COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka kuwa suka fito, KB ganin yanayin Zaidu yasa shi riƙe Zaidu wanda yake tangali kamar zai ci kasa.

Lokacin da su Zaidu suka iso an gama shirya Na’ila tsaf tana kwance a cikin Makara(gadon mulkin kowa kenan Allah kasa mudace Allah kasa mu gama lafiya) parlour aka fito da ita domin yan uwa da abokan arziƙi su mata addua.

Mama Anty Ummu Hafiza Ummi Umma Inna har da su Manal da Afnan, wanda tsoro ya gama kamasu.

Mama durkushewa tayi a gaban gawar tama rasa wani Addua ne zata fara karantowa, jikinta sai kyarma yake yi, cikin dauriya bakinta na b’ari ta ce.
“ALLAH YA YAFE MIKI NA’ILAH, NA YAFE MIKI DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH YA SADAKI DA ANNABIN RAHMA S,A,W, ALLAH YA SAKA MIKI ƳATA!” daga haka Mama ta nemi maganar dake bakinta ta rasa abu ɗaya zuciyarta ke nanatawa shine kalmar Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!.

Anty Ummu cikin kuka ta yiwa Na’ila Addua tare da kalamai masu ban tausayi da karya zuciyar duk wani mai imani, haka ma su Afnan ba abarsu a baya ba sun yiwa kawarsu addua, su Umma da kowa da kowa anyiwa Na’ila Addua amma banda Hafiza da take bin mutanen wajan ido.

Ubaidullah da su Safwan suka shigo ya duƙa a gaban gawar Na’ila, Hannunsa ya ɗaga sama yana kwararo addua in da a karshe ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, kukan da Ubaidullah ya saka yayi dai-dai da shigowar su Zaidu KB da Zeey.

Turus Zaidu yaja ya tsaya yana kallon jama’ar dake wajan, da karfin ya ce.
“INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN!”
Take Ubaidullah da sauran mutane wajan suka ɗago suna kallon Zaidu.

Da rarrafe Zaidu ya karaso gaban gawar yana binta da kallo kafin ya kalli Amininsa cikin fitar hayyaci ya ce.
“My Man !pls karka ce min Lovely ne kwance anan zuciyata ba zata iya dauka ba, pls Mama Umma ku bani amsa mana, dan Allah ina my lovely take” ya juya yana kallon Hafiza wacce ta kurawa mutane wajan ido tana bin su da kallo tamƙar tab’abb’iya, tun fitowar su bata ce komai ba, dan bata yarda yar uwarta bace kwance a gabanta ba.

“My sister ina lovely take nasan ke ba zaki min karya ba?”

Umma ta ce.
“Zaid ban son shashanci!”

Ummi ta ce.
“A’a bari a buɗe mata fuska su gani”

Nan Ummi da wata mata makwabciyar su Mama suka warware likafanin fuskar Na’ila ya bayyana, Zaidu kusan haukacewa yayi ganin abun bana kare bane yasa su Umma sake rufe fuskar Na’ila sannan suka yiwa mazan dake waje magana azo a dauke ta, ganin haka yasa Hafiza sakin ihu gami da riƙe makaran gam, tana cewa.

“Wayyo Allah na! Wayyo na shiga ukuna! Ina zaku kai min yar uwata! Dan Allah ku ajiye min ita, ba mutuwa tayi ba bacci fa take dan Allah ku ajiye min yar uwata! Wayyo Allah zan mutu, Na’ilata! Wayyo Allah Na’ilata! Yar uwata! Dan Allah karku tafi min da yar uwata! Ina zaku kai min ita mugaye azzalumai! Mama kina gani ko? Yaya zasu tafi min da Yar Uwata! Anty Ummu kice su ajiye min yar uwata!”

Da kyar aka b’anb’ari Hafiza daga gawar Na’ila aka fice, ana fita da gawar Mama ta yanki jiki ta fadi, Anty Ummu itama tayi baya-baya ta zube kasa aka bar Hafiza tana ta kururuwa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Comments

Share

Momyn Ahlan
Taku ce????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

jinjina da dubun gaisuwa gareku masoyana dan Allah ku ce min kun amsa ???????? Alkhairin Allah ya kai muku har garin da kuke har cikin ɗakunar ku, masu cmmnts ina yi muku sonso domin Allah, marasa cmmnts kuma na gaisheku ????????, babbar kyauta ga wa inda suke following dina a wattpad, jinjina gareku masu min cmmnts a wattpad ????????, kar de ku manta da cewa Momyn Ahlan TAKU CE ????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

page°°°°°46&50

Da sauri jama’ar da suke wajen suka yo kan Mama aka hau jijjigata amma shuru, cikin Kuka Ummi ta ce.
“Ina ga fa asibiti zamu kai su, ina Abi’at…” maganar da Ummi bata karasa ba kenan ta ga Abi’atu shame-shame ita ma a kasa, salati Ummi ta saka tana share hawaye, nan dai matan da suke wajan suka taimaka aka ɗaga Mama aka kwantar da ita akan dogon kujera aka cire hijabin dake jikinta aka hau mata fifita ana yayyafa mata ruwa.

Haka ma Anty Ummu da Abi’atu ruwa aka yayyafa musu suka farfaɗo,tukunna aka maida hankali kan Mama sosai ake yayyafa mata ruwa ana mata fifita, amma ina kamar ba a yi mata komai, wata mata ce a cikin yan gaisuwa ta ce.

“Gaskiya ni a nawa shawaran ya kamata ace a kira Likita yazo gida ya dubata, dan gaskiya bai kamata a kaita asibiti ba, hankali ne zai rabu ko ya ku ka ce?”

Umma ta ce.
“Eh haka ne akwai wata kawata Likita ce tana aiki a Rimi Hospital bari na kirata” Umma ta ɗaga waya ta kira kawarta cikin sa’a kuwa ya shiga ta shaida mata cewa zata zo kafin suka yi Sallama.

A daki kuwa Hafiza ta gama haukacewa Inna da wata tsohuwa su ne suketa kokarin lallashin Hafiza amma ina kamar ba da ita suke ba, ihu kawai take yi tana cewa a dawo mata da yar uwarta.

Inna ta kamo fuskarta ta ce.
“Hafiza!HafizaHafiza! Kalleni nan kalli fuskata, ina so na tambayeki ki jini da kyau, kina jina?” ta gyaɗa kai alamun eh tana fizge-fizge.

Inna ta ce.
“Hafiza kin yarda da Allah?” ta gyada kai.

“Kin yarda kullu nafsin za’ikatil maut ne?” ta sake gyaɗa kai.

“Kin yarda da kaddara mai kyau da marar kyau?”
Nan ma sake gyaɗa kai tayi.

Inna ta ce.
“To Hafiza tun da kin yarda da Allah kin yarda da akwai mutuwa kuma kowa zai mutu babu wanda yazo zama a wannan duniyar, kuma kin yarda da kaddara ina so ki daina yiwa yar uwarki kuka kina ihu, itama ba zata so haka ba, ki dinga mata addua Allah ya jikanta da rahma Allah yasa can yafi mata nan kinji? Barin ma Na’ila baki ga yadda tayi jama’a bane, ko ba kiji ance mutanen da suka yi mata sallah sun kai kusan dari da wani abu bane? Ai abun farin cikin mu ne, uwa uba kuma wasu azzalumai ne suka yi sanadiyar barinta duniya kinga kuwa da yardan Allah ita kam ta dace kinji? Ki daina ihu da kukan nan ki tayi mata addua kina yawan fadin kalman Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Kinji Hafiza?”
Ta ce.
“To Inna na bari” shuru tayi na wasu lokaci kafin zuwa anjima da ta ɗaga kanta ta hango hoton su wanda suka yi da Sallah sun rungume Juna su na dariya, nan Hafiza ta sake birkicewa ta sake sakin wani ihun.
“Wayyo Allah Yar Uwata!! Wayyo Na’ilata dan Allah ki dawo!”

Inna hakurinta da dauriyarta ya kare dan haka suka fice tana share hawaye aka kulle Hafiza da su Afnan a daki su na kuka babu mai ce ma dan uwansa yi hakuri.

Parlour wajan karban gaisuwa Inna suka koma suka zauna wata makwabciyar su take tambayar Inna akan cewa Hafizan tayi shuru kuwa, Inna ta ce.

“Ina kuwa , da kamar tayi shuru da muka lallasheta amma tana ganin hotonta da yar uwar ta sake birkicewa” Matar ta girgiza kai gami da cewa.
” Allah Sarki! Dole ta fita hayyacinta, kullum zaki gansu tare, idan makaranta ne ko aiken su aka yi, ko wani waje ne tare zaki gansu, gashi itama Hafizan yarinya ce bata saba da mutuwar ba, tun da ko lokacin da Mahaifinsu ya rasu su na yara ne, Na’ila kuma basu taba rabuwa ba, ko wani garin zasu je indai kwana ne tare suke tafiya, amma lokaci daya mai yanke kauna ta yanke a tsakaninsu dole sai an haɗa mata da rubutu, gashi irin wannan mutuwa na farat ɗaya tafi shiga jiki, Allah na tuba gwanda ace mutum ka ganshi yasha jinya a gabanka,amma ka rabu da yaro lami lafiya adawo maka da gawa, abun akwai tashin hankali gaskiya, Allah dai ya karawa yan uwanta hakuri da juriyar rashinta” aka amsa da Amin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button