CIKIN WAYE?COMPLETE NOVEL

Fateenku ce????
Ummu Affan
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Bismillahir rahmanir rahim
????2⃣5⃣-2⃣6⃣
????Nan take kuwa barci ya kwasheta,
Ansaka bikin Sakina wata hud’u masu zuwa,Alh Babale matarsa daya da yara hudu shi zata aura yana sonta da tana masa wani gani-gani burinta ta sami saurayi amma ganin cikin samarin duk wanda tawa magana daga ranar bata sake ganinsa dole ta hakura,ba laifi yana da arziki don d’an kasuwa ne,
Yanzun mun shiga SS3 aji na k’arshen secondry zuwa lokacin Naanah ta wani ciko sosai ta zama cikakkiyar budurwa samari sosai suke kawo mata hari amma bata kulasu don tana son cika burin Yayanta,
Marwan kawai ta ke kulawa wanda ya gama fushinsa da kansa ya sauko ganin ita Naanah ko ajikinta shi kuwa yana mata son da bazai iya rabuwa da ita ba,sosai suke soyayyarsu amma a 6oye don bata son Yah Ameen ya sake ganinta da shi so take idan tagama saita fitar da Marwan a matsayin mijin da zata aura tuni suka yi alk’awarin hakan,
*** *** *** ***
Allah ya kawo mu bikin Anty Sakina wanda yazo daidai rana d’aya da na Anty Rashida yayar Zainab,sosai suka sha biki har taro yatashi lafiya,inda aka kai Anty Sakina Badarawa,gida d’aya suke da kishiyarta saida kowa da part d’insa,ita kuwa Anty Rashida kinkinau aka kaita sai addu’ar Allah ya ba ma’aurata zama lafiya Ameen,
Kwance ta ke a d’akinta tun wajen goma na safe ta ke barci sai wajen uku na yamma ta farka,wannan wanne irin barci ne ita kanta abin ya bata mamaki don bata ta6a irin wannan barcin ba,
Abinda kawai zata iya tunawa yau wajen k’arfe tara na safe Anty Rahma ta bata wani Fresh milk tasha tun daga lokacin bata sake sanin inda kanta ya ke ba,yink’urawa tayi da niyyar tashi amma sai taji ta kasa tashi,wani irin zugi ta keji ta k’asanta bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,da k’yar ta rarrafa ta sa ruwa a hita don daman bata iya wanka da ruwan sanyi,
Ta dad’e tana gasa jikinta sannan taji dama-dama,ta d’auro alwala tazo ta gabatar da sallah tana istigifari ganin lokacin sallah har ya shige bata yi,jin ana kiran la’asar yasa ta tashi tayi,ta dad’e zaune a gurin jikinta takeji wani iri duk saitaji kamar ta wani abu yasameta,ganin tunani zai dameta ta tashi ta koma kitchin ta daura abincin dare daman su Umma sun fita gidan suna k’anwarta ce ta haihu,
Tun daga wannan rana sai Naanah ta dunga jinta wani iri,da haka harta samu suka kammala jarabawarsu wa Waeci da Neco,kamar ana jira sukama sai yawan kasala da amai ga tofe-tofen miyau,da barcin ba gairi babu dalili,
Yauma suna zaune a farlour Abba da Umma sai Anty Rahma,kwance nake kaina bisa cinyar Abba muna hira,ina hammar barci,Rahma ta zubo abinci tanaci,k’amshin abincincin da naji yasani tashi da gudu nayi waje bakin fanfo na fara a mai kamar zan k’arar da yayan cikina,
Da gudu suka biyo bayana,Abba ya rik’eni yana”subuhanallah meke damunki ne Naanah,saida na wanke bakina sannan nace ina haki”Abba banda lafiya bansan abinda ke damuna ba,Umma ta matso kusa da ni tace”ni nasan wannan farin da Naanah keyi a kwai wata a k’asa,ta kamo hannayena ta bud’e tafin hannuna,ta bud’emin ido tare da le6an bakina,
Ta sakeni da sauri tana tafa hannu tace”yau na shiga uku ni Karimatu Naanah badai ciki ne da keba,basu Abba kad’ai ba hatta ni abinda ta fad’a ya furgita ni,Abba yace”Karimatu ki iya bakinki sharrin naki har yakai kice Naanah ciki ne gareta to aniyarki ta biki,tace”zanyima k’arya ne to wallahi baza a haifar mana shege a gida ba,Abba yace”ranki zai 6aci aniyarki saidai ta koma miki,ya kama hannu na muka koma ciki ba abunda nake sai kuka,bayan mun zauna Abba ya kamamin hannaye cikin damuwa yace”Naanah ki fad’amin gaskiya shin maganar Ummanku gaskiya ce ko yaya?,Nan na sake fashewa da kuka nace”wayyo na shiga uku Abba wallahi ni bana da ciki,ya saremin hawaye yace “nayarda da ke Naanah nasan sharri take miki sako hijabinki inkaiki asibiti a dubaki ko shawara ce gareki,da sauri na sako muka wuce,Umma sai surfamin ashariya take,
Gwajin likita na farko ya tabbatar cewa ina d’auke da ciki na wata d’aya da sati d’aya,wata k’ara na saki na zube a gurin ina kuka da birgima,Abba kuwa ko motsi ya kasa numfashinsa nayin sama-sama,yana k’okarin d’aukewa,da sauri ni da likitan mukayi kansa nan ya fara masa temakon gaggawa,
Abba na kwance gadon asibiti yayin da Umma da Rahma suna tsaye ni kuwa zaune nake da6as a k’asa ina kuka,tun jiya da mukazo asibiti sai yau Abba ya farfad’o,kwatance nawa likitan yaje ya kira su Umma don yana da kyirki sosai,Abba ya bud’e idanuwansa,yana zubar hawaye yace”Naanah kin 6ata wayonki kin cuci rayuwarki wallahi kin bani kunya,banta 6a tunanin zakiyi hakan ba,
Umma tace”aini yarinyar nan duk naga take-takenta kuma wallahi kinji na gaya miki bazaki haifar mana shege a gida ba,kuka na fashe dashi na kasa cewa komai don tun jiya da likita yace cikine gareni nazama kurmar k’arfi da yaji ni sonake ms in tuna taya hakan ta faru,
Kwanan Abba biyu aka sallamesa muka koma gida,
A falo muka zube,Idan banda aikin harara ba abinda nake samu daga gurin Umma,dole na sadda kaina k’asa ina kuka,Abba ya kalleni yace”Naanah ina so ki fad’amin tsakaninki da Allah CIKIN WAYE?A jikinki,kuka ya sartsemin harda majina nace”Abba ina so ka fahimceni domin kai mai fahimta ne wallahi bansan ko CIKIN WAYE?A tare dani ba,
Umma tace”kuji munafukar yarinya kije ayi miki cikin kice bakisan ko CIKIN WAYE?ba to k’aryarki tasha k’arya yarinya wallahi ki fad’a mana ko yanzun nan in yanka ki…..
Uhmm,hmmm,hmmmm
Kudai cigaba da biyono
Fateenku ce????
Ummu Affan✍????
????CIKIN WAYE?????
❤❤❤❤
❤❤
❤
Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee’u
(Ummu Affan)
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
Bismillahir rahmanir rahim
????2⃣7⃣-2⃣8⃣
????Wallahi ki fad’a mana gaskiya ko yanzun nan in yankaki,
A gigice na d’ago runannun idanuna na zuba mata,tace”kina ganin wasa nake ko mayya da shegun idanunta kamar na aljanu,da sauri na mayar dasu k’asa ina hawaye,
Umma tace”Rahma mik’omin wuk’ar nan a kitchin yau idan bata fad’i CIKIN WAYE?ba kasheta zanyi,Rahma ta nufi kitchin a gigice na tashi zan gudu ta rik’eni gam,Abba yace”Karimatu wannan wanne irin haukane,harara ta banka masa”ai gara ta fad’a musan ko waye tajecen gurinsa ta k’arata don ba za’a haifar mana shege a gida ba,ance duk gidan da aka haifi shege gidan ba a ruwan sama kuma mala’ikun rahma basa shiga gidan,
Abba yace”a’uzubillahi wannan wanne jahilin malamin ya fad’a miki hakan wallahi Karimatu kiwa kanki fad’a,cikin fad’a tace”na lura kai bakasan laifinta amma kana ganin abin kunyar da tayi so kake a dunga nuna mu a layi ko me?,yace”ba haka na ke nufi ba amma sai mu bita a hankali yadda zata sanar da mu ko,tsaki taja me k’ara tsuuuwwwwwww!!!,tace”kanka kuma a keji don wallahi bazan yarda a haifar mana shegeba,nan ta fara kimata kuka nake ina mata rantsuwa bansan CIKIN WAYE?ba,amma tak’i saurarata,
Ta sauta wuk’ar da Rahma ta kawo mata a wuyana cikin masifa tace”zaki fad’i CIKIN WAYE?Ko sai na kasheki,aini tunda naga wuk’ar nan a wuyana na tsure saboda tsabar tsoro,fitsari kuwa tuni ya fara juba ajikina,