COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Bayan an yiwa Na’ila Sallah a kofar Masallacin Jumma’ar dake unguwarsu kafin suka wuce maƙabarta.

Aka siya kabari aka yi komai,amma kafin nan sai da aka faɗi sunanta aka rubuta da date din da ta rasu da cutar da ya yi sanadiyar mutuwar tata da shekarunta.

Ubaidullah da Zaidu da KB Safwan da wasu samari Uku tsaye a gefe, wani Malami ya ce.

“Ita mai rasuwar tana da miji ne?” Malam Liman ya amsa da.
“A’a”

“To ina Mahaifinta?”
Ubaidullah ya rintse ido yana karanto “Innalillah wa inna ilayhirrajiun!”

Wani ƙanin Baban su ne ya ce.
“Mahaifin su ya rasu da ɗaɗewa”
Malamin ya ce.
“To ina wani ɗan uwa makusancinta ya matso kusa ya sakata a kabarinta”

Jikin Ubaidullah ya dauki kyarma, sai da Abba da Baba (Yayan Baban su) suka dafa Ubaidullah kafin ya wuce ya kamo kanwarsa yana yi mata kallon karshe a cikin likafani, zuciyarsa ce ke cewa.

“Yanzu Na’ilata kece wannan? Kece zan shinfiɗaki a karkashin kasa?” nan hawaye ya shiga wanke masa fuska har yana ɗiga akan likafaninta, babu abun da ya faɗo masa sai ranar da suka fita ya jibgesu ita da kawayenta, kuka sosai Ubaidulllah ke yi yana kwantar da ita a cikin kasa, yana gama shinfiɗeta ya ce.
“Allah yasa Annabi S,A,W, yasan da zuwanki Kanwata Allah yasa Annabin Rahma S,A,W, ya karbi baƙuntarki, ki yafe min Kanwata nima na yafe miki!” ya karasa yana kuka har da sheshsheƙa.

Zaidu ma Kuka yake yi kamar ranshi zai fita ya duƙa yana cewa.
“Allah ya haskaka ki My Lovely, Allah ya yafe miki..!” kasa karasa sauran adduar yayi kuka yaci karfinsa nan aka hau mai da kasa akan Na’ila yayinda Ubaidullah da Zaidu suka koma gefe suka rungume juna gam su na kuka mai ban tausayi.

Tun su na kallon likafanin Na’ila har aka gama tula mata kasa a kai ya yi tsini.

( Hummm Rayuwar kenan fa, ta bakin hausawa suka ce karshen alewa kasa, duk kudinka duk mulkinka dun kyawunka, duk kasaitar ka, duk izzarka, da zarar ance wannan ran ya fita a gangar jikinka nan ne madakatar ka, Allah kasa mu gama da duniya lafiya Ameen)

An juma ana yi mata addua kusan awa daya kafin jama’a suka fara watsewa.

Sai da kowa ya watse aka bar Ubaidullah Zaidu KB Safwan Abba da Abokan Abba mutum biyu.

Da kyar aka lallashi Ubaidullah da Zaidu suka tashi suka baro maƙabartan, su na tafiya su na kallon maƙabarta har suka daina ganinta.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A gida kuwa Likita tazo ta duba Mama har anyi mata karin ruwa, ta farfado amma bata um bare um um, saboda hawan jininta ya tashi sosai.

Hafiza kuwa sai da aka yi mata alluran bacci kusan biyar kafin bacci ya dauketa.

Su Ubaidullah su na dawowa daga maƙabarta nan fa sabon kuka ya tashi.

Anty Ummu ta shiga dakin su Na’ilan tana kallon pic dinsu da Hafiza, kuka Anty Ummu keyi kamar ranta zai fita tana cewa.
“Yanzu shi kenan fa kin tafi kenan, Allah sarki kanwata ashe ban kwana kika zo min jiya da safe, Allah sarki Na’ila Allah ya gafarta maki kanwata” ta ci gaba da kuka.

Ubaidullah part dinsa ya wuce kai tsaye bayan an dawo daga maƙabarta ana parking din mota ya fice, Zaidu da KB suka bi bayansa.

Yana shiga parlour ya fara fashe-fashe yana ihu, ba mutuwar bane abun da yafi ɗaga masa hankali da ɗimauta shi ba, a’a yadda mutuwar kanwar tasa ta kasance yasan mutuwa dole ce, baƙin ciki ne ke cin zuciyarsa idan ya tuno sanadiyar abun da ya kai kanwarsa kasa yau.

A rayuwarsa ya tsani yaji kalma mai kaman ceceniya da FYAƊE idan aka kawo case akan fyaɗe sai inda karfinsa a kare amma sai gashi kanwarsa sanadin fyaɗe ta mutu ta rasa ranta,sunyi sanadiyar kaita cikin kasa, taya zai yafe? taya zai daina yaƙi da masu fyaɗe? taya ba zai kara tsanar fyaɗe ba?
Taya zai gansu? Gashi bai san su ba, bai san ina zai samu mutane bakwai din nan ba, idan ma yace bincike zai yi ta ina zai fara? Ita ce ya kamata ta gaya masa suwaye amma Ubangiji ya karb’i abunsa hannunsa biyu ya zuba a kansa yana kuka mai ciwo, babu abun da ya sake faɗo masa rai sai lokacin da take fizge-fizgen azabar fitar rai take ce masa.
“Yaya su bakwai ne!”

Ihu Ubaidullah ya sake gami da dauƙar glass din table din da ya fara nan take ya farke hannunsa dashi, kuka yake ina faɗin.

“Ina zan gan kuuuuu!! Wayyo Allah ni Ubaidullah! Ya Allah kabani ikon cin wannan jarabawar da ka ɗaura min! Lokaci ɗaya na rasa abu biyu masu mahimmanci a gareni mafi soyuwa wanda ka karb’eta a gareni itace kanwata, Ya Allah hakika ina son yar uwata amma ka fimu sonta, Allah kai ne ka halicce mu, kuma dole zamu koma gareka, ya Allah nasan kanwata daka ɗauketa yanzu bata yi sauri ba, mu kuma daga barmu ba muyi jinkiri ba, Ya Allah ka sassauta mana raɗaɗin rashin baiwarka Kanwata Na’ila, ya Allah ka bayyana min ta inda zan ga azzaluman bayinka, hakika bazan gushe ba, bazan gajiya ba wajan nemo wanda suka aikata min haka na hukuntasu da hannuna ko da kuwa shine abun da zanyi na karshe a rayuwata, Ya Allah ka nuna min suuuu!!” ya zube kasa gami da kifa kansa akan kujera ya ci gaba da kuka.

Tun da Ubaidullah ya fara magana Zaidu da KB suke tsaye su na jin maganar tasa tana shiga kansu ɗaya bayan ɗaya, Zaidu ne ya matso kusa da Ubaidullah idonsa jajur ya duƙa gaban Ubaidullah cikin dasheshshiyar muryarsa wanda yasha kuka ya ce.

“My Man, ban fahimci maganganunka ba, ina bukatar karin haske, meya samu lovely? Me aka yiwa lovely? Kashe! Lovely aka yi!? Sannan suwaye suka kasheta? Duk tambayar da na yi maka ina bukatar amsar su!?”

Shima Ubaidullah ɗaga rinannun idanuwansa yayi wanda idan ya kalleka dasu zaka iya rantsewa idanunsa basu taba fari ba, miƙewa tsaye yayi cikin ƙaƙƙausar murya ya ce.

“Zaidu Kasheta suka yi!”

Shima Zaidu mikewa yayi jikinsa har na b’ari cikin zaƙuwa ya ce.
“Su waye?”

Hannu Ubaidullah ya ware.
“Nima abun da nake tambaya kenan, SU WAYE!? Zaidu abun da na fi tsana a rayuwata wai yau shine ya faɗo akan kanwata, Zaidu FYADE FA AKA YIWA KANWATA! FYAƊE!FYAƊE!FYAƊE!”

Saurin toshe kunnuwansa Zaidu yayi take ya ji jiri na ɗibarsa maƙogoronsa ya ji har wani ɗaci-ɗaci take masa, kishi haushi baƙin ciki duk suka haɗe masa waje guɗa har wani duhu-duhu yake gani.

“Whattt! Fyaɗe!? Fyaɗe!? Fyaɗe!? Wa matar da na zauna jira zan aura din? Yanzu lovely fyaɗe aka mata?” yayi maganar hawaye na sake wanke masa fuska yana kallon Ubaidullah.

Jinjina kai Ubaidullah yayi ya ce.
“Ta ce mutum bakwai, amma bata faɗa min su waye mutum bakwai din ba, amma abu ɗaya na sani shine zan bazama neman mutum bakwai din nan na kashesu da hannuna duk da yanzu ni ba jami’i bane”

KB ya ce.
“Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Hakika wa inda suka aikata abun nan basu san su wa suka tab’o ba, basu san sun taba yar gidan soja kanwar soja wanda yake sa ran auranta soja ba, amma komai muyi hakuri mu kuma dage da addua Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa amma zasu gane basu da wayo, ni dai abu ɗaya na sani shine duk rintsin rayuwa duk tsanani duk wuya muna tare da kai Ubaidullah”

Kuka suka saka a tare gami da rungumar Juna.

Sallama aka yi, wanda ya saka su sakin junansu suna share hawaye, Abba ya girgiza kai ya ce.
“Haba Ubaidullah, zaman gaisuwar kanwarka fa akeyi amma ka dawo ciki kana kuka kayi hakuri dan Allah mu dauki kaddara kowa lokaci yake jira Allah yasa Na’ila ta huta”
Suka amsa da ameen, kafin Abba ya saka su a gaba suka koma kofar gida ana karban gaisuwa amma kallo ɗaya zaka yiwa Ubaidullah shi da Zaidu ka fahimci kalar tsananin tashin hankali da damuwar da suke ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button