CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Yah Ameen na hango zaune cikin wata luntsume miyar kujera ya k’ara wani haske da kyau na musamman sai shek’i ya ke idan ka kallesa baza kace wani abu na damunsa ba amma cike yake da damuwar son yaje gida,Naanahrsa na yawan fad’o masa sai yaji gabansa ya fad’i sosai,lumshe kyawawan idanuwansa yayi tare da shafa kyakkyawar sumar dake kansa,6are ledar chocolute yayi ya wurga bakinsa ya fara tsotsa,ya d’au remote yana cenza tasha,gabansa ne yaji ya buga da k’arfi lumtse idanuwansa yasakeyi tare da jawo wayarsa lambar Naanah ya nemo ya danna kira,amma abinda yaji baturiyar cikin wayar na sanar dashi wayar ya kashe take yasa shi k’walalo manyan idanunsa akan wayar,sake gwadawa yayi nan ma akaashen take,siririn tsaki yaja tare da cillar da wayar,ya zame kad’an ya mayar da hankalinsa ga TV,amma sai yaji ya kasa fahimtar komai,sake d’auko wayar yayi yasake jaraba kira bata shigaba,gashi k’irjinsa ya kasa dena bugawa,”Naanah”ya kira sunanta ciki Sweet voice d’inshi,ya duba wristwatch d’insa karfe tara ne na dare acen k’asar,da Daddy yaso ya kira ya fad’a masa gobe zai dawo amma ganin dare yayi sai ya fasa,yaci gaba da kallonsa da bai fahimtar komai sai tunanin Naanah da yacika masa zuciyarsa,
*******
Umma ce zaune a kan ruwan cikin Naanah tana bugu da kai naushi,cewa take “yau sai cikin nan ya zube na gaji wallahi bazan yarda ki haifar mana shege a gidaba kisa talauci ya mana sallama don duk gidan da aka haifi shege talauci ke musu katutu ga ruwan sama da ba’a musu,
Anty Rahma tace”nusheta da kyau Umma shegiyar ko kunya bataji ba wai itace hardayo cikin shege a fuska musa a zuciya fir’auna,nishi nake sama-sama donko kuka nakasa numfashina da k’yar yake fita,saboda shak’ar da Umma ta min kakarin mutuwa kawai nake,ganin yanayin da nake ciki baisa Umma ta tausayamin ba…..
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Sorry Fan’s jiya baku jini ba,karku damu ana tare,kuci gaba da biyoni,wasu cikinku suna tacewa suna son jin CIKIN WAYE?saurin me kuke kubini a sannu k’ila da kanku ma zaku gano,amma dai muje zuwa,akwai sauran tafiya ,ina jin dad’in comments dinku musamman masuyimin sharhi,inayi daku sosai,❤
Bismillahir rahmanir rahim
3⃣1⃣-3⃣2⃣
????Ganin halin da nake baisa ta tausayin ba,saima k’ara nusar cikin da take,cewa take “Wllh ni na gaji da wahala tsintacciyar mage ai bata mage,
Jin abinda Umma ta fad’a yasa na d’ago fuskata a waharce kukanma ya kasa zuwa sai na zuciya,d’agani tayi tanaci gaba da masifarta,na tattare guri guda kamar kayan wanki na cusa kaina tsakankanin cunyoyina,ji nake kamar girjina zai fito waje saboda bugun da yake,”tsintacciyar mage bata mage,na sake na nata kalaman Umma”to me take nufi?,na tambayi kaina amsar da nakasa ganowa,
Jan k’afata nayi zuwa d’aki ina tafe iska na d’aukata saboda tsabar ramar da nayi daman abu ga bamai jikiba,ga wani irin jiri da ke kwasata saboda rashin isasshen abinci,ina zuwa na zube a d’aki ina haki numfashina na sauka da k’arfi,
Wayata na jawo na kunna,kamar ana jira sak’onni suka dunga shugowa,na mutum uku ne Yah Ameen,Yah Marwan,sai Zainab,nata na fara bud’ewa ga abinda tace,
“Naanah lafiya kwana2 baki ba dalilinki please sister don Allah kizo naganki,duk kin sani a damuwa karki manta shak’uwarmu tum muna yara Allah ne ya had’a soyayyarmu wallhi jinki nake tamkar ciki d’aya muka fito,gashi nazo harso ba adadi Umma na korana ke kuma kin kashe waya idan wani abu na miki kiyi hakuri sis.
Ina gama karantawa hawaye ya fara zubarmin “Allah sarki Zainab babu abinda kikayimin rayuwace ta cenzamin bansan yadda zaki d’auki k’addarar da ta fad’omin ba,Nima kina raina ‘yar uwata,
Na Yah Ameen na bud’e,shi kuwa cewa yayi”Naanah meke faruwa kika kashe wayarki,ina fatan kina lafiya,I miss u ina kewar ganinki sosai ki gaishemin su Umma Abba da Rahma,
Share guntun hawayen da ya zubomin nayi tare da jan ajiyar zuciya”yanzu idan yah Ameen ya dawo yazanyi ni nasan kasheni kawai zaiyi yaji wannan labarin to CIKIN WAYE?zance masa idan ya tambayeni,nan na rushe da wani irin kuka ina bugun cikin wayyoni na shiga uku ya zanyi da rayuwata ko waye yamin cikin nan bazan ta6a yafe masaba,
Jawo wayar na sakeyi na dubo na Marwan shi kuwa cewa yayi”My luv me yasa me nayimiki kinsan halin da nashiga na rashin ganinki kuwa zuciyata tana cikin k’una rayuwata tana cikin jin d’aci ina cikin rashin lafiyar ganinki kuma kece kad’ai maganin wannan ciwon domin kallonki ganinki jinki sune zasu warkar dani,
“Wayyo Marwan d’ina nima kana raina saidai nasan idan kaji abinda nike d’auke da shi nasan rabuwa zakayi dani,na fashe da kuka ina nushin cikina fad’i nake”ciki don Allah ka fita meyasa ka zauna a jikina bayan kasan bai kamata kazo a irin wannan lokacinba,me yasa kayimin haka,me yasa kayi saurin zuwa baka bari saida nayi aure ba,a lokacin da ba wanda zai tambayeni NA WAYE?balle a takura rayuwata a lokacin da kowa zaiso ganinka me yasa kazo a lokacin da aka tsani jinka ko ganinka,(NI KUWA UMMU AFFAN NACE NAANAH TAKI K’ADDARARCE TAZO DA HAKA DOMIN TUN RAN GINI TUN RAN ZANE HAKA ALLAH YA TSARA MIKI),
Ina cikin wannan halin naji sallama a tsakar gida kamar muryar Hajiyarsu Zainab,da sauri na tashi ina layi kamar wata ‘yar maye,na nufi tsakar gidan,abinda naji Umma na fad’a yasani dakatawa “munafukai azzalumai me kikazo yi mana a gida bayan kinsa d’anki ya gama lalatama yarinya rayuwa sannan zaki wani lalla6o wai kina nemanta to k’aryarku tasha k’arya kuna ganin ku ga masu kud’i kun isa kuyi komai a gari ba wanda zaice muku donme to kuje ku da Allah,
Hajiya naji tana cewa cikin 6acin rai”Karime kiji tsoron Allah ‘ya’yayammu kiwone a wajenmu wallahi sai Allah ya tambayemu duk abinda muka aikata garesu,ke wacce irin uwa ce Karimatu ni wallahi tuni na gama gano bake kika haifi Naanah ba,amma ko bake kika haifeta ai d’a na kowa ne don kaima idan katemaki d’an wani kaima wani zai tai maki naka don bakasan inda zasu fad’a wataranba,
Cike da hargagi da sababin masifa Umma tace”eh d’in ba ‘yar tawa bace ke saikizo ki d’auka kitemake tan kuma wallahi bakinki yasari d’anyan kashi kice yaranki zasu fad’a uk’uba wataran ba yarana ba,kuma ki barmin gida kafin inmiki babban wulak’anci magulmaciya kawai,
Hajiya ta kalli Umma cike da takaici kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya harta kai”k’ofa ta juyo,tace”wallahi na barki ne saboda nice nazo gidanki,Naanah kuwa da sannu Allah zai ku6utar da ita daga hannun muguwa irinki jahila kawai,
Kururuwa Umma ta saka tana zage-zage don taji zafin jahila da Hajiyar ta kirata,ita kuwa tuni Hajiyar ta fita ta barta tana zage-zagenta,juyowar da zatayi ta ganni tsugunne ina kuka,wani hauri da takaimin saida na kifa nan take goshina ya fashe,tace”munafuka ba ke kika jawomin abinda akazo har gidan mijina akamin ba,wallahi yau sai kinbar gidan nan bazan iyaba na gaji,
Daidai shugowar Abba yace”bazata bar gidan nan ba saidai ke kibarsa Karimatu,harara ta buga masa tace”ai idan kaga nabar gidan nan to saidai idan wani gidan ka sake ko kuma gawata,yace”to itama haka Naanah aure ne kawai zai rabata da gidan nan,ya jawoni yana min sannu,hannuna yarik’e muka shiga ciki,