BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallan ta yayi yace “Ummah naje tace bata sona”

Gaba dayansu Yan falon suka Juyo suna Kallan sa, wacce yarinya ce zatace bata son yayansu?

Ummah tace “kamarya?”

Juyowa yayi yasake Kallan Ummah yace “Ummah ki tambayeta kiji, naje nace mata Ina sonta, kifada mata nine naje da adedeta saboda motata tasamu matsala a hanya, Kuma tace koda na aureta bazata iya kula dakeba Ummah,sannan tare naganta dawani Gaye suna zance, kinga kenan itama tanada Wanda takeso,to menene amfanin auren ta? Ummah duk wadda bazata iya kulawa da mahaifiyata ba, bazan iya auren taba “

(Kai Babban Yaya irin wannan batu haka 🤣😂)

Ummah tadauki wayarta takira wayar maman Nadiya, Bayan sun gaisa maman Nadiya tace
” Hajiya Baqon namu Kuma baizo ba, muna ta jira angama shirya masa abin motsa baki Amma Nadiya tacemin baizo ba Kuma bai kira wayarta ba”

Ummah tace” Yanzu nake tambayar sa yacemin yazo tace masa bata sonsa, Wai tace bazata iya kula daniba koda ya aure ta”

Maman Nadiya yace “Anya hajiya itace kuwa? Amma Bari inkirata”

Ummah tanaji maman Nadiya ta daga murya takira Nadiya, nadiya tana zuwa maman ta tace “Big Brother yazo kince masa bakya sonsa, kince kokin aure shi bazaki kula da umman saba, anyi haka ko ba’ayi ba?”

Nadiya tanajin wannan bayani tatuna mutumin dayazo wajan ta dazu a adedeta, ta d’ora hannunta aka 🙆🏻‍♀️tafashe da Kuka tace “wallahi mama bansan shibane, yaudara ta yayi, Allah Ina sonsa” cikin kuka tanufi dakinta da gudu

Maman Nadiya ta sassauta murya tacewa Ummah “Hajiya komai fa ya lalace, zamuyi magana daga baya” daga Nan ta kashe wayar

Babban Yaya ya kalli Ummah yace “Ummah kinji da kunnanki ai naje ko?”

Cikin bacin rai Ummah tafara girgiza kafarta tace “naji Naufal, ai banyi tunanin yarinyar zatace bazata kula daniba, bansan haka tarbiyar ta takeba”

Wani farin ciki ne ya mamaye shi, yaga Ummah ta yarda da komai, to tun kafin waccan Nadiyar tazo ta musu bayanin komai ta fada musu 6oye kamarsa yayi, Gara yagudu yabar qasar😂

Cikin ladabi yace “Ummah, muna shirye-shiryen fara World cup very soon, zan fara training Jibi, Insha Allah gobe da Asubar fari zan wuce” 😂😂

Ummah tace “Allah yakaimu Son”

Firar da ba’a qarasa dashi ba kenan, ya wuce dakinsa ransa fess👌🏻

Sonake agano min iyayen wadannan taurarin guda biyu NAUFAL DA WAHEEDA

To Babban Yaya yatsira wannan lokacin, kome Waheeda zata aikata ya dawo dashi qasar?

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:49 – Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

11&12

Suna tashi da safe sukahau shirin school,awajan break fast Waheeda taga babu Babban Yaya, anan taji cewa yatafi tun asuba kamar yanda yafada jiya da daddare

Bataci wani abincin kirki ba, Sai tea me kauri, ta kalli ‘yanbiyu taga Sai lokacin zasu fara cin abincin, tatashi tayi d’akinsu da gudu

Kowa yabita da kallo Amma babu Wanda ya tanka mata, wayarta tad’auko ta kunna ta sannan takira Babban Yaya, a lokacin suna cikin jirgi har anfara sanarwa a kashe waya jirgi zai tashi, yayi mamakin ganin number ta tana kira, already yanada number tun jiya yayi saving d’inta a wayarsa
Dauka yayi tareda cewa “Lafiya ko laifin kika sake yi?”

Dariya tayi tace “Babban Yaya,Aina Dena laifi yanzu, nayi Hankali Nima”

Yace “Allah yasa, kinga de wannan Karon munrabu lafiya dake, banaso wani abu yasake faruwa kisa in dawo qasar Nan kwana kusa, kinga yanda nasamu narabu da rigimar su Ummah akan yarinyar Nan Nadiya, to banaso kisake aikata wani abun dazaisa nadawo Nigeria ta dalilin ki “

Bakinta ta turo gaba kamar yana Kallan ta, sannan cikin shagwa6a tace” Babban Yaya to ai wannan dinma ba nice da laifi ba, Basaida na nuna ma abinda akamin ba?”

Runtse idonsa yayi, Waheeda zata kashe shi, yadade da mantawa Amma saida tasa ya hango cikakkun breast dinta a’idon zuciyar sa, cikin sauri yace”naji,naji, menene Kuma saikin tuna min?” 😂

Tace “to Babban Yaya kayi hakuri, yaushe zaka dawo?”

Kai tsaye yace “Babu rana, kuma nafada miki banaso kema kiyi sanadin zuwana Nigeria”

“Angama Babban Yaya, Allah yakiyaye hanya” daga haka ta kashe wayar Tata, Takoma falo,Ummah ta kalleta tace “lafiya?”

Tace “Da Babban Yaya nayi waya”

Sa’eed yace “um kaji masu waya”

Dariya tayi kawai, ta jira yanbiyu suka gama sannan suka fita compound driver ya daukesu suka tafi

Bayan uncle ya fita daga ajin nasu,Maya ta kalli Waheeda tace “Waheeda waiya kuke da Babban Yaya ne?”

Kallan Maya tayi tace “Kamarya ya muke? Mekike nufi?”

Maya tace “Ina nufin Wai Ummah ce ta haifeku dukanku?”

Kai tsaye tace “itace mana, me kikaga?”

“babu abinda nagani Waheeda, kawai de Naga kinshaqu dashi fiyeda yanbiyu, sannan Shima yana sonki sosai, shine nace koba Ummah ce ta haifeku ba”

Waheeda tayi mata wani banzan kallo tace “toba Ummah ce ta haifemu ba waye yakawo mu duniya Kenan? Nasan nashaqu dashi yanda bakya zato, saboda tun Ina qarama nasaba dashi, sannan dakika ce yanaso na wannan Kam Ina tantama, saboda idan yana sona ma, to wannan soyaiyar dayakemin bata hanashi yamin hukunci, idan nayi laifi zaneni yakeyi wallahi, kinbani mamaki Maya, ashe zarginmu kike “

Maya tace” innalillahi…. Waheeda zargi Kuma? Meyasa zan zargeku Bayan yayanki ne uwa d’aya uba d’aya? Kawai de kun birgeni ne jiya danaga yanda yake baki kulawa, harfa mota yabude miki, shine nayi tunani idan ku masoya ne abun zaifi dadin Gani, yana miki soyaiya kina maida masa martani “

Cikin masifa Waheeda tace” A’uzubillahi…. Maya kamar wata marar Hankali Zaki dinga dangantani da yayana?”

Maya ta kamo hannunta tace” yi hakuri qawata, nabata miki rai, kiyi hakuri Dan Allah “

Waheeda tayi banza ta qyaleta, har wani uncle din yashigo ajin yafita, bata sake kula Maya ba, Sai tsaki take saki ita kad’ai

Bayan sun koma tana duba wayar ta taga missed call dayawa da wata number, cikin mamaki tace “to waye wannan ya kirani har 5 missed call da number daya?”

Kiran number tayi, cikin zazzaqar muryarta tace “Naga kirane waye?”

Cikin salon yaudara akace “kira Kuma? Da wannan number?, Kai may be mistek ne”

Ba tace komai ba ta kashe wayarta

Bayan kusan minti biyar wannan number tasake kiranta, harta d’aura towel tana shirin shiga wanka, tadawo ta d’auki wayar, “Amincin Allah ya tabbata agareki sarauniyar kyawawa”

“Amin, Lafiya?”
abinda tace masa kenan

Yace “bekamata mace kamar ki, tayimin wannan tambayar ba kyakykyawa, ai kinsan ta tsuniyar gizo bata wuce ta qoqi, wallahi tunda kika amsa wayata dazu, naji hankalina ya kwanta dake, nasan aduk inda kike, ke mace ce Mai nutsuwa, me tarin Hankali da cikar haiba, uwa uba tare da kyau “

Kalamansa sun ratsa Waheeda, da atsaye take, Amma yanda taji yana zubo Nata kalamai, saita nemi bakin gado ta zauna

Yanbiyu suka shigo Dakin kowacce tana ajiye Jakarta, Ihsan tayi toilet da gudu saboda fitsarin daya matseta, inti Kuma ta kwanta agadon

Waheeda tajuya idanuwanta tace “nagode, naji dadin yabonka agareni, kafadamin meyafaru?”

Intisar tadago daga kwanciyar da tayi, ta kalli Waheeda, taji tawani sauya murya tana waya da alama da wanine

Daga nasa bangaren yace “zan so kibani Dama indinga jin wannan zazzaqar muryar Taki koda sau daya ne a rana”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button