COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ubaidullah juyawa ya yi, ya kalli jinin da kafafunsa suka taka ya kalli Safwan kwance babu rai babu alamun rai Abi’atu ta ɗago shi tana kuka mai cike da tashin hankali ta ɗora kansa bisa cinyoyinta ga Hafiza a yashe a kasa itama sumammiya.

Wani kujera Ubaidullah ya ja tsakiya sannan ya dauki Hafiza ya shinfiɗeta a gefe, ya ɗaga Abi’atu wacce take durkushe da Yayanta wanda ta kifa kansa saman cinyoyinta ya miƙar da ita tsaye riƙe kafadunta, sannan yasa hannu ɗauki Safwan tamkar ba namiji ya ɗauka ba, ganin yadda ya dauki Safwan abun ya sake firgita su matuƙa, kwantar da Safwan ya yi a gefe shi ma, sannan ya dauki wayar Abi’atu wacce ta sakesa ya faɗi ya jawo hannunta, damƙa mata wayar ya yi, ya sa hannunsa yana goge mata hawaye cikin murya wanda Abi’atu bata taba jin Ubaidullah da shi ba, bata taba tsammanin yana da ita ba, wanda da ya yi mata magana da shi itama sai da ta ji tsoron murya, wai a hakan ma ita ya sassauta mata.
“Abi’ah just give me 10mins only, zamu kai Safwan Asibiti In sha Allah babu abun da zai faru da shi” ta jinjina masa kai ta sake ɗaga Safwan ta ɗorasa a saman kafarta, tana tare jinin dake malala daga kansa da mayafinta, duk mayafin nata ya b’aci da jini.

Kujerar da Ubaidullah ya ja tsakiyar wajan zama ya yi a kai ya duƙar da kansa kasa, kafin ya ɗago jan idonsa yana kallonsu da shi, jira yake yi wa inda suka fita su dawo, bai jima da zama ba kuwa sai gasu sun shigo su na ganin Ubaidullah suka firgita, ɗaya daga cikin wa inda suka shigon ne ya ce.
“Wanene kuma wann…..” maganar da bai samu damar karasawa ba kenan sakamakon haɗa ido da ya yi da Soja Namijin Duniya Ubaidullah! juya idon da Ubaidullah ya yi ya hango wata igiya kakkaura, duba agogon hannunsa ya yi ya ga har yaja mintuna hudu a cikin goman da ya ambata, yana tashi idonsa a rufe da ya yi wani kukan kura ya shaƙi wuyar yan iska ya dinga gwara su da bango, ji yake yi ma gabaki ɗaya baya hucewa, dan ya rasa kalar dukan da zai yi musu, ta ko ina ya shiga kai musu zafafan naushi, suka fara ihu su na neman agaji igiyar da ya gani ya ɗauka ya hadasu waje guda ya ɗauresu tamƙar yadda ake daura bayi marasa galihu da yanci a zamanin da can baya, haka ya ɗaure su ƙwaƙƙwaran motsi basu iyawa dan kuwa ɗauri ba na wasa Ubaidullah ya musu ba, ya juya ya ga su koken da sauran wasu kayan maye, ɗaukar koken din ya yi ya tura musu a hanci da baki ya ɗaure musu bakin tamkar yadda suke ɗaure na ƴaƴan mutane, sannan ya tattara komai nasu a kangon ya ajiye gefe daya, ajiya mai kyau ya musu, da sauri ya ɗaga Safwan ya fita da shi ya saka shi a mota sannan ya dawo ya tattara wayar Safwan din ya dauki Hafiza ya fice da ita da gudu Abi’atu tana binsa a baya, ya sa Hafiza a mota itama, gudu yake shararawa sosai yayinda ya dauki hanyar Specialist Hospital, yana zuwa emergency ya bukaci a shiga da Safwan amma suka ce ba zasu karbesa ba sai yan sanda sun zo sun sa hannu Ubaidullah ya sa hannu a aljihun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya nuna musu card dinsa ya ce.
“I’m Captain Ubaidullah Abdullahi Nigerian Army, wannan kuma Ɗan Uwana ne ya samu hatsari da miyagu ne” nan kuwa suka karbi Safwan suka ce Ubaidullah din yasa hannu ya saka, sai da aka shiga da shi emergency sannan ya miƙa Hafiza ma wata Dr mace, ya ce.
“Pls Dr ki bincika min ita sosai idan babu abun da aka mata” Dr ta amsa da “ok sir”, kafin Ubaidullah ya hau jeka ka dawo ya kasa zaune ya kasa tsaye wai ga wa ya yi bai ga Abi’atu ba, da sauri ya fita yana nemanta yana kiran sunanta a hankali, can wajan bayan asibiti ta zauna ta haɗe kai da guiwa tana rusar kuka dan gani take yi kawai ta rasa Yayanta dan bai yi kama da rayayye ba.

Ba karami sanyi jikin Ubaidullah ya yi ba, ganin yadda Abi’atu ke dirzan kuka, tabbas Abi’atu masoyiyarsa ce ta hakika, dan duk abun da ya samu Safwan ta sanadin ceton kanwarsa ce, shi kuwa me zai yi wanda zai saka ma wa innan bayin Allah masu matukar mutunci da karamci gami da halacci da kyautatawa? Wani tausayin Abi’atu ne ya kama shi da fargaba yana addua Allah yasa Safwan na raye, dan kuwa har ya fara hango kalar tashin hankalin dasu Abba da Ummi zasu shiga, da sanyin jiki ya karaso yasa hannunsa ya kamo kafaɗunta, jikinsa a matuƙar sanyaye ya ɗagota, still kukan da ta ke yi ta kasa dainawa, fuskarta ya tallabo da hannunsa biyu hawayenta na zuba a tafin hannunsa, ji yake tamkar shima ya sa kukan suyi tare amma idan ya yi haka abu ya b’aci, cikin murya mai cike da taushi gami da lallashi ya ambaci sunanta, dan ba zai iya jurar kukan da take yi ba.
“ABI’AH!” yana kiran sunan nata ta ji kukan nata ya ƙaru, sake ɗago fuskarta ya yi, ya sake ambatar sunan nata kafin ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta sake fashewa da sabon kuka dan kuwa ta kasa daina kukan, ga uban faduwar gaba, kuka take har tana shiɗewa ga shi yanzu ta kafesa da ido sabida fuskarta da ya tallabo da ambatar sunanta da ya yi, Ubaidullah idanunsa suka sake rinewa ganin yadda take kukan tana karawa, a hankali ya jawota ya haɗeta da kirjinsa yasa hannuwansa duka ya zagayeta da shi gabansa na faduwa, jinta a jikinsa yasa sautin kukanta sake canza kala, dan kuka take mai cike da ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, da kyar ta fara magana mai cike da ajiyar zuciya da shesheƙa.
“Shi ke nan! Zan rasa Yayana, mutuwa zai yi shi ma ko? Zan ras…..” da sauri ya sake matse fuskarta a ƙirjinsa sai ga hawaye na zubowa daga idon Ubaidullah kuma ya ƙi yarda ya ɗago da fuskarta, sosai Abi’atu tasha kuka lokaci ɗaya wani azabebben ciwon kai ya dirar mata, sai da ya tabbatar ta yi shuru kafin yana rungume da ita suka koma cikin asibitin.

     @@@@@

Sai wajan gaf da magriba Likitar da Ubaidullah ya sakata bincika masa lafiyar Hafiza ta fito, da sauri Ubaidullah ya yi wajanta yana tambayarta ya lafiyar Hafiza, nan take shaida masa lafiyarta kalau basu yi bata komai ba, wani wahalalliyar
Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke, ya juya ya sake rungume Abi’atu wanda idanuwanta suka ƙanƙance sabida kuka da ciwon kai.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A dayan bangaren kuwa.

Ko da Mama ta zo gidansu Ummi take cewa ina Abi’atu da Hafiza, Ummi take cewa ita bata ga Hafiza ba, amma ba mamaki da zata zo sun hadu dasu Safwan da Abi’atu a gate sun fita tare, dan Safwan da Abi’atu sun tafi karb’o sako, da haka ne suka shiririce da zancan, har can yamma lilis ba Safwan ba Abi’atu balle a saka ran gani Hafiza tana tare dasu, abun bai damu Ummi ba, sai ana kusan sallar magriba tukunna wanda za a karba sako a hannunsa ya kira waya ya ce fa ga shi ba a zo an karbi sako ba, Ummi ta fara mita tana yiwa Safwan faɗa sai kace yana gabanta, har tana cewa, ya kama sun tafi da Abi’atu da shike itama mai kafar yawo ce da auranta sai da nace mata zauna ta ƙi, waya Ummi ta ɗauka ta fara kiran layin Safwan a lokacin ita kuma Mama ta koma gida ta ce gidan ba kowa sai mai gadi idan su Abi’atu da Hafizan sun dawo sa sameta a gida, lokacin da kiran Ummi ya shigo wayar tana aljihun wandon Ubaidullah yana zaune Abi’atu tana kwance a kafadarsa, ɗan ɗagata ya yi kaɗan, sannan ya duba wayar ya ga sunan Ummi na yawo a screen din, gabansa ne ya fadi dan baya so ya kirasu ya gaya musu halin da ake ciki sai likitoci sun fito an faɗi a wani mataki Safwan yake, babu yanda Ubaidullah ya iya haka ya ɗaga wayar Ummi jikinsa a matuƙar sanyaye, tun kafin Ubaidullah ya yi magana Ummi ta ri ga sa da cewa.
“Haba Safwan! Wani irin rashin hankaline haka!? Tun wajan karfe uku saura ku ka fita amma har yanzu baku dawo ba fisabilillah!? Kuma kasan Abi’atu matar aurece yanzu ko!? Ba kamar da ba ce, wai ma tukunna ba ku je kun amso min sako ba, sannan ku baku dawo gida ba, ina ku ka biya ne kam? Hafiza tana tare da ku ne!? Dan Mama ta zo nace mata banga Hafiza ba, amma watakila kun hadu da ita a gate ku ka tafi tare” duk a lokaci daya Ummi ta jero magana da tambaya, jin shuru ba amsa ne ya sata kara faɗin.
“Hlo Safwan ba ka ji nane?”
“Ummi mu na asibiti!” cewar Ubaidullah muryarsa kamar zai sa kuka, jin muryan Ubaidullah yasa gaban Ummi bugawa da karfi,a kiɗime ta ce.
“UBAIDULLAH!? meya faru!? Baka tafin bane!? Waye kuma a asibiti!?” shuru Ubaidullah ya yi ya kasa ba wa Ummi amsa, ya kalli ido Abi’atu wacce take shirin sake saka masa kuka, girgiza mata kai ya yi alamun kar ta yi sannan ya sake kifa kanta a gefen kirjinsa, da kyar Ubaidullah ya ce.
“Ummi, ku taho Specialist Hospital yanzu pls da Abba da Mama” yana gama faɗi ya ajiye wayar, a kiɗime Ummi ta hau neman layin Abba Allah ya so bugu biyu ya daga nan ta shaida masa Ubaidullah ya ce yanzun nan su taho
Specialist Hospital, shi ma Abba a zabure ya ce dama Ubaidullah din bai koma aikin bane, waye ba lafiya, Ummi tace itama bata sani ba, Abba yace dama yana kusa da gida ga shi nan zuwa, Ummi ta ce ya dauke su kawai ita da Mama a bakin gate din gidansu Ubaidullah din, Abba ya amsa da to, ko da Ummi ta yi Mama magana hankalin Mama ya tashi in da take cewa dazu da ta shigo gida Zaidu ya kirata akan ina Ubaidullah ta ce masa tun karfe biyu da yan mintoci yabar gida ya tafi airport yake ce mata yana ta kiransa baya dagawa, Mama tace masa, ba mamaki yana jirgi da haka suka yi sallama da Zaidu, yanzu kuma ance ana asibiti to waye ba lafiya? nan dai cike da zullumi suka fito gate suka tsaya su na tunanin waye ba lafiya da har su ka je asibiti, sannan ya akayi Ubaidullah shi da ya kama hanyar airport ya bige da zuwa asibiti, to ma ya akayi suka hadu dasu Safwan har wayar Safwan ta shiga hannun Ubaidullah? Wannan shi ne tambayoyin da Ummi da Mama da Abba suke yiwa Zuciyoyinsa amma babu mai basu amsa sai sun isa asibitin, basu fi minti bakwai da fitowa ba Abba ya iso nan suka burma motar su na jimamin meya faru, a cikin da kankanin lokaci suka iso asibiti Abba ya kira wayar Safwan dan ya kira na Ubaidullah bai daga ba, nan Ubaidullah ya ɗaga ya gaya musu inda suke gami da yi musu kwatance, tafiya sukeyi da sauri-sauri kamar zasu tashi sama, su na shigowa suka hango Ubaidullah da Abi’atu, ga jikinsu duk jini da sauri Abba ya karaso yana kiran sunayensu Abi’atu tana kallon Ummi ta sake barkewa da kuka ta tashi da gudu ta rungume Ummi, sosai jikin Ummi ta yi sanyi, kallon Ubaidullah Mama ta yi wanda ya dukar da kansa kasa, Mama ta ce.
“Ubaidullah meya faru!? Hatsari aka yi ne!? Ina Safwan da Hafiza!? Wai meke faruwa ne!?” Abba ya kama Ubaidullah ya ce.
“Mama kiyi masa tambaya a hankali, Ubaidullah meya faru, karka ji komai faɗa mana?” ganin Ubaidullah ya kasa magana yasa Mama dago Abi’atu daga jikin Ummi ta ce.
“Abi’atu meya faru!? Hatsari ku ka yi ne? Ina Safwan!? Kun fita da Hafiza!?” cikin sheshsheƙar kuka Abi’atu ta gya ɗa kai ta fara basu labari da dasheshshiyar muryarta wacce tasha kuka ta godewa Allah, tana gaba basu labari Ummi ta yi baya-baya zata faɗi da sauri Abba ya tarota ya yinda Mama ta zube kasa sharab irin zaman yan bori sabida tsananin tashin hankali, Abba ya kalli Ubaidullah ya ce.
“Yanzu ina Hafizan!?” da kyar Ubaidullah ya ce.
“Tana ciki, likita ta ce basu yi mata komai ba”
“Safwan din fa!!!!? Cewar Mama da jikinta ya ɗauki b’ari, a sanyaye Ubaidullah ya ce.
“Tun da suka shiga da shi har yanzu basu fito ba, balle mu ji ya yana yin jikinsan yake” Abba ya ce.
“To su yan iskan su na ina!? Ba dai barinsu ka yi ba!?” murmushin baƙin ciki Ubaidullah ya yi ya ce.
“Abba taya zan barsu!? Mutanen da na dauki tsawon lokaci ina nemansu RUWA A JALLO sunyi sanadiyyar mutuwar kanwata, abun bai ishesu ba, sun sake zuwa suka dauke dayar, ga shi yanzu a garin taimakonta ga Ɗan Uwana yana cikin emergency ban san a wani hali yake ba, taya zan barsu Abba!? Su na can na daure su, so nake na san halin da Ɗan Uwana yake ciki kafin na koma garesu” Abba ya yi ajiyar zuciya gami da cewa.
“Bari na kira Police” ya fada yana kokarin kiran waya, da saurin Ubaidullah ya rikosa ya ce.
“Abba wani police kuma zaka nema bayan ga Soldier a gabanka? Mai mukamin Captain? Ba bukatar police Abba, nine nan zan hukuntasu da kakina, na godewa Allah da aikina ya dawo ababen farauta ne suka bayyana, sai na dandana musu azaba kafin na kashesu!!!!” ya faɗa bakinsa na hayaki,jinjina kai Abba ya yi, babu wanda ya sake magana a cikinsu illa fargaban da suke ciki, nan suka koma suka tsaya cirko-cirko, kafin likita ta fito ta ce Hafiza ta farka, su na shiga suka sameta tana kuka tana shirin wafce drip din da aka ɗora mata tana ambatar sunan Yaya Safwan, Abba ne ya dakatar da ita akan cewa karta cire Safwan yana lafiya, kallon Abi’atu ta yi wacce itama ke layi sabida matsanacin kanta dake mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, Hafiza ta ambaci sunanta, Abi’atu ta zo ta rungumeta su na kuka tare abun tausayi, matukar tashin hankalin haƙiƙa hankalinsu a tashe yake, sai wajan karfe sha ɗaya kafin wasu Doctors su biyu ne suka fito su na sharce gumi, da sauri Ubaidullah ya tare su yana tambayar jikin Safwan, ganin yadda hankalinsa yake tashe ne suka dafasa sannan suka ce shi da Abba su biyo su office, hakan kuwa aka yi, ko da Abba da Ubaidullah suka zauna Dr ya ce.
“Alhamdulillah! Aiki muka yi masa but mun sha wahala sosai, sabida da kyar jinin da ke zuba ya tsaya, dan bayan wajan ƙeyar kusa da wujan wuyarsa gurin ne
Ya fashe dan kuwa abun da aka buga masa mai karfi ne gaskiya, saukinta ma bata wajan kwakwalwarsa bane da ya mutu ko ya samu tabin hankali, a gaskiya ya zubar da jini sosai, yanzu jini muke bukata dan da kyar muka samu muka tsaida jinin kafin muka yi masa aiki” da sauri Ubaidullah ya mika hannunsa yana cewa.
“Dr ku auna nawa idan zai masa ku ɗiba a saka masa!” murmushi Dr ya yi ya ce.
“Ka kwantar da hankalinka, Nan da 2days Dan Uwanka zai iya farkawa da zarar mun saka masa jini, dan mun ga ka damu sosai In sha Allah he will be fyn very soon” gauron ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke yana hamdala, nan aka auna jinin Ubaidullah amma bai zo dai-dai dana Safwan ba, dan haka Abba ya ce a dibi nasa, nan kuwa aka ɗibi na Abba aka jonewa Safwan, ranar babu wanda ya rintse haka suka tsaya a asibitin, kuma likitoci sun hanasu ganin Safwan din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button