COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Dan sosa gefen wuyarsa yayi dan shi bai cika son yiwa Mama karya ba amma yanzu ya zama dole ya suturta maganarsa.

ya kafin ya ce.
“Am so sorry my Momma, ina fita wani kiran ya taso min shiyasa dole na je nayi wancan aiki tun da nasan kun fita da Zaidu zai yi abun da ya kamata.”

“Oh Allah to da Zaidun bai zo ba kuma fa?”

“Kiyi hakuri Mama tun da ya zo ai shikenan, yanzu ina Zaidun ya ke?”

Mama ta juya ta shiga kitchen tana ba sa amsa tana kiran sunan Hafiza.

Fita yayi ya je ya samu Zaidu zaune a kujera ya duƙufa akan systerm, sallama Ubaidullah yayi, Zaidu ya ɗago ya kallesa ya amsa, ganin sai wani cin magani yake yi yasa Zaidu ɗauke kansa shi ma ya ci gaba da abun da yake yi.

Can zuwa anjima Hafiza ta shigo da sallama, suka amsa kafin ta ce.

“Mama ce ta aiko ni na zo na tambaye ku, a kawo muku abincin nan ne ko zaku zo ku ci?”

Zaidu ya kashe systerm din dake cinyarsa ya tashi yana cewa.

“No my sister nikam a wajan Mama zanje na ci amma bansan wannan Yayan naku dan zafin kan ba”

Tsaki Ubaidullah yayi shi ma ya tashi suka fito a tare, har izuwa parlour, Mama ta shinfiɗa musu babbar lade na cin abinci, suka zazzauna.

Hafiza ta zauna can nesa dasu tana jiran fitowar Na’ila amma shuru ba Na’ila, ita kuma Hafiza ba zata iya cin abincin ba matukar y’ar uwarta ba ta fito ba.

Zaidu ya kula da haka ya juya yana kallon Mama ya ce.

“Mama meya faru ne kam, me aka yiwa my lovely aka faffasa mata jiki gashi yanzu taƙi fitowa ta ci abinci?”

“Zaidu wannan lovelyn dinka bata jin magana kwata-kwata jiya wai sun tafi walima yaran nan tun rana amma sai karfe tara na dare suka dawo, sai ka ce basu da mafaɗi, shiyasa Yayansu ya jibgesu har da kawayen nata ai kaga gobe ba zata sake zuwa ba, na rasa dalilin da yasa Na’ila bata jin magana tun dana iyanzunta take son tuburewa ai gwanda ya mai dota saiti.”

Zaidu ya ce.
“Haba Mama yanzu a gabanki ya musu wannan dukar sai kace ya kama b’arawo a guardroom? abokina nan fa ba barracks ba ne, gida ne bai ka mata ka dakesu da belt din sojoji ba ,gaskiya ban ji dadin haka ba, yes punishment din da ka musu shi ne dai-dai kuma naji dadi da ka haɗa har da friends din gobe ba zasu ƙara zuwa su ja ta ba, amma dukan yayi worst gaskiya ka dinga sassautawa.”

Mama dai bata sake cewa komai ba illa ma tashi da tayi ta shiga daki tabarsu a wajan.

Ubaidullah ma ko uhum bai cewa aminin nasa ba.

Zaidu ya kalli Hafiza wacce ta raƙube a gefe ya ce.
“My sister oya tashi ki je ki kira min my lovely”

Hafiza ta amsa da to , ta tashi tayi hanyar dakinsu.

Da sallama ta shiga ta samu Na’ila zaune ta zuba tagumi har yanzu fuskarta a kumbure yake, wani tausayin yar uwarta ne ya kamata, tazo ta zauna kusa da ita ta ce.

“Sister ki taso ki zo muje muci abinci mana?”

Girgiza kai Na’ila tayi ta ce.
“Na ƙoshi bana jin yunwa jikina ne yake min ciwo”

“To ki sha paracetamol sai ki zo muje Yaya Zaidu ya ce na zo na kira ki ,kuma na tabbatar mun zo tare ki taso muje kinji siaterna”

“Yaya yana parlourn?”

Ta tambayi Hafiza.

Hafiza ta ce.
“Eh mana yana parlor ina so idan mun je ki basa hakuri kinga Yaya yana sonmu amma ke baki jin magana ,Na’ila ba kyau Mama ta ce kibar abu amma ki ƙi ji Yaya ya hanaki yawo Anty Ummu ma ta hanaki amma duk baki ji, ki ga fa idan har Anty Ummu ta saka Yaya abu yana yi fa, to ke meyasa idan ya sakaki ba zaki ji ba ko kinga ni haka nake yi ne iyee?”

Girgiza kai Na’ila tayi alamun a’a.

Kafin Hafiza ta ce.
“To ki natsu kin ga dai yanzu Yaya, ya zama mugu amma bana mugunta ba dan haka mu bisa a hankali mu dinga jin magana, gashi karba ki sha muje”

Karban maganin Na’ila tayi tasha da kyar, kafin suka fito sai rakub’e-rakub’e suke yi dukkansu.

Su na fitowa Ubaidullah ya musu kallo daya yaga yanda jikinsu ke rawa alamun tsoronsa suke ji ,shi kuma ba haka bane burinsa ace ya zama dodo a wajan ƙannansa.

Dan haka su na fitowa ya tashi ya fice yayi hanyar part dinsa.

Zaidu ma fada yayiwa Na’ila sannan ya bi bayan amininsa.

Kwance ya samesa a 3sitter ya lumshe ido.

Zaidu yayi murmushi ya ce.
“Na ga kalar soyayyar yan uwa, amma shine duk da haka ka shirgiɗa musu na jaki?”

“Mtsww Zaidu ba zaka gane bane izuwa yanzu yaci ace ka gama karantar halina”

“Eh na fahimce ka my man addua zamu dinga musu, ni fa kasan wani abu kuwa?”

Ubaidullah ya girgiza kai yana kallonsa.

Zaidu ya ce.
“Ni wallahi da zaka ban Na’ila ita nake so wallahi zan jirata nan da shekaru biyar na aureta dan ina sonta.”

“Hahahah Zaidu kenan ko dai ka fara shaye-shaye ne? Na’ila fa ka ce ina zaka kai wannan gagaran,dama Hafiza ka ce yauwa amma Na’ila sai a hankali” ya karasa maganar yana dariya sai ka ce ba shi ba.

Abun da Zaidu ya fahimta shine Ubaidullah ya dauki maganarsa a matsayin wasa shi kuma da gaske yake yi ,amma ba komai zai basa mamaki.

Zaidu zai sake yin magana ,Ubaidullah ya ce.
“Ka ga tashi muje na gano y’ar uwata Yayata Anty Ummu naje naga lafiyarta daga nan naje na gaishe da Umma, mu zagaye gari tun da 5days kawai zamu yi.”

Zaidu ya ce.
“Ok mu je”

Fitowa suka yi a tare sai da suka yiwa Mama magana kafin suka shiga mota suka bar gidan.

   ~~~~~~~~

COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍????????????‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~
MARUBUCIYAR

HALITTA DAGA ALLAH NE
GUDU A JEJI
SHUHADA
NIDA ƘANNAN MIJINA
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????


Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

________________________

page°°°°11&12

Ganin haka yasa Mama hankalinta tashi, dan tasan ba ƙaramin aikinsa ba ne yan zun nan ya musu lahani.

Ubaidullah dake riƙe da kafaɗun Mama jin abun da dayan saurayin nan ke fadi ya saka shi sakin Mama ya juya a fusace cike da zafin nama, cikin hanzari Mama ta riƙosa gam kafin ta ce.

“Kul Ubaidullah ban yarda ba ban amince ba karka taba daya daga cikinsu ka kyalesu muje, mu shirya, mu wuce asibiti a duba yaran sannan a basu ƙannan su, dan ni gaskiya banji dadin haɗawa da yaran mutane da kayi ba, danni ban son damuwa da hayaniya ko tashin hankali basu da dadi.”

Mama ,tana ta mita riƙe da hannun Ubaidullah wanda gabakid’aya jijiyoyin jikinsa sun fito raɗa-raɗa, tsantsan bacin rai, domin maganar saurayin yayi mugun bata mishi rai har gadara yake yi cewa shi dan sara suka ne kuma har yake fada masa ko dan bai san shi waye ba ne”? ya tambayi kansa.

Da kyar Mama ta janye Ubaidullah ,suka shige cikin gida.

Mama ta zaunar dashi ganin yanda jijiyoyin jikinsa ya fito ya bayyana, idanunsa suka sake ƙanƙancewa ,suka yi jajur dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button