COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ke har kin isa ki daga min murya Rumaisa? Da kika cewa ni ba uwarki bace bana fata Idan nayi aure Allah ya bani ƴa kamarki mashanranciya munafuka!, sannan a ta wani fanni ni nafi karfin uwarki! ko ubanki!, dan kinsan duk matan barracks din nan babu wacce ta kaini zafi, idan kuma akwaita ta ɗaga min hannu, tambayarki nake yi dan musan gaskiyar lamari, kuma ni ban daga miki murya ba, me yasa ni za ki daga min murya? Ko ni mate dinki ce?”

Filin taro kamar ba kowa, dan kuwa rashin gaskiya ya bayyana ƙuru-ƙuru a fuskar Rumaisa, dan haka su General Of The Army, General, Major General, General, Colonel, Brigadier lieutenant Colonel duk manyan wajan babu wanda ya dakatar da Zeey ko kuma ya katseta ko ya ce abun da take yi bai dace ba, sabida yanzu mafita suke nema, dan nadama ta fara kamasu, su na so su san gaskiyar lamari dan a samu a ba wa Captain hakuri ya dawo bakin aikinsa dan a samu a ceto rayuwar yan matan da aka yi garkuwa dasu, sabida rayuwarsu tana cikin hatsari.

Marin da Zeey ta kifawa Rumaisa sai da ta ga gittawar wasu taurari a idanuwanta da fuskarta, network din kanta sai da ya je hutun wucin gadi, kafin da kyar ta miƙe tsaye tana dafe mararta wanda ya murɗa mata lokaci guda.

Kuka Baban Rumaisa ya saka gami da cewa ana so a tozarta sa shi da ƴarsa, amma babu wanda ya sauraresa.

Ganin badaƙalar tana yin yawa ne, kuma ga shi asiri yana gaf da tonuwa ya sa, S Ema neman hanyar da zai fece daga filin taron, amma me tuni KB yasa masa kafa ya fadi gami da cewa.
“To Almirin’jaki, baƙin munafuki algungumi, ina zaka je?” nan aka juyo ana kallon S Ema, Zeey ta ce.
“Shi ma wai guduwa zai yi ko? Hahaha ina son irin haka, KB riƙesa da kyau ban zo kansa ba tukunna”

“Rumaisa ke muke saurara?”

Cikin rawar murya Rumaisa ta ce.
“Ni kam sharri! Kike so ki min, amma ni kam bani da wani ciki.”

“Au haba? To shi kenan, Dr Mark!?” Zeey ta kwalawa Dr kira wanda dama yana kusa, babban likita ne a cikin asibitin dake barracks yawanci idan ciwo ya yi tsanani shi yake duba marasa lafiya masani ne sosai ta fannin aikinsa, kuma babban mutum ne dan a kalla shekarunsa zai iya kai wa 69 yawanci ana girmamasa a barracks din sosai.

Tun da Zeey ta ambaci sunan Dr Mark, hankalin Rumaisa ya sake tashi, fitowa Dr Mark ya yi, dan shi ma Ubaidullah mutuminsa ne sosai, kuma yana son Ubaidullah, sabida kamun kai din Ubaidullah yasa yake birgesa,duk da yana barracks din amma bai san abun da ya faru da Ubaidullah din ba, tun da baya shiga hidimar fannin aikinsu yafi zama wajan fannin aikinsa, hawa kan mumbari Dr Mark ya yi, sannan cikin girmamawa Zeey ta zo gabansa da takardun hannunta ta ce.
“Baba Mark, kai ne ka gwada Rumaisa shekaran jiya har result ya fito jiya,a in da ka gano tana da jaririn ciki na tsawon wata biyu haka ne?” cikin harafin turanci suke magana.

“Shakka babu, nine nan na au’na ta kuma ga result din a hannunki, tana da jaririn ciki na wata biyu”

“Good! Ko Rumaisa ta taba yin b’ari wata biyar da suka wuce? Tun da dai nasan babu wani asibitin da zata kwanta in dai bana cikin barracks ba?”

“No, bata kwanta ba, cox 2years kenan yanzu ban yi tafiya ba, ina nan, balle ace ko bani nan wani Dr ya dubata.”

“Tnk u sir” cewar Zeey, kafin ta juyo ga Rumaisa, wacce hankalinta ya kai ƙoluluwa wajan tashi, dan tasan karyarta ya kare yau.

“Rumaisa lokaci ya yi, da za ki bude baki kiyi magana, shawara ce nake baki,tun kafin na bayyana wani video kuma idan har na bayyana videon nan ba kiyi magana ba hummm! Rumaisa ni a karan kaina bansan abun da zan iya aikata maki ba, gwanda ki bude baki kiyi magana, First Lieutenant KB ka hauro da S Ema.”

Nan KB ya hauro da S Ema wanda shi ma yake zare ido, Zeey kallonsa take yi ranta bace ta ce.
“Zaku yi bayani ne ko kuma sai na saki videon? Kunsan halina wajan bincike bana sanya barin ma wanda na saka kaina, akan Captain zan iya muku komai, dan haka zaku faɗi gaskiya ne ko har yanzu zaku ci gaba da kauce-kauce da neman hanyar guduwa, ko kuma kokarin shirya drama, kai za kayi bayani ne, ko kuma karya za ka yi kamar yadda ita…b sai na karasa ba dan ka fi ni sani abun da nake nufi ko?”

Shuru S Ema ya yi gabansa na faduwa suka haɗa ido da Rumaisa, sai zufa suke yi, Zeey ce ta ce.
“Bana son aiki da bata lokacin dan hak…”

“No! Pls!” cewar Sergeant Ema.
“Zan fadi gaskiya duk abun da na sani.”

“Yauwa dan gari, muna sauraron ka?”

“Lokacin da nazo barracks din nan Captain baya nan amma ina jin labarinsa, kasancewar ni mutum ne mai ƙyashi da hassada, da haka har alaƙa ta shiga tsakani na da Rumaisa, har take bani labarin Captain Ubaidullah da yanda take son sa take sha’awarsa, ko da Captain Ubaidullah ya dawo daga tafiyar da su kayi na ganin gida, na ga yanda ake ba da labarinsa yana da kyau da gwarniji kamala, haiba, nasaba, kamun kai, ji da kai, jarumta, gwarzon maza, ƙi gudu sa maza gudu, dana gansa sai na ga duk yafi yadda ake bada labarinsa, da haka ne Rumaisa ta zo ta sameni wata rana da wani video karami wanda ta rungume Ubaidullah har ya wanka mata mari, to wannan videon ne muka haɗa lokacin ne muka kwanta da Rumaisa a karo na farko sabida ta ce tayi alwashi sai ta muzguna masa, fuskata ne muka yi amfani da shi muka saka fuskar Captain, wanda da shi ne aka samu madafan dafawa domin a tozarta shi ya aureta, shi kuma ya ƙi, ko bayan faruwar hakan da ya bar aiki bamu daina mu’amala da Rumaisa ba, kuma babu wani ciki a tare da ita lokacin, munyi wannan videon ne dan mu kawar da tunanin manya dan kar ace aje a au’nata, kuma munyi nasara a wancan lokaci, kuma ko yanzu cikin da yake jikin Rumaisa nawa ne, wannan shi ne gaskiya abun da ya faru wanda na sani amma dan Allah ayi hakuri bazan sake b…”

“Shut up!!” Cewar Zeey ta katse sergeant Ema idanunta sunyi ja, juyawa ta yi ta kalli manya ta ce.
“Kun gani ko? Kun gani ko? Abun da muka ta fama ku fahimta kenan tun kwanaki amma kun kasa fahimta, ba iyakar binciken da nayi akan Rumaisa ba kenan, domin tun lokacin da Captain ya bar barracks na fara bibiyar rayuwar Rumaisa da duk wani shige da ficenta, ko da muka je bauchi nice kawai bani nan amma duk abun da ke faruwa ina sane dashi, idan wannan hujjar bai isheku ba, sai na sake muku wasu wanda zaku gansu ƙuru-ƙuru, kuma Wallahi Rumaisa idan har ba ki buɗe baki kinyi magana ba ko, Rumaisa idan na rufeki da duka sai na kaiki lahira kuma na kashe banza! Idan kince wasa ne to mu zuba mu gani!”

Nan Rumaisa ta zube kasa tana kuka, tana cewa ta tuba a yafe mata, Major Usman ya ce.
“A tafi da Rumaisa da S Ema a saka su a guardroom, kafin a san abun yi” nan Rumaisa ta hau ihu tana kuka tana magiya, Babanta ma yanayi, amma ina babu wanda ya saurare su, nan fa aka ce an kira secret meeting a secret room wanda manya ne kawai zasu yi wannan meeting din, dasu Zaidu da KB, amma daga ciki har da Zeey.

Ko bayan da aka shiga secret meeting magana ce ake yi akan ya za ayi aje a bawa Ubaidullah hakuri ya dawo bakin aikinsa.

Zeey ta ce.
“Captain Zaidu ka kira mana Captain Ubaidullah”

Murmushi Zaidu ya yi, ya ce.
“Nasan halin Ubaidullah sarai, ba zai taba yarda ya dawo ta dadi ba, but let me try my best” Zaidu ya faɗa yana kokarin kiran Ubaidullah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button