CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Anyi Mother’s day,Wato ranar iyaye mata anyi hidima sosai a ranar sannan akazo akayi diner farty wanda shi na angwaye da amarene sai abokai da k’awaye,uhmm abin baya fad’o,ko da yake na hango ‘yan CIKIN WAYE Fans,sunsha ankonsu gefe guda suma sunzo taya Ameen da Naanah murna,haka na hango WUSAID DA UWANI HANAN,Wato UWANIN QAUYE,DA Fans d’insu sunzo taya Ameen da Naanah murna,????????????
Anyi abu agurin na girma da wayewa anci ansha taro ya watse lafiya(Naanah nawa CIKIN WAYE?FANS ban gajiya fatan kowa ya koma lafiya????????)
Washe gari aka d’aura auran Fareeda da Alh Babale,da yamma aka gabatar da k’ayatacciyar walima da aka gaiyato babbar malamar addini,Malama Rabee’atu Safyan Kd,ta gabatar da wa’azi akan ma’aurata,tayi wa’azi sosai da nasiha inda jikin kowa yayi sanyi a gurin,
Wajen k’arfe bakwai na dare aka kai amare gidajensu,
Bayan nasihar da iyayensu Maza sukai musu sosai da kuka aka fitar dasu musamman Naanah da ta k’amk’ame Didiy tana kuka sosai shiya shigar da ita mota sannan aka d’aga da ita tana kuka da waiwaye,
Ahaka har gidan tana kuka,k’anwar Mamee Anty Raliya tace”shiga da bisimillah da k’afar dama,hakan tayi tana kuka,
Kan gadonta aka ajeta,mutane sai yaba tsarin gidan suke,wajen takwas darabi kowa ya watse,daman ba k’awaye garetaba,Zainab ce ita ma kuma tare aka fita dasu tayi d’akin nata mijin
Bayan ta tabbatar kowa ya gama fita mik’ewa tayi tare da cire mayafinta ta kalli ko ina na d’akin sakkowa tayi taje falo ta kalli komai tasami guri kan kujera ta zauna,
Afili tace”ka shugo lafiya ina jiranka zakaga tsiya kuwa,uhmmm wallahi Ameen zaka gane kuranka tunda na shugo gidan nan
Jin alamar shugowar mutum ta gyara zama tare da d’aura k’afa d’aya bisa d’aya tana kallon k’ofar idanuwanta tasssss……
Tofah ku buyoni donjin k’arshen littafin insha Allahu a page na gaba nakesa ran kammala muku wannan littafin
Idan naga ruwan comments zan muku da yamma,idan kuma ban sami lokaciba ko kuma na raina comments d’inku sai tomorrow,
Amma ina son inji sharhin me kuka fahimta acikin littafin nan,wanne irin darasi kuka d’auka,wanne abune mara kyau da za’ayi watsi dashi sai najiku,ina godiya da had’in kan da kuke bani musamman fans d’ina na FACEBOOK,ina godiya????
Sai mun had’en,08104335144 whatsAPP me
Fateenku ce????
Ummu Affan✍️✍️✍️
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
STORY AND WRITING BY FATEEMAH SUNUSI RABEE’U
(UMMU AFFAN).
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Bismillahir rahmanir rahim
????️9️⃣1️⃣-1️⃣0️⃣0️⃣
Da sallama ya shugo hannayensa rik’e da manyan ledoji,ciki-ciki ta amsa don shikansa baiki mai tace ba,ta amsanne ma saboda ladar da takeson samu,
Ganinta zaune tana karkad’a k’afa alamar masifa takeji yasa yad’an saki k’ayataccen murmushinsa,
K’arasowa yayi yace”Sarauniya da girman kujerarki,harara ta banka masa,tare da kauda kai gefe,
Zaunawa yayi kusa da ita da sauri ta mik’e cikin fusata tace”meye hakan,yace”Allah ya baki hakuri kinsan kin zama hukuma saida rarrashi,
Tsaki taja mtuwww ta wuce,ya bita da kallo,Alwala tayi tazo ta gabatar da sallar asha’i da batayi ba tayi shafa’i da wuturi,
Tana addu’a ya shugo,bakin bed ya zauna yana kallonta harta gama,tare suka shafa yace”Allah ya amsa mana,banza ta masa,
Bayan ta nunke daddumar ta ajiye tare da cire hijabin,tace”malam don Allah katashi ka fita zan kwanta,yace”ba komai amma nasan bakici komai ba ga abinci nan kici,ko kallon inda ya nuna mata bataiba,mik’ewa yayi yace”pls Naanahta don Allah kici,murmushin mugunta tayi tace”to angaya maka bazanci bane ai idan nak’i cima ni zan cucikaina,cike da mamaki ya kalleta”ina Naanah ta koyo bak’ar magana haka jinjina kai kawai yayi ya fice,wani murmushin muguntar tayi,aranta tace zaka sani,
Ta d’auko pulet ta bud’e ledar bank’ararriyar kaza ce sai k’amshi da k’yilli take,ta zauna taci ta k’oshi ta kora da freesh milk dake cikin ledar(Wayaga su Naanah an zak’e anci kazar amarci ko kunya babu,uhmm wayaga su UMMU INTEESAR agari,Marubuciyar ‘YAR GANTALI,ko kuwa kema Maman Khaleel haka kikayi lokacin naki marubuciyar KISHIYAR ZAMANI ????????????Ana tare ‘yan uwa loll)
Tunda tayi sallar asuba bata tashiba sai wajen goma na safe,toilet ts fad’a ta tsantsara wankanta bayan ta fito kan diresin merror ta zauna ta tsantsara kwalliya kai kace gasar kyawu zataje,
Wasu fitattun kaya danaga Naanah ta ciro saida na zaro ido????Siket da riga ne na kanti,siket d’in saboda kankantarsa har mazaunanta ana hange gashi ya kamata sosai rigar kuwa ko cibi bata rufe mata ba ta d’aure gashin kanta daman akwance yake tasa ribon,ko kallabi bata d’auraba ta saka cingam abakinta ji kake k’as-k’as tayo falo bayan ta zura wani dogon takalmi mai shegen tsini,tana tako d’aid’ai,
Alokacin Ameen na farlour tun dawowarsa masallaci bayan yayi wanka yanawo farlour yana kallon labarai,tunda tafito ya zuba mata ido cike da mamaki yayinda k’irjinsa ke bugawa da k’arfi,ta maza yayi bayan ya daure ya daddage ya kauda fuska yana murmushi,
Gabansa ta tsaya ba gaisuwa tace”kayi mana girki ko don yunwa nakeji,kuma bansjin zan ta6a girki agidan nan,murmushi yasake yace”My sweetheat ko gaisuwa babu to fatan kin tashi lafiya,ya mitsa fuska tayi “daban tashiba zaka ganni,
Yace”to Allah ya baki hakuri ga abinci cen an aiko daga gidan Momy,dinning table ta nufa tana kwarkwasa ta juya mazaunai,binta yayi da kallo,tana zama ta d’ago kai da sauri ya kauda mursa,murmushin mugunta tayi,
Yau satin guda da tarewar su Naanah kullum da sabon salon da take kawowa nasaka kaya iri iri masu matuk’ar tada sha’awa,Ameen bai ta6a cewa komaiba bama daki guda suke kwanaba duk da ba k’aramin gasasa takeba kai harma da suya haka yake daurewa bai ta6a nuna mata yana buk’atar taba,
6angaransu Marwan masha Allah sun fahimci juna ysyin da suke zuba soyayyarsu,sosai yanzun suke son junansu,hakama su Zainab sai fatan alkhairi,itama Anty Fareeda suna zama lafiya da abokiyar zamanta kowa na girmama kowa,
Yau shuru ba akawo abinci daga gidan Momy ba,
Naanah ta fito daga bedroom cikin shigar wasu riga da wando wad’anda suka kamata sosai,tasha kwalliya,
“Yah Ameen nifa yunwa nakeji,ta fad’a cikin tsantsar shagwa6a,idanuwa ya zuba mata cike da sha’awa,hura masa ido tayi,tare da turo baki gaba”magana fa nake maka ka zubamin ido ko baka ta6a ganina bane,
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace”Momy tace tunda munyi sati biyu tadena kawo mana abinci,
Tace”sai katashi kamana ni yunwa nakeji,zaro ido yayi yace”haba Naanah kiyi hakuri ki mana kinsan ni ba iya girki nayiba,turo baki ta yi”aiko kama koya daga yau,
Ganin baida niyyar tashi tasa kukan shaga6a”wayyo cikina yunwa nakeji,zai kasheni ya hanani abinci,da sauri ya mik’e “Allah ya baki hakuri bari na siyo miki a hotal,kuka tasake saki”ni wallahi banso da kanka zakayimin,
Huci ya furzar kai Naanah rigima yace”shekenan bari na miki,rigar jikinsa ta shadda ya cire yabar singilet da wandon,ganin yadda kwantaccen gashin k’irjinsa yafito akan faffad’an k’irjinsa yasa Naanah kauda kai tana harare harare,girgiza kai yayi ya nufi kitchin,tabi bayansa da kallo bafa kushe yah Ameen ya had’u ajin farko ne,