COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko ba komai yau Ubaidullah an wanke shi da ga zargi, kuma ana jira ya dawo ya maka su a kotu.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Sai dare Ubaidullah ya dawo, part din Mama ya wuce ya sameta zaune a dakinta, nan ya shiga ya zayyano mata komai bai boye mata komai ba, Mama ta ce.

“Duk hukuncin da ka yanke dai-dai ne, amma ina so ka je kayi tunani da kyau, idan zaka koma fyn idan ba zaka koma ba duk daya, Allah dai ya zaba mana abun da yafi alkhairi” ya amsa da ameeen sannan ya mata sallama ya wuce part dinsa Mama murmushi kawai tayi ta bi bayansa da kallo dan tasan har kwanan gobe yana son aikinsa na soja.

Ko da ya shiga yau bai ga abokiyar tawayen tasa ba, kuma shi ma bai bi ta kanta ba, dan yana bukatar hutu da tunani.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da washe gari ma bayan sun gama cakwakiyarsu ya fice dan yau yana so ya je ya dubo shagunarsa ne.

Da yamma ya dawo yana dawowa ta tashi da gudu ta yi bedroom, kuma kayan da take sakawa kenan yanzu guntun wando da yar fingilar riga.

Bai jima da shigowa ba ya sake fita, bayan ya sake fita tana daki ta ji ana zabga mata sallama da gudu ta fito da ta ji muryar mai mata sallamar ba kowa ba ce face Shafa’atu rungume juna suka yi cike da murna kafin Abi’atu ta saketa tana harararta.

“Wallahi Anty baki da kirki inace sai yau kikayi niyyar zuwa inda nake? Wata na nawa da aure?”

“Kai mitau, ai wata ba shekara bane, balle ki sakani a gaba da mita, tun da yanzu nazo ai shi kenan, bikin da ba muyi shiri ba kawai sai ji muka yi anyi wuff da ke” suka kwashe da dariya nan suka hau hiran yaushe gamo, sai dare Safwan yazo ya dauki Shafa’atu ya kai ta gida.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da washe gari misalin karfe goma na safe, Ubaidullah yana shirin fita ya ji, jiniyar motar sojoji na tashi a gate dinsu, abun ba karamin mamaki ya ba shi ba, ba zato ya ga shigowarsu Zaidu da KB kafin nan sai ga Manyan sojoji, da sauri Ubaidullah ya karaso gabansu ya kame yana sara musu dan Ubaidullah yana da ladabi.

Nan ya musu jagora har parlourn Mama, kafin kace me an cike musu gaba da kayan motsa baki Abi’atu da Hafiza.

Bayan an gaisa suka ɗan taba kayayyakin motsa baki aka kawo musu, Mama zata mike nan Major Usman ya dakatar da Mama, sannan suka zayyano wa Mama da Ubaidullah abun dake tafe dasu, sannan suka hau ba wa Ubaidullah hakuri su na masa magiya, ji yayi duk sun dauresa da jijiyoyin jikinsa, harta Mama sai da ta sa baki da kyar Ubaidullah ya ce ya hakura nan ma sai da Zaidu ya saka baki, nan take aka miƙawa Ubaidullah takardan komawa bakin aikinsa tare da bindigarsa da sabbin kakinsa sannan aka ce masa jirgi na jiransa gobe sojoji zasu zo su dauko sa, sun jima a gidan kafin suka je gidansu Zaidu aka gaisa sama-sama dan sun bata lokaci gidan su Ubaidullah dan yau zasu sake komawa Abuja tunda a jirgi ne ba bata lokaci.

Har airport Ubaidullah ya rakasu sannan aka bar masa wasu sojoji wanda zasu daukesa su kaisa airport gobe, rungume juna suka yi shi da abokansa sannan suka daga masa hannu alamum sai sun gan shi a barracks gobe, murmushi kawai ya yi, sai da jirginsu ya daga kafin ya dawo gida ya ba wa sojojin da aka bar masa umarnin su tafi barrack din bauchi gobe idan ya shirya zai neme su,suka amsa cike da girmamawa.

Ba karamin dadi Ubaidullah yaji ba, har sai da ya yi hawaye, Mama da Hafiza Anty Ummu Matarsa Abi’atu da iyayenta da iyayen Zaidu babu wanda bai masa murna ba.

Da dare yana kwance Abi’atu tazo ta same shi ta zauna kusa dashi yau ba kamar kullum ba ,cikin sanyin murya ta ce.
“Hakika nayi farin’ciki da komawar ka aiki Allah ya taimaka ya bada sa’a, Allah ya daɗa daga darajanka” sosai ta din ga kwararo masa addua, wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar shi, har da yi mata murmushi ya amsa da ameen gami da cewa ya gode, murmushin itama ta yi ta tashi ta koma dakinta.

Da washe da safe Abi’atu ta roƙi Ubaidullah tana son komawa aikinta, nan ya amince mata tayi masa godiya, jirginsa karfe uku zai tashi, Abi’atu ta shirya har ta je aiki abun ta.

A safen ranar Hafiza ta fita ta kai sako gidansu Abi’atu wa Ummi.

In da wasu samari mutum bakwai a baƙar mota sun shigo layin sukayi arba da Hafiza tana tafiya ta fito daga gate din gidansu zata koma gidansu Abi’atu Mama ta aiketa, wani daga cikin samarin da suke motar yace.

“Kai Bahba kalli wancan yar flawern”

Wani ya ce.
“Kai daga ganinta zata yi dadi, zata kai yanda ake so” wani ma ya ce.
“Amma fa kamar mun taba operation a wannan gidan fa?”
“Anya kuwa?” cewar wani daga cikin su.
“Eh mana Bahba ka tuna mana , nidai ban manta ba wata yarinya tasa farin less muka sunkuceta a nan kofar gate din, kuma na ga su na kama ko dai yar uwarta ce?”

“To kai Bangis yaushe ka fara tuna yaran da muka farke?” magana suke yi irinta yan iska b’ata gari.

“Nima dai ban sani ba, amma dai nasan na tuna yarinyar.”

“To dai ku bar wannan maganar mu san yanda zamu dauke wannan yarinyar ko yau ko gobe in dai tana fita” haka kuwa suka zauna suka tsara plan.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Karfe sha biyu Abi’ah ta dawo daga aiki, gidansu kuma ta wuce dan an fara shirye shiyen bikin Yayanta, sai karfe biyu da rabi ta koma gida ita da kanta ta hadawa Ubaidullah kaya suka yi sallama, da kuka suka rabu da Hafiza, har Abi’atun ma sai da tayi kuka a boye, ba tare da ya gani ba, shima duk sai ya ji ba dadi, da haka dai ya shiga mota sojoji suka ja shi suka dauki hanyar airport.

Da Ubaidullah ya tafi Abi’atu ma, magana ta yiwa Mama zata je su gaisa da wasu y
Yayun Babanta Mama tace babu damuwa sai ta dawo itama zata shigo anjima.

Abi’atu tana tafiya tayi gidansu ba jimawa Hafiza tacewa Mama itama zata bi Abi’atun gidansu dan gidan ya mata Shuru Mama ta amsa da to Hafiza sai nazo.

Fitowa Hafiza ta yi, dai-dai lokacin da wannan samari su bakwai motar su tasha kwana, nan suka hango Hafiza tana tafiya, da sauri suka fara dan jan motar tasu, itama kuma har ta sha kwana wajan gate din gidansu Abi’atu, daidainan Abi’atu da Safwan suka fito a mota an bude musu gate zasu karbo sako me zasu gani? Wasu kartin maza ne suka finciki Hafiza suka ɗurata a mota ihu Hafiza ke yi tana tirjewa tana neman taimako suka toshe mata baki suka turata a motar da karfi.

Cikin ɗimauta Abi’atu da Safwan suka saki ihu, da mugun gudu Safwan ya take mota ya bi bayansu sannan ya cewa Abi’atu ta kira Ubaidullah idan jirginsu bai tashi ba ya dawo, duba wayarta tayi taga ashe ma bata da lambarsa, ta ce.
“Yaya babu lambarsa anan”
Wayarsa Safwan ya wulla mata ya ce kira shi da nawa, nertwork din wayar Safwan ce ta dauke, da sauri ta dauki lambar a wayar Safwan ta shiga kiransa lokacin har ya fara taka matattakalar bene ya ji wayarsa na ringing ya dubawa ya ga bakuwar lamba ya yi tsaki bai daga ba.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️ Cakwakiya.

Momyn Ahlan taku ce????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

~•~•
Tun daga wannan page din har izuwa karshen wannan book din na ku ne my 5 stars.

My Doter Samira bint Abdallah✨????
Dear Fatima Bintu Sagir✨????
Sisina Farhat Mrs M’J✨????
Antyn Ahlan Princess (Nafeesat)✨????
Habibty احلام فاطمة✨????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button