COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

page°°°°°61&65

Da misalin karfe tara da rabi na safe.

Da sallama ya shiga
dakin, Mama tana zaune akan sallaya da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallarh walha ne.

Amsa sallamar tasa tayi, ta shafa adduar kafin ta fuskancesa dan kuwa kallo ɗaya ta masa ta ga akwai magana shinfiɗe a fuskarsa.

“Lafiya kuwa Yaya Babba? Daga ganin fuskarka akwai damuwa haka ne?”

Gyaɗa kai Ubadullah ya yi, ya matso kusa da Mama ya kama hannunta sosai gabansa sai faduwa yake yi cikin sanyin murya ya ce.

“My Momma, akwai abubuwan da suka faru a wajan aikina, wanda shi ya yi sanadiyyar dawowata gida, ina dawowa dan naji da ciwo ɗaya , sai kuma na iso na tarar da babban miƙin da har na mutu ba zata taba warkewa ba, Mama bansan ya zaki dauki labarin da zan ba ki ba, amma ni dai nasan mahaifiyata ta yarda dani, kuma tasan bazan taba aikata abun da ba shi da kyau ba, Mama ke da bakinki kin sha faɗamin cewa samu da rashi duk na Allah ne, idan Allah yaso zai baka abu sannan ya kwace a duk lokacin da yake so, inajin tsoron faɗa miki amma kuma duk daren ɗaɗewa dole ki sani, ban son ki sake shiga damuwa a ta sanadin hakan mahaifiyata” ya karasa maganar hawaye na zuba a idonsa.

Sosai jikin Mama ya yi sanyi, hakika Ubaidullah wani abun na damunsa amma daurewa yake yi kawai, kallonsa tayi ta ce.
“Yaya Babba, karka ji shakku akan abun da zaka fadamin, a yanzu yadda nake jin kaina, babu abun da za a fadamin wanda zai tayar min da hankali, domin kuwa idan tashin hankaline na gansu sau biyu a gabana, na gansu kwance su biyu a gabana, ba komai bane fa ce gawar mahaifin ku da kuma gawar yar uwar ku, dan haka naga gawar mijina naga na ƴata wanda ko wata ba tayi ba kwance a cikin kasa, ka faɗamin abun da kake son faɗa min.”

Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke kafin ya sun kuyar da kansa kasa ya ce.
“Mama na ajiye aikina na soja, yanzu ni ba ma’aikaci bane” nan Ubaidullah ya shiga bawa Mama labari tun abun da ya fara shiga tsakaninsa da Rumaisa bai boye mata komai ba harda yan matan da suke bibiyarsa a barracks din ,duk ya faɗa mata, daga karshe ya kara da cewa.
“Mama iyakar gaskiya ta na fada miki, na ajiye aikin ne saboda gudun a min wulakanci a ci zarafina, ni kuma ba zan dauka ba, kar nazo nayi abun da zai jawo a kasheni saboda zuciyar da nake dashi, shi yasa na ajiye aikina.

Sosai Mama ta fahimci maganar Ubaidullah, duk da zuciyarta sai ƙuna take yi, a hankali cikin dauriya Mama ta kalli Ubaidullah wanda kallo ɗaya tayi masa ta hango tsananin damuwa da tashin hankali a tattare da shi.

Kasa magana Mama tayi sai da Ubaidullah ya sake cewa.
“Mommana ke ma baki yarda dani bane? Naji baki ce komai ba, wallahi Momma da gaske nake fada miki idan ma baki yarda ba ki kira abokaina Zaidu da KB su zasu faɗa maki gaskiya , da wannan yarinyar da suka zo ta’aziyyar Kanwata.

Share hawaye Mama tayi dan kuwa ba karamin sake shiga damuwa tayi ba , da Ubaidulllah ya fada mata da cewa yabar aiki, a hankali Mama ta ce.

“Allah yana tare da mai gaskiya ni nasan hali ɗana a matsayina ta mahaifiyarsa, kuma na yarda da ɗana, karka damu Ubaidullah dukkan mumini sai Allah ya jarrabesa dan a gwada imaninsa, Allah yabamu ikon tawakkali da rungumar kaddarar’mu hannu biyu” shi ma Ubaidullah hawaye yake yi ya kifa kansa akan cinyar Mama yana kuka tamƙar karamin yaro, zai yi magana suka ji Hafiza na shashsheƙar kuka a bakin kofar Mama.

Ubaidullah ya ce.
“Kanwata!?” da gudu ta bude kofar daki ta shigo da alama taji duk abun da Ubaidullah da Mama suke magana a kai ne, rarrashinta Ubaidullah da Mama suka shiga yi
Amma taƙi tayi shuru, sosai hankalin’su ya tashi, da kyar Hafiza ta taƙaita kukanta , tana jan zuciya ta ce.

“Yaya shi kenan kai ba Soja bane yanzu? Wa in da suka kashe min yar uwata suka barni ina rayuwata ni kadai sun kasheta a banza kenan? Yanzu Yaya ba zaka daukarwa Yar Uwata FANSA ba, yanzu Yaya kai ba soja bane ba zaka nemo wa inda suka kashemin Sismieta suka rabani da ita ka kashe su ba yanzu Yaya b….” bai bari Hafiza ta karasa ba ya rufe mata baki da hannunsa gami da cewa.

“Kul! Wa ya gaya maki cewa bazan nemo su na hukunta su ba?ai kullum cikin neman su nake, Dole na, na nemo wa innan azzaluman bayin na kashe su da hannuna nayi alkawari sai na ɗanɗana musu azabata, duk abun da na koya na training soja sai na sauke musu shi, ki daina wannan maganar kinji ko?” ya karasa yana rungumeta, tashi Mama tayi ta fice tana share hawaye, ta bar Ubaidullah da kanwarsa a daki su na kuka ita ta koma parlour tana nata kukan.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da yamma Ubaidullah ya shirya zai fita, har ya shiga mota dan kuwa ya sanar da Mama cewa zai fita, da gudu Hafiza ta fito ta tsaya tana kallonsa.

Fitowa ya yi a motar yana tambayarta akan menene ko tana son wani abu ne,amma ta tsaya sai tura baki take yi kamar zata yi kuka.

Da sauri ya karaso gabanta ya kama hannunta ya ce.

“Wa ya taba min ke?” dan kuwa Mama da Ubaidullah da Anty Ummu basu son su ga Hafiza a damuwa dan tafi basu tausayi.

“Yaya, ya muka yi da kai?”

Daga kai Ubaidullah ya yi, alamun tunani amma ya kasa tunawa, dan shi gaskiya har ga Allah ya manta da wani magana.

“Am sorry Lil’Sis wace magana ce? Namanta tuna min pls.”

“Na hakurin da zamu je mu bawa Anty Abi’atu mana, tun abun nan da ya hadaku bata sake shigowa ba fa, amma kullum tare muke wuni kuma tana ɗebemin kewar sismieta duk da ba zata taba zama kamar ita ba, amma Yaya ina son Anty Abi’atu sosai, Mama tana sonta idan taji abun da ka mata kasan Mama ba zata ji dadi ba, kuma idan aka yi kwana biyu bata zo ba Mama zata fara zargin kayi mata wani abu ne tun da agabanta ka fara yiwa Anty Abi’atu magana da ihu tun a gidansu Yaya Zaidu” ta karasa maganar tana dukar da kanta kasa.

Ubaidullah yasan duk abun da Hafiza ta faɗa gaskiya ne dan haka ya ce.
“To shi kenan, shiga mota muje” girgiza kai tayi ta ce.

“Yaya, nan da nan shine sai mun je a mota? ni kam kawai ka zo mu taka mu shiga.”

“Ohh Allah na, Hafiza kin koya rigima wallahi, anya ba wannan yarinyar mai iyayin ba ce ta koya maki rigima?” duk a cikin zuciyarsa yake faɗin wannan maganar, a fili kuma ya ce.

“Haba Hafiza baki ga zan fita bane?”

” ni dai Yaya muje da kafa” ba tare da ya sake magana ba ya kulle mota suka fita a tare.

Tun da Hafiza suka fito daga gate dinsu ita da Yayanta ake bin su da kallo, ga kamannin da suke yi wasu yan matan unguwa ma ba su san Ubaidullah ba tun da ba zaman garin yake yi ba idan yazo ya jima da yawa shine ya yi sati ɗaya ya koma, kuma idan ya zo fitar su kullum a mota ne shi da Amininsa Zaidu.

Wasu ma idan suka ga Hafiza sai su dauka Na’ilah ce dan ita ce mai jama’a, sai ka matso kusa tukunna zaka gane ba Na’ilah bace dan kuwa Na’ilah tafi Hafiza fadin Fuska, sai sake yi musu ta’aziyya ake yi su na amsawa, wasu ma yan mata da gayya suka zo yiwa Ubaidullah ta’aziyya dan kawai ya yi musu magana saboda yau ne karo na farko da suka fara ganinsa, basu taba ganinsa ba sai dai su ji labarinsa, ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar ta su, da haka ya ja hannun kanwarsa suka wuce dan sauri yake akwai inda za shi.

A gate din gidansu Abi’atu Hafiza ta kwankwasa karamin kofa, rabonta da fita tun rasuwar yar uwarta, sai kuma fitan da suka yi a mota da Yayanta, shi yasa take ganin komai daban yake mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button