CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

miqewa yayi ya kalli Rahma yc”ina Sakina,kame kame ta fara don har yanxu Sakinar bata dawo gida ba,girgixa kai yayi tare da fad’in Allah yashiryaku,ya wuce,
da sand’a Sakina tashugo gdn don tadade da dawowa ganin Abba a falon yasa bata shugoba,sai da taji ya shiga ciki,umma tc”meye na wani sand’a,tc”uhmm umma Abba mana kinsan halin tsohon nan yanxu ya cikama mutane kunne da wani wa’axinsa,
Guri tasamu ta xauna umma tc”me akasamo mana yau Allah yasa akwai kud’i masu auki kinsan xankai kud’in adashi danake tarawa idan bikinku yaxo(A’uxubillah uwace waike fad’in hakan Allah kashiryamu kashirya mana xuriya),
Sakina ta turo baki gaba “wllh ke umman nan kin cika son banxa ni dashan wuya keda kwace kud’i kinsanma menayi nasamesu,umma tc”don kaxakaxanki bansonji idan ban barki kin fitanba xaki samesu sai in had’aki da tsohon naku ince gaki kin dawo daman yanxu ya gama tambayarki,sakina tc”ke umman nan kin cika kwafsi daga wasa nifa wasa nake miki,nan ta bud’e xaka ta kwaso kud’i taba umma nan haqora suka washe tc”da kyau ‘yar albarka kinga da bikinki xaki kwashi kaya,banda su Naanah da ba abinda aka iya sai xaman gida da xuwa makaranta hali sak irin na tsoho gaba d’aya sukasa dariya harda tafawa,
girgixa kai nayi daga ckn d’aki nayi juyi a kan ya mutsattsiyar katifata hawaye na tsiya.
ummu affan
please share
and comments
???? CIKIN WAYE? ????
❤❤❤❤
❤❤
❤
story
and
written
by
*Fateemah Sunusi Rabee’u
ummu affan
????3⃣-4⃣
Bismillahir rahmanir rahim
????Hawaye na tsiyaya,sai yaushe umma zata gane gaskiya ta kula da tarbiyyar yaranta Allah kashiryasu na fad’a tare da goge hawayena nayi addu’ar barci,nan kuwa barcin ya kwasheni,
Washe gari da wuri na tashi kamar kullum alwala na d’auro na gabatar da sllar,salatul fujur na fara sannan nayi sallar asubah,na dad’e ina addu’o’i sannan na shafa,
Kasancewar ranar asabarce babu boko,sai na koma na kwanta baikai ga yin barcinba naji ana kwalamin kira,tashi nayi ina tafiya cikin sanyina duqawa nayi saitin umma wacce itace tayi kirana,
Nace”umma gani,cikin masifa tace'”wllh duk munafurcinki saidai ki tsaya iyakar uban naku da yayanku amma ni bazakimin shiba,Aunty Sakina tace”shegiya wata simimi kasau da ita saikace mutiniyar arziki,
Nidai bance musu komaiba sai hawaye dake bin fuskataAunty Rahma tace”duk kukanki na banza ne yau ko bazakije wannan makarantarba aiki zakiyi,umma ta amshe maganar dacewa”Abu dole ai ko bakiso saikinyi tunda bazakije ki wani kwantaba sai aini kici,
Bance musu komai ba na nufi kitchin d’in ni kaina inason yin aikin girki don nak’ara k’warewa saidai Abba ne ya hana tasani ganinsa ga manyan ‘yan mata nan gabanta bata sakasu saini,
Sauri-sauri nayi aikin don k’arfe takwas da rabi muke zuwa Islamiyya kuma malaminmu yayi gargad’i akan duk wanda baizo ba bulala goma don hadda ya bada,kuma zai iya don malam sani bashi da mutumci,ni kuwa a duniya idan akwai abinda natsana to bulalace,
Kusan takwas saura na gaba girkin na jera komai a k’aramin dinning table d’inmu snn nazo na gyara kitchin d’in na wuce d’akina,toilet na fad’a wanka nayi sannan nazo na shirya cikin uniform d’ina purple colour nasaka safa na d’auki lik’af d’ina a hannu farlour na dawo harsun gama breakfast d’insu gurin kacha-kacha,
Tsintsiya na d’auko na tattara gurin sannan na karya,na d’au na wankewa na kwanke sannan na fito na d’aura nik’af d’ina,har lokacin Abba bai fito ba daman idan yadawo masallaci yana dad’ewa kan ya fito,d’akinsa nashiga yana zaune kan prayer mat yana lazumi ganina yasa yayi addu’a,duk’awa nayi kusa dashi na gaishesa ya amsa cikin sakin fuska da nuna kulawa,
Yace”Naanah har anshirya kenan,nace”eh Abba zan wuce sai nadawo,shafa kaina yayi yace”Allah yayi miki Albarka ya kareki aduk inda kika shiga,cikin farin ciki na amsa da “Ameen Abbana,gaba d’aya mukayi dariya sannan namasa sallama na wuce,
Kasancewar makarantar tamu ba wani nisa gareta ba anan k’asan layinmu ne da k’afata na k’arasa,ina zuwa kuwa malamin da zai amshi haddar na gani cikin ajinmu,nashiga cikin ajin da sallama,
Ya kalleni sama da k’asa sannan yace”Naanah Firdausi Isma’il zonan,dawowa nayi na tsugunna daga k’asansa nace”gani malam,yace”inaga agwogwon gidanku bai tafiya daidai ko?,k’asa nayi da kaina cike da rud’ani nikaina nasan na makara domin tara daidai nafito gida,
Ahankali nace”don Allah malam kayi hakuri wani aiki nayi,yace”wanda yasaki aikin baisan lokacin makarantane ba,yana fad’ar hakan yana zaro bulalarsa,cikin sauri na mik’e a razane nayi cikin ajin,kallona yayi yana zaremin ido sannan yace”ke Naanah na lura duk cikin ajin nan kinfi kowa rainani ko,nace”don Allah donsonka da Annabi muhammad S A W kayi hakuri bazan sake makara ba,
Ajiye bulalar yayi yana kallona sosai yace”shi kenan na rabu dake amma idan baki iya haddar dana baku jiya ba kinsan sauran,nace”na yarda,sannan na tsugunna na fara yi mishi karatuna cikin natsuwa daba ko wanne harafi hakkinsa,bayan nagama akayi kabbara,sannan naje na zauna inda nasaba zama kusa da k’awata Zainab Ibrahim….
Ummu Affan
Please Share
and comment
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story
and
Written
By
Fateemah Sunusi Rabee’u
Ummu Affan
????5⃣-6⃣
Bismillahir rahmanir rahim
*Na sadaukar da wannan page ga Hussaini 80k Nagode kwarai da gaske Allah yabar zuminci Ameen*
????Zainab ta kalli Naanah tayi mgn cen kasa,”gaskiya Naanah kin ya bawa aya zaki da yau kinsha bulala,murmushi kawai tayi don Malam Sani sam bashi da kyirki yana kyale Naanah ne saboda tana da kokari duk ajinsu ita ce ta farko sannan Zainab,shiyasa kosun makara wataran ba a bugunsu don makarantar na alfahari da su,
Zainab Ibrahim nan kusa da gidan su Naanah take tun suna yara suka taso tare,makarantar boko da islamiyya duk daya suke kuma aji guda,
mahaifin Zainab yana da kudi sosai babban dan kasuwa ne,yara uku suka haifa shida matarsa Hajiya Rabi wacce suke kira Hajiya Marwan shine babban dan su wanda yake qasar waje karatun likita sai Rashida sannan Zainab,
Iyayensu suna matukar ji dasu sun taso cikin gata da kulawa ga Ingantacciyar tarbiyya,Hajiya da farko bata son kawancen Zainab da Naanah saboda atunaninta halinsu daya da sauran ‘yan gidansu sai daga baya da taga ne halin Naanah ya banbanta da nasu takejin sonta har cikin ranta take kaunar kawancen nasu tana matukar tausayawa halin da Naanahr take ciki,
An tasosu suna kan hanyar dawowarsu gida Zainab tace”wai yau Naanah me yasaki makara kuma kinsan sarai malam Sani zai amshi haddarsa yau,
Nace”kedai bari Zainab kinsan halin Umma ita ce tasani aiki bayan nayi sauri ma da bazan samu zuwa ba,tace”Allah ya kyauta,na amsa da ameen,
Daidai nan tazo kofar gate dinsu tace”ni zan wuce gida sai gobe mun hadu a skul,nace”shi kenan sai goben,
Wata dan kareriyar moto na gani kofar gidanmu,ba ka ganin wanda ke ciki a tunani na samarin su Aunty Sakina ne don haka na shige ciki,saidai ina shiga na jiyo hira sama-sama da sauri na shiga ciki,
“Yayah Ameen,na fada cikin murna da fara’a,shima fuska sake ya kalleni tare da sakarmin tsadajjen murmushinsa,da sauri na karasa na fada jikinsa ina murnar ganinsa,”oyoyo Yayanmu,shima cikin muryarsa mai sanyi yace”oyoyo autarmu, daga makaranta ake,Nace”eh yayah Ameen saukar yaushe,yace”ban dade da zuwa ba,
Ganin ba’a kawo mishi komai ba sai na wuce dakina na cire uniform na wuce kitchin ruwa da abinci na d’oro akan tire na aje gabansa,na zauna kusa dashi,