CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Fama yake tayi,yarasa me zai had’a dame dominshi idan ba ruwan tea ba ba’abinda ya’iya,ya share gumin dake ta feso masa,ruwa ya xuba a tukunya bayan ya kunna gas,sannan ya zuba markad’an kayan miya masu uban yawa da yamarkad’a yazuba uban kishiri da maggi,sai curry,bayan ya gama wannan ya d’auko taliya yasa sannan ya zuba mai????????????daga jin wannan girki zai had’u fa,(Maman khaleel bisimillah),
Daman ruwa kad’an ya zuba nan da nan ya tsotse sai kawai ya sauke,ko dahuwa bataifa,murmushi yay yauwa Alhamdulillah ashe daman na iya girki,ya sami pulet ya juye sannan ya d’auko chokula biyu ya fito,
Tana nan inda yabarta,ai kallo d’aya ta masa ta saki dariya ganin yadda duk ya had’a gumi ga mai a goshinsa wajen share zufa ya goga,amma 6oye dariyarta tayi,a gabanta ya ajiye,kallo d’aya zakawa abincin ka gane na musammanne????,
Gyara zama tayi tasa chokali,ai loma d’aya ta furzar da gudu tayi toilet tana kakarin amai da sauri ya bita yana mata sannu,bayan ta gama ta galla masa harara,”haka ake girki,sai kuma tasaka kuka rungumeta yayi yana lallashi”sorry my dear bari na sayo miki,turesa tayi ta nufi d’aki,
Haka rayuwa taci gaba har sukai wata biyu Naanah na gasawa Ameen aya a hannu bata kulasa bata girki kullum shine sayo abinci ga shigar da take ta firgita ‘yan maza????,
Zainab ce takawo mata ziyara,Sayyeed ya kawota,bayan sun gaisa ya wuce office da yake yafara aiki,shima yah Ameen lokacin baya gida,
Zainab tace “amarya kinsha k’amshi ya amarcin,murmushi nayi”amarci yana gurinku ku amare,harara ta bankamin”ke banson rainin wayau badai haryanzu kina gasa bawan Allah nan ba,
Dariya Naanah ta tuntsure anan take sanar da Zainab duk abinda ke faruwa ta d’aura da cewa”nayi masa hakanne don in gane da gaske k’aunata yake ko sha’awata alhamdulillah yaci jarabawa ni kaina nayi mamakin abinda na aikata masa,
Gaba d’aya sukasala dariya Zainab tace”lallai hakan da kikayi daidai ne,yanzun sai abasa gara ya kwasa,”ke zainab banson iskanci fa,tasa dariya to k’arya nayi don Allah ki tausaya masa haka wallahi ya bani tausayi,sukasa dariya haka sukai ta hirarsu da yamma tare suka shiga kitchin suka shirya abinci mai rai da lafiya abinda Naanah bata ta6ayi ba a gidan girki sai yau,sosai suka gyara gidan ko ina yad’au k’amshi,
Wajen biyar yah Sayyeed yazo yatafi da Zainab bayan fitarsu,toilet na fad’a nayi wanka,saida nayi sallar isha’i sannan na shirya kaina cikin wasu had’addun kayan barci,sosai suka amshe ni,
Tundaga harabar gidan Yah Ameen kejin tashin k’amshi cike da mamaki ya shiga ciki,ai lumshe idanuwansa yayi saboda dad’in kamshin da yashak’a a cikin farlour,
Da sallama ya shugo,Naanah dake zaune a farlour ta taso da sauri ta amshi jakar dake hannunsa “Sannu da dawowa Yayanah,ido ya zuba mata cike da mamaki hanyar bedroom dinsa ta nufa,ganin bai taho ba ta juyo,murmushi ta sakar masa ganin ita kawai yake kallo”kazo muje mana,
Haka yabi bayanta cike da mamaki,guri ta samu ta’ajiye masa jakar office,sannan ta duka,ta kwance igiyoyi ta kalminsa ta zare masa,harzuwa lokacin kallonta yake cike da mamaki,
Mik’ewa tayi,”na had’a maka ruwan wanka,kagama shiryawa kafito abinci yana jiranka,ta wuce,binta yayi da kallo kafin ya mik’e yacire kayan jikinsa,ya fad’a bathroom
Bayan ya gama shirinsa ya fito don saida yayi sallah sannan ya shugo gida,tana ganinsa ta mik’e suka nufi dinning tare,
Ta zuba masa lafiyayyar farar shinkafa da dasu kabeji da biyar zallar naman kaji,ta tsiyaya masa sanyayyen kunun ayan da ta dama,tun kafin yakai baki yake faman had’iye yau sbd k’amshin da ya bid’esa,
Sosai yaci abincin don rabonsa da yaci abinci irin haka tunda Momy ta dena aiko musu da abinci donshi ya tsani abincin saya k’amk’ami garesa,
Bayan sun kammala falo suka dawo,suna kallo,ganin ta fara hamma ta mik’e,”Yayanah sai da safe,ta d’aga masa hannu,binta yayi da kallo tare da had’iye yawu????,
Tashi yayi yabi bayanta,kan bed ta fad’a,zata gara kwanciya ta gansa,gabanta ya buga da k’arfi,tace”yah Ameen lfy,
Zaunawa yayi bakin gadon ya ruk’o hannayenta duka biyun yace”please My dear,duk wannan wasan kwaikwayon damuke ya isa haka,kinga yanzun mun ruga munzama d’aya don Allah Naanah kiyi hkr ki mance da komai,
Numfashi taja cike da tsoro ganin yadda yake murza mata ‘yan yatsu,tace”shikenan komai ya wuce,da sauri ya rungumeta yace”yauwa Tawan nagode,
Haka suka kwana cikin farin ciki washe gari sai nan2 yake da ita,wajen k’arfe tara ya shugo da leda da ya sayo musu kaza da freesh milk,sukaci cikin farin ciki,
Yace”Babyna kiyo alwala kizo muyi sallah don godewa Allah dayasa muka kasance ma’aurata,gabanta ne ya buga da k’arfi tace”to,asanyaye ta tashi ta dauro alwala,
Nan sukayi sallah bayan sun idar,ya kama goshinta ya mata addu’ar da manzon Allah ya koyar,daga nan saifa zancen ya sauya salo,
Wani irin hut kissing yake aika mata,tun anayi ak’asa har aka koma saman bed,tunifa hankalinsa ya gushe,Naanah kuwa ganin abin bana k’are bane ta fara hawaye,
Kai nima da naga abin yafi k’arfina farlour na koma,gefin asuba na koma jin Ameen na sauke numfashi Naanah kuwa kuka take,tasowa yayi ya rungumeta,
Albarka kawai yake samata,Fad’i yake Naanah ketadanbance wallahi badanni na aikata miki abinda ya faruba wllh da sai ince sharri aka miki,’anya kuwa ke kika haifi Muhseen,
Turesa tayi cikin shagwa6a tace”ban sani ba,
Chak ya d’auketa yayi bathroom da ita dakansa ya mata wanka shima yayi sannan suka fito,
Ai tundaga wannan rana Ameen da Naanah suka d’unke soyayya mai tsafta suke gabatarwa,
Al’amura dayawa sunci gaba da faruwa,
Kammala karatun su Naanah da k’arin girma da Ameen ya samu gurin aiki,
Abindai sai sam barka,Zainab ta haifi yaronta,me sunan Daddy ana kiransa Hanif,itama Salma ta haifi me Sunan Hajiya ana kiranta Khairat,
Rahma kuwa sai abinda Allah yayicdomin abin nata yayi yawa,watarana tayo shaye shayenta,tahau babban titi bata saniba wata mota tazo tayi ciki da ita tabin takan k’afafuwanta,me motar ya gudu,aka kwasheta sai asibiti yanzun dai haka tana gida ba inda take zuwa,kuma ba k’afafuwa,
Zuwa yanzu Yaran Naanah uku harda Muhseen hudu,bayan Muhseen tagwaye tayi duk mata shekararsu uku ta musu kani,me sunan Abba,sunace masa Abiey,
Ameen ne ya shugo gida,ya dawo daga office,da gudu yaran sukayo kansa”oyoyo Abbanmu,d’aya bayan d’aya ya dunga d’agasu,sannan ya rungume Abiey,
Naanah ta turo baki gama cikin shagwa6a tace”ni kad’aice ba ad’aga ba wllh bazan yarda ba,da saurin ya saukar da Abiey yace”sorry princess,zuwa yayi ya rungumeta ya had’a da yaran ya rungume yace”Alhamdulillahi Allah ya rayamin zuriyata,duka suka amsa da amin,
Nima anan nake cewa ALHAMDULILLAHI
Allah na godemaka da kabani ikon sauke wannan littafin me suna CIKIN WAYE?Alkhairan dake cikinsa Allah yasa damu dasu akasin kuma Allah ya karamu dashi,
Ina godiya da goyan bayan da kuka bani tundaga farko har zuwa k’arshen littafin,
Godiya ga Anty Hauwa shugabar kungiyar arewa Allah ya arbarkaci zuri’arki,
Jinjina ga Hussaini 80k,nagode Allah yabarzuminci ya baka mata tagari,muzo musha biki loll????????
Fatan alkhairi ga duk wata member ta kungiyar arewa writers
Masoyana kuma na gode muku sosai ana together????????ina sonku fiye da tunaninku sai mun had’e a sabon Novel d’ina????????