COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yau kam duk sun gama shirinsu na tafiya kasar india, sun kara training na tsawon kwana biyu ne kacal, zaune suke a airport su na jiran tashin jirgi sojoji su dari da saba’in da bakwai ne zasu tafi, manya ja gaba a wannan tafiya mutum na farko shine Commander Isa Bala, sai kuma ja ragamar yaƙi wato Captain Ubaidullah, da kuma mai taka masa baya Captain Zaidu da Mataimakinsa first lieutenant KB da dai sauran rundunar sojojin 9ja barracks, wayarsa ya ciro ya yi waya dasu Mama, Anty Ummu, Hafiza, Ummi, Abba da Safwan wanda a halin yanzu an sallamosa izuwa gida ya ji sauki sosai Ma sha Allah, alhamdulillah, an ci gaba da shirin yin shagalin bikinsa, dasu Umma,Inna, sai da ya gama waya dasu kafin ya kira Matarsa, ji ya yi gabansa na faduwa, sai da ya mata kira kusan uku kafin ta ɗaga,a tare suka sauke ajiyar zuciya, sun kai kusan mintuna shabiyar kafin ya fara mata magana kamar mai raɗa.
“Madam, gamu a airport zamu wuce, ayi mana addua, Allah ya kaddara saduwarmu, sharrin karfe ma kadai wani ishara ne, kuma kin ga…..” bai karasa ba ta saki kuka har da sheshsheƙa, sosai hankalin Ubaidullah ya tashi, gefe ya koma yana shirin ya lallasheta amma kashh!! Nan aka fara kiraye kirayen sunaye jirginsu zai tashi dan haka bai samu damar lallashinta ba, a hankali ya ce.
“Ki kula min da kanki, In sha Allah zan dawo, idan na samu sarari kuma zan din ga kira dan ku ji lafiyata nima naji ta ku, I LOVE U MY ABI’AH goodbye” ya tsinke wayar ihu Abi’atu ta saka wanda yasa Hafiza dake kusan shigowa parlorn ta karaso da gudu, Hafiza ta san kukan da Abi’atu take yi, dan itama yanzu ta gama tata kukan, shine Mama ta ce mata taje ta dubo Abi’atu ta kirawota ta daina zama a part din ita kadai, rungume Hafiza Abi’atu ta yi tana cewa.
“Hafiza ya tafi fa!! Ya tafi ya barni wayyo mijina” cikin kuka Hafiza ta ce.
“Anty ba fa mutuwa ya yi ba, mu tayasa da addua, barin ma ke da Mama, dan Allah ki bar wannan kukan Anty, kar ya jawo miki ciwo” ta rungumeta tana lallashinta itama tana kuka, a hankali Abi’atu ta ce.
I LOUVE U TOO MORE MY UBAID, SO MUCH LUV MIJINA, ALLAH YA DAWO MIN DA KAI LAFIYA YA BAKA SA’A” ta ci gaba da kuka, haka ranar Abi’atu ta wuni sakoko ba guzari a jikinta har ta wani fige dan tafiyarsa da ya yi, dama gata ba wani auki ba.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A bangaren Alhaji Madugu sunje sun kwashi gawawwakin ƴaƴansu, yayinda Alhaji Madugu ya yi matukar tunzura da ya ga gawar dansa a wulakance, nan ya ci alwashi gami da lashen takwabin ganin bayan farin cikin Ubaidullah na har abada.

(Wannan kenan mu ci gaba da kaftawa Mah ppls ????????‍♀️????????‍♀️)

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Alhamdulillah su Ubaidullah sun sauka a kasar india lafiya, ya yinda suka duƙufa aikin abun da ya kawosu izuwa kasar, sunje yankin bangaladash amma sam babu wani information da suka samu dan gane da yan matan da aka yi garkuwa dasu, basu yi kasa a guiwa ba suka sake zuwa yankin bangalour amma duk abu ɗaya ne, sosai hankalinsu ya tashi, sun kwashe wajan sati biyu su na faman ƙetara yanki yanki dake india, wanda ta’addanci yake bunƙasa, amma basu samu komai na labari da ya danganci yan matan nigeria ba, tun da su Ubaidullah suka zo india babu wanda ya rintsa a cikinsu, idan kuma musulmai zasu yi sallah sai dai suyi taimama idan sun risƙi wajan da ba ruwa, abinci kuwa duk abun da ya samu ci kawai Suke yi, da haka a wahale su Ubaidullah suka share wata daya a india, kuma tun da suka zo sau biyu kacal suka samu damar yin magana da yan gida, wasu daga cikinsu har sun fara fidda ran nasara ga wannan aikin amma sai Ubaidullah ya kara musu karfin guiwa, yau ma kamar kullum su na zazzaune a jejin Naidu wani sergeant ya ce.
“Sir, a gaskiya na fara karaya, yau fa watanmu daya har da kwana biyar a jeji,amma babu wani information anya ba gida zamu koma ba kuwa? Mun je yanki yanki yafi sama da talatin a kasar nan amma shuru, sai kace maye yaci shirwa” shuru gaba dayansu suka yi, Commander Isa Bala ya kalli Ubaidullah ya ce.
“Captain me ka ce akan wannan batun?” Ubaidullah ya kai kusan minti goma kafin ya miƙe tsaye da sauri ya ce.
“Bamu je yankin Kashmeer ba” Zaidu ya ce.
“Yes of course bamu je ba kam tabbas” Ubaidullah ya ce.
“Da asuba zamu wuce Kashmeer” addua suka yi Allah ya basu sa a.

   @@@@

Da asuba suka gama shirinsu tsaf zasu shiga yankin Kashmeer da ga in da suke 100km ne, dan haka da zasu shiga yanki mutanen da suke haduwa dasu a hanya idan suka ce musu zasu shiga yankin kashmeer wasu har gargaɗansu sukeyi domin kuwa yan ta’addane da suka gagari rundunar hukumar ƙasar india baki ɗaya, nan su Ubaidullah suka sake shiga, amma da ta ka tsantsan sabida su na dauke dasu mugayen makamai, tun daga farkon sassaninsu aka fara tarbo su Ubaidullah da ruwan alburushi, nan fa yaƙi ta barke yayinda sojojin nigeria aka rarraba kafa nan su ma suka shiga mai da martani, yaƙi ne wanda ake kira KO KA KASHE!! KO A KASHEKA!! a dan ƙanƙanin lokaci Ubaidullah ya zubar da mutane kusan dari a kasa, yawancin yaƙin shi ya fi kowa kokari, dama shine karfin guiwar yaƙi, Zaidu ma ya yi kokarin dan ya zubar da hamsin, KB ma haka, kowa yana iyakar kokarinsa wajan cuto rayuka, taƙaddama kamar wasa amma inaa yaƙi sai kace ana karawa wuta fetur dan kuwa yan ta’addan su na da mugun yawa, Commander Isa Bala ganin an fara zubar da sojojin nigeria dan ga shabiyar kwance a cikin jini nan ya bada Umarnin su gudu, haka aka fara ja da baya, yayinda Ubaidullah yake kara tura kansa cikinsu, kwala masa kira Commander Isa Bala ya yi ya ce.
“Captain!!!!! Kazo mu gudu tukunna!!” juyowa Ubaidullah ya yi, ya girgiza kai alamun ba gudu ba ja da baya, da kyar fa Zaidu da KB da wasu sojoji goma suka yanje Ubaidullah suka gudu can wajan kasar babbar rafin kashmeer suka maƙale, ga shi dare har ta yi, wa inda suka ji rauni ne aka fara yi musu magani ta hanyar hura wuta da wuƙa aka cire musu bullet yayinda mutum uku suka rasa rayukansu, sosai hankalin Ubaidullah ya tashi dan har ya fara tausayin iyalansu.

✨✨✨✨✨✨✨✨

MOMYN AHLAN TAKU CE????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

~UBAIDULLAHI~
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0
•~~•
Special gift to my 5 ☆stars★
Samira bint Abdallah????
Fatima bintu Sagir????
Farhat Mrs M’J????
Princess (Nafeesat)????
احلام فاطمة????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

SAKON BARKA DA SALLAH GA ADMINS DIN (COLONEL UBAIDULLAH FANS 1 GRP ????????

@⁨????mhiss precious????????????‍♀️⁩
@⁨Kulsuum Muhd Sadeeq⁩
@⁨Sahra????????⁩
@⁨JOURNALIST????????⁩
@⁨Mrs……. Ce????⁩
@⁨Mrs. Meenad⁩
@⁨Mu’az⁩
@⁨Rashida Usman⁩
@⁨Be smart????????⁩
@⁨fateema bintu sagir⁩
@⁨احلام فاطمة⁩
@⁨Afnan❤️

SAKON BARKA DA SALLAH ZUWA GA DAUKACIN MEMBERS DINA MASOYANA YAN (COLONEL UBAIDULLAH FANS 1 GRP) ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button