba, Sai hakan yasake d’aga mata hankalin ta tasake fashewa da Kuka,cikin kuka ta kalleshi takasa bashi haquri, cikin taqaici ya d’ago Kansa, Idonsa duk hawaye yace “bazaki min shiru ba saina bige bakinki anan?…”

Itama cikin kuka tace “toba kaine kaqi yin shiru ba…”

Hannunsa duka biyun yasaka yarufe fuskarsa, saida yagama kukansa ma’ishi, sannan yaja motar suka qarasa gidan

Maigadi yazo ya gaishe su cikin ladabi, ganin yanayin uban gidan nasa ba daidai ba yasa yajuya yakoma mazauninsa

Suna shiga falon ya nuna mata d’aki yace “gashinan”

‘Dakin tashiga Wanda yaji kayan komai na more rayuwa, fad’awa tayi kan gadon ta Fashe da Kuka, wanne irin aure ne wannan? Babu masu rakiya babu komai ko kayan sakawa Ummah bata bataba, tayaya zata rayu dashi awannan gidan a matsayin ma’aurata? Kuka take sosai saida taji kanta yafara ciwo sannan tayi shiru

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button