COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da washe gari sun makara sallah dan bacci ya musu dadi, rabon da su yi bacci kamar haka sun manta, sai karfe goma suka yi sallahn asuba, bayan sun idar suka sake komawa bacci basu da farkawa ba sai karfe biyu, nan ma sai da Anty Ummu ta aiko Hafiza ta duba ko su na lafiya, tukunna suka tashi, ta taimaka masa ya yi wanka ta shirya shi, itama ta yi ta shirya sannan ta kama shi suka yi part din Mama, tun daga kofar parlour hayaniya ke tashi, su na shiga kuwa suka iske mutane, su Ummi ne dasu Umma, Inna, Zaidu, Anty Ummu, Yaya Safwan da Matarsa Shafa’atu, da sauran maƙotan arziƙi, su na shiga aka hau gaishe-gaishe, Inna ganin Ubaidullah ta ce.
“Ohh Allah Ubaidu? Sannu ansha fama,an wuce da kyar ko? Yanzu sabida rashin imani haka suka yi maka? Dan ma kana da taurin rai inaji da yanzu zaman makoki muke yi, ina dalili da wannan aikin soja, kun bar mu cikin firgici da tashin hankali, gaskiya ni kam abun ya isheni” ta karasa maganar tana haɗe rai, Ubaidullah suka yi dariya shi da Zaidu, ba tare da sun bawa Inna amsa ba, aka ci gaba da hira su na bada labarin tashin hankalin da suke gani kafin Zaidu ya fara bada labarin yan ta’addan da aka kashe da sojojinsu da aka kashe duk da sunji a labarai amma ance waka a bakin me shi yafi dadi, yawancin mutanen da suke wajan fatan Alkhairi suka din ga yiwa sojojin nigeria, tare da adduar Allah ya daga nigeria, su Safwan ne suka miƙe su na yiwa jama’ar dake wajan sallama dan Shafa’atu bata jin dadi tana faman da laulayin karamin ciki, tun da Ubaidullah ya fahimci Shafa’atu na da ciki ya ji shi ma fa a duniya yana son ya ga Jininsa kwanan nan, inda ya kudirta a ransa kafin ya koma barracks sai ya mai da Abi’atunsa cikakkiyar mace, hira aka sha da Ubaidullah kamar ba shi ba, duk da azaban ciwon da yake ji a jikinsa, sai dare kafin jama’a aka watse.

Haka aka din ga yi har na tsawon sati daya ana cika a gidan Mama tamkar wanda ake shagalin biki, jikin Ubaidullah Ma sha Allah yana samun sauki kasancewar Hajiya Abi’atu an zage dantse wajan kula da miji, abun da yasa ta kara mai da hankali sabida yan matan da ta ga su na shigowa masu baki kamar na jab’a wai su na zuwa gaishe da mijinta ko wacce da kalar fari da idon da take masa, shi yasa ta sake ƙaimi wajan ba shi kulawa, da haka har ya yi sati biyu, kuma yanzu alhamdulillah yana iya daga dayar hannun nasa, wajan ciwon ya fara kamewa, yau ma kamar kullum ta fito daga kitchen shi kuma yana zaune kasar carpet, zama ta yi kusa da shi hannunta dauke da cup, fara ba shi kunun ta yi a baki yana sha, ya dan ja kumatunta, ya ce.
“Abi’ah?” kallonsa ta yi ba tare da ta amsa ba, ya kuma cewa.
“Abi’ah, KINA SO NA?” gabanta ne ya faɗi, tabbas tana son shi mana, amma sai ta tsinci kanta da kasa ba shi amsa, shi ma ganin ta yi shuru bai sake ce mata komai ba, illa zullumin da zuciyarsa ta shiga, tashi ta yi sabida ya gama shan kunun, tana tashi ya bita da wani kallo wanda ya haifar masa da kasala da jan ido, hakika Abi’atu tana da sirhitaccen kyau, jinginuwa ya yi da kujera ya lumshe ido yana taro yadda take tafiya halittar jikinta yana motsawa, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai sani ba, sai da ta da fa shi ta ce.
“Lafiya kuwa?” bude ido ya yi, ta ga yadda idonsa ya rine, ta zaro ido ta sake jefo masa tambaya.
“Ya salam! Me ya same ka ne? Ko wani waje na maka ciwo ne?” bai bata amsa ba ya sake lumshe idonsa, kamar da, 5mins haka ya ce.
ABI’ATU, nayi miki tambaya amma ba ki bani amsa ba, ko me yasa?” sake yin kasa ta yi da kanta tana wasa da fingers dinta, ji ta yi ta furta masa tana son shi ya mata tsauri a baki, fizgota Ubaidullah ya yi ta zube a kirjinsa wanda sai da ta bugi ciwonsa da sauri ta ce.
“Ciwon ka fa?” zata sa hannu da hannunsa marar lafiyar ya ture hannunta kamar zai yi kuka ya ce.
“Ban damu da wannan ba kawai ni ki bani amsata, do u luv me?” Shuru ta yi tana dan wani nazari kafin ta gya ɗa masa kai alaman eh, sake matseta ya yi a jikinsa dan farin ciki,duk da dai ya so ta furta ne a baki ba wai da kai ba, amma ya san ta da kafiyar tsiya kuma sai ta furta da kanta, magana ya fara mata ya ce.
“Yauwa, ni dama magana nake so muyi dake ko nace ina so ne muyi yar wata shawara,kinsan matarka itace abokiyar shawararka hakane?”
“Eh, haka ne, ina jin ka to”
“Yauwa, ina so ne Zaidu ya yi aure kafin mu koma bakin aiki, dan kin ga ance za a karrama mu ne, zan so ace yana da mata shi ma, dan haka ina so ayi aurensa da Hafiza kafin mu koma, amma ke ya kika gani?” gyara zama ta yi ta riƙe hab’a ta ce.
“Maganarka abun dubawa ne, amma kai kana ganin auren nan zai yu kafin ku koma? Yanzu fa saura sati biyu ne kawai, har za ayi shiri kafin ku koma?” murmushi ya yi, ya ce.
“Me zai hana, sati biyu ai da lokaci, da kudinmu fa a hannu, kuma kin ga auren gida ne ba na waje ba, daga yau zamu fara shiri in dai kin bada shawarar ayi, to ki koma gefe kiyi kallo” dariya ta sa ta ce.
“Na bada goyon baya dari bisa dari, na bada shawarar ayi, amma mijina bai ji sauki ba fa?”
“Wa ya gaya miki Mijinki bai ji sauki ba?”
“Au yanzu kai a ganinka ka ji sauki?”
“Ke ba ki yarda da naji sauki ba?”
“Taya zan yarda?” tashi ya yi ya kamo hannunta ya ce.
“Zo muje bedroom dina na gwada miki naji sauki, za ki sha mamakina yau” ba tare da ta fahimci abun da yake nufi ba ta hau binsa, har sunje bakin kofa zasu shiga ta gane me yake nufi da sauri ta fizge hannunta tana dariya ta sa gudu tayi hanyar bedroom dinta har tana riƙe kirji, shi ma dariya ya yi ya ce.
“Ai da kin tsaya na nuna miki yar nema kawai” kaya ya shiga ya canza ya fito ya kwankwasa mata kofa “matsoraciya, fito muje wajan Mama” da sanɗa ta fito su na haɗa ido suka saki murmushi a tare, kafin suka jera izuwa part din Mama, a dakinta suka sameta, nan Ubaidullah ya mata bayanin shawarar da suka yanke, Mama ta yi na’am da hakan, sannan ta ce ya nemi Zaid din su yi magana, yanzu ita ma zata nemi su Umma su yi magana sai asan abun yi, amma yana ganin jikinsa ya warke ne da zai bullo da maganar biki, ya amsata da shi baya jin komai ciwon ne kawai da basu gama hadewa ba, Hafiza dake tsaye kofar Mama ta ji shigowarsu Yayanta tazo ta gaishesu taji su na maganar da ya daga mata hankali, da gudu ta koma dakinta ta sawa kofar key ta dauki pic dinsu ta kifa a kirjinta ta hau rare kuka.
“Anya zan iya kuwa? Zan iya auren wanda ya so auren yar uwata? Kuma har kwanan gobe yake sonta? Anya nayiwa kaina adalci nayiwa yar uwata adalci? Anya idan na yarda na aure sa banci amanar yar uwata ba? Kai inaaa!!! Gaskiya bazan iya auren Yaya Zaidu ba, zanje na sanarwa su Mama ba zan auresa ba” duk maganar zuci take yi tana kuka, har wani ciwon kai ya sauka mata nan bacci mai nauyi ya yi gaba da ita, tare da mafarkin Na’ilah tana ce mata.
“Sismieta!! Yaya Zaidu yana da kirki karki kuskura kice ba za ki auresa ba, idan kika yi haka na yarda baki sona, ki auresa za ki ji dadi zakiyi farin ciki, idan ba ki auresa ba kinci amanata, kuma bamu ni babu ke dan haka kin ga tafiyata!!!” a bacci Hafiza ke mikawa Na’ilah hannu tana “sismieta ki tadawo na amince zan auresa dan Allah karki tafi ki barni” Na’ilah tana b’acewa Hafiza ta farka gami da kwala wa Na’ilah kira da karfi wanda Mama da tazo wucewa zata shiga kitchen ta ji, da sauri ta zo ta hau bugawa Hafiza kofa dan ta tura ta jita a garƙame, da kyar Hafiza ta rarrafa tazo ta budewa Mama kofa, jikinta sai kyarma yake yi gashi duk ta jiƙe da zufa, kuka Hafiza ta saka ta kwanta a jikin Mama tana yi, rarrashinta Mama take yi ba tare da tayi magana ba, dan ta sani har abada Na’ilah ba zata taba fice musu arai ba, Mama ta ce.
“Dama kina daki kina bacci har magriba? Ba dole ki din ga mafarkai ba, idan kinyi mafarkin yar uwarki ki daina mata ihu ki din ga mata addua, yanzu ki tashi ki watsa ruwa kiyi sallar magriba kafin a kira isha’i, anya ma kinyi azahar da la’asar?” ta girgiza alamun aa, “to ki tashi ki yi yanzu ko?” ta amsa da “to” Mama ta fice jikinta a sanyaye dan har an gama maganar bikin Hafiza da Zaid, inda za ayisa nan da kwana goma, ko da Hafiza ta watsa ruwa a daddafe ta yi sallah sabida mugun zazzabin da ya sauko mata, tana kife a wajan akayi isha’i, tana yi ta kwanta ta shige bargo, wajan takwas da rabi ta ji an banko mata kofa ana dariya, ji tayi har da guɗa, cikin zazzabi ta daga ta bude idonta ta kalli su Afnan da Manal da Afrah da Iman, kawayen su Afnan din ne, Afnan ce ta zauna a bakin gadon ta yaye bargon ta ji jikin Hafiza da zafi radauu ta ce.
“Subhanallahi!! Ba ki da lafiya ne? Manal je ki kirawo Mama” da sauri Manal ta fita, Afrah ta ce.
“Tooo daga saka aurenki shine har kin kwanta ciwo?” cikin zafin ciwo da tsananin mamaki Hafiza ta dago tana kallon Afrah ta ce.
“Aure kuma Afrah? Auren wa?”
“Keee! Kina nufin kice bakin an tsaida ranar aurenki yau ba? Nan da kwana goma? Yoo mu fa abun da ya kawo mu kenan mu fara shirye shiryen abun da zamu yi, dan aradun Allah zamu cashe, babu mai faɗa mana muji sai manya” suka sa dariya su na tafawa, yayinda Hafiza ta ji zazzabinta ya ƙaru, da haka Mama ta shigo ta dubata ta ce ko a kaita asibiti ne,amma firrr Hafiza ta ƙi, dan haka aka bata magani, su Afnan suka mata sallama da cewa zasu dawo gobe Allah ya kara sauki, suka fice abun su, su na fita Hafiza ta koma cikin bargo ta ci gaba da rera kukanta, abu goma da ashirin ne suka haɗe mata waje daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button