COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“To ban gane ba na tambayeka ka hau sun kuyar da kai me hakan ke nufi?” Anty Ummu ta tambayi Zaidu cike da rashin fahimta.
Ubaidullah ya ce.
“Amma dai ba shirmen da ka fada min dazu bane kake wannan gulman sun kuyar da kan wa big Anty ba?”
Kallonsu Anty Ummu tayi ta ce.
“Kai ban fahimta ba me kuke nufi,kun sakani a duhu fa wace magana ce?” ta juya ga Ubaidullah.
Ubaidullah ya ce.
“Nifa wallahi har na manta ashe shi bai manta ba, kinsan jiya da nazo na yiwa su Na’ila duka har sai da na kaisu hospital”
Cikin firgici Anty Ummu ta ce.
“Me kuma su Na’ila suka yi da ka dakesu ,kuma har da Hafiza, ita da bata da hayaniya?”
“A’a Big Anty ba fa Hafiza ba ce, Na’ila dai da kawayenta,wallahi Big Anty bansan me yake damun Na’ila da yawo ba wai jiya sun je walima tun rana amma yaran nan basu dawo ba sai 9 ni kuma raina ya b’aci nayi musu duka ita da kawayen nata sannan na kaisu asibiti”nan ya dinga bawa Anty Ummu labari.
Anty Ummu ta ce.
“Na’ila kam ai sai dai Addua Allah ya shirya mana ita, amma Na’ila kam bata ji, to miye kuma Zaidu yake sun kuyar da kai din?”
Ubaidullah ya ce .
“Wai cewa yayi yana son Na’ila zai jirata nan da shekara biyar ya aureta”
Anty Ummu ta hau dariya tana kallon Zaidu.
Ubaidullah ya kuma cewa.
“Ina ma laifi ya ce Hafiza ita ma din tayi masa yarinya yanda yake b’ab’atun auren nan kam”
Sosai Zaidu yaji haushi yana hararar amininsa ganin yana so yaja ra’ayin Anty Ummu ita ma ta mai da maganar wasa yasa Zaidu tasowa yazo kusa da Anty Ummu fuskarsa babu alamun wasa, ya ce.
“My Big Anty plss karki biyewa Ubaidu ba zai gane bane amma Antyna ki yarda dani wallahi da gaske nake ina son Na’ila, kuma ko yanzu aka bani ita zan riketa ba tare da nayi mata komai ba har ta kai shekara sha shidda, zan ci gaba da kula da ita na raineta,amma bazan so na rabasu da ƴar uwarta ba saboda akwai shaƙuwa mai karfi a tsakaninsu, Anty karku duba cewa Na’ila tayi ƙanƙanta nima ai yaro ne, a wani kauyen ma wallahi Antyna karki yi mamaki kiga yarinya sa’ar Na’ila tana da yaronta a hannu, pls Antyna ki shige mun gaba ki bani kwarin gwiwa, am serious wallahi” ya ƙarasa cike da fuskar tausayi.
Sosai Anty Ummu ta natsu tana sauraron maganar Zaidu kafin ta numfasa ta ce.
“Karka damu ƙanina in dai har da gasken gaske kake yi, ni kuma nayi maka Alƙawari Na’ila matar ka ce”
Zaro ido Ubaidullah yayi kafin ya kalli Anty Ummu ya ce.
” What! Big Anty matarsa fa kika ce? ina wallahi Na’ila ba zata iya da kai ba, ka nemi wata mata” ya faɗa cike da sigar jin baki.
Anty Ummu tana dariya ta tashi tana cewa.
“ku kam halinku sai ku ,ba a iya muku ,yanzu dai idan naje gida zan faɗawa Mama ɗanta yana son ƴarta”
Sake sosa kai Zaidu yayi ya ce.
“Pls Antyna ki bari sai mun koma tukunna”
Dariya Anty Ummu tayi ta ce.
“Naƙi na bari ai gwanda Mama ta sani tun yanzu, kai kuma Dan Uwa zan ga ranar da zaka zo kace min ga zab’inka ina nan ina jira.”
Tabe baki Ubaidullah yayi ba tare da yayi magana ba, haka suka ci gaba da hira cike da nishaɗi, sai da akayi sallarh la’asar kafin suka yiwa Anty Ummu sallama suka nufi gidan su Zaidu.
~~~~~~~~
Da sallama suka shiga Inna ce kawai a tsakar gida tana ta faman sababi.
“Haba ace ayi yara basu jin magana kwata-kwata sai kace ƴaƴan jinnu to wallahi nikam ƙaniyarku zanci ƴan buhun uba, yara sai rainin tsiya wallahi mai sunan ifrituwa zaki dawo ki sameni ne ha.”
Zaidu ya ce.
“Oh Allah matar wa ya tabamin ke ne kam haka kike ta faman mita?”
“Kai dai bari kawai soja mugun mutum ni da ƙannanka mana masu kai kamar giginya, ai yau babu abin da zai hanani ban b’allawa yarinyar nan kafa ba mai sunan jinnu ifrituwa”
Zaidu ya ce.
“Yanzu dan Allah Inna ba zaki dai na kiranta da sunan ifritu ba, ba fa haka sunanta yake ba, sunanta (Afnan) ne”
“Mtswww dalla tafi can ka bani waje yara gaku nan duk suna babu tsari ba kan gado balle kan kujera, yanzu miye wani suna wai afirina?”
Dafe kai Zaidu yayi sannan ya ce.
“Ni dai Inna baza ki saka min ciwon kai ba, my man muje ciki”
“Au ka ce min tare kuke kai da aminin naka mai fuska kullum babu rahma,wallahi na tabbata idan na rantse bazan kaffara ba, wannan a alluran da ake yi muku shi nashi na musamman ne,dan ana yi masa ƙari da na rashin dariya, haba mutum kullum sai kace ana masa bishara da mutuwa?”
Girgiza kai Ubaidullah yayi sannan ya gaisheta ya wuce yayi gaba Zaidu ya bisa a baya nan Inna ta sake tasa wata sabuwar mita tare da zage-zage.
“Zaku ji dashi wato ina magana shine ku ka yi gaba, ku ka barni ina magana ni ka daina wato na ɗaɗe ban yi ba ko, da abokin kan nan da idonsa ƙifi-ƙifi kamar ta soyu gyada.”
Su dai basu kulata ba parlour suka wuce suka gaida Umma ta amsa tana cewa.
“Me yasa kuke son tab’o Inna ne kam? Kuma nasan kai ne Zaid,dan baka jin dadi in dai baka tsokani Inna ba, to wallahi ku kiyayeni yanzu suka gama dasu afnan kafin su fita”
Zaidu ya ce.
“Wallahi Umma nikam ban tsokaneta ba ai kinsan halin Inna”
Umma ta ce.
“To naji bar maganar haka kafin tazo ta sake fata-fata damu baki ɗaya”
Tashi suka yi, Umma ta ce.
“Ku huta kafin na gama abinci,”
Suka ce a’a sunci abinci a wajan Mama da kuma gidan Anty Ummu.
Umma ta ce .
“To yayi kyau ai haka ake so sun taimaka muku gauraye”
Su na dariya suka wuce gaba.
Sai yamma lilis gafen magriba kafin suka fita yawon zaga gari, basu koma gida ba sai bayan sallarh isha’i wajan tara zuwa goma, kowa gidan su ya wuce.
~~~~~~~~~
Da washe gari ma haka suka dinga zagaye gari, Ubaidullah har gidan dangin Baba yaje ya musu alƙairi wanda ya saka su jin kunya suka dinga kame-kame, amma yayi kamar bai san suna yiba.
Yau kwanarsu hudu sun fara shirin komawa Abuja bakin aikinsu, kafin nan kuma, Anty Ummu ta fadawa Mama yadda suka yi da Zaidu dariya Mama tayi ta ce, Allah ya zab’a abin da yafi alƙairi aka bar maganar a haka.
A kwanaki hudun da Ubaidullah yayi sam baya shga hidiman ƙannansa , wanda hakan ya saka su damuwa, Hafiza ce ta kawo shawara su masa girki da kansu sannan suje su basa hakuri karya tafi yana fushi dasu, hakan kuwa aka yi.
Suka shiga kitchen, Mama take tambayarsu, me zasu yi, suka ce zasu yiwa Yayan su girki ne, Mama ta ce. ” to Allah ya taimaka ta fita ta barsu”
Da misalin goma na safe, Ubaidullah yana tsaya a dress mirror yana shiryawa, waya ne a kunnensa, su na waya da K,B.
Sallama suka yi a hankali, jikinsu na kyarma saboda tsoro.
Amsa sallamar tasu yayi kafin ya ci gaba da wayarsa da K,B yana tabbatar masa akan cewa zasu dawo gobe, kafin suka yi sallama ya a jiye wayar ba tare da ya kallesu ba.
Na’ila ce tayi karfin halin cewa.
“Yaya mun shirya maka breakfast”
“Get out!! ya faɗa a tsawance, ba ƙaramin tsorata suka yi ba, a madadin su fitan kamar yanda ya bukata sai kawai suka ruga da gudu suka rungumesa sannan suka saki kuka a tare.
Nan take jikin Ubaidullah yayi sanyi dan yana da raunin zuciya wajan tausayi, ɗaure zuciyarsa yayi,daƙile ya kuma cewa.
“Ku sake ni!”
Amma sun ki sai kukan su dake ƙaruwa cikin ,Kuka Na’ila ta hau magana.
“Pls 4give me Yaya I promise u bazan sake ba, pls Yaya karka tafi kana fushi dani bazan sake ba na tuba pls Yaya trust me Yaya” ta ci gaba da kuka.
Ita ma Hafiza hakurin ta hau basa cikin sanyin muryarta.
“Yaya kayi hakuri mun san kana yine saboda son da kake mana but pls Yaya ka daina fushi damu”