COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

General ganin fa idan ba da gaske akayi ba wajan tare Ubaidullah idan ya kama Rumaisa to sai dai wata amma ba ita ba, da sauri General da Major suka riƙo Ubaidulllah ta baya, har Ubaidullah ya juyo zai kai duka sukayi ido hudu da General Of The Army nan ya sauke hannunsa da sauri sannan ya sara masa,jikinsa sai b’ari yake yi jijiyoyin jikinsa sun sake fitowa raɗa-raɗa, cikin tsananin bacin rai General Of The Army ya ce.
“Aje a kulle Ubaidullah a saka shi a guardroom” da sauri Hanan ta ce.
“No pls Daddy kar a a saka shi a guardroom sai kace wanda yayi sata ko yayi wani babban laifi, daddy da muƙamin shi da komai dinshi a saka shi a guardroom?”

Tsawa General Of The Army ya dagawa ƴarsa wanda ya sakata firgita har sai da taja da baya tana zare ido, Major ya ce.
” Captain Ubaidullah yayi babban kuskure na dukan da yayiwa Sojoji dan bai kamata ace ya dakesu ba, dan ya fisu muƙami,sannan ba a yarda da maganar da Rumaisa ta faɗa ba sai da ta gabatar mana da hujjar wani video recording wanda suke mu’amala tare, dan haka a tafi dashi” da karfi Raihana da wata yarinya christen mai suna Doratie suka mike gami da cewa.
“Na lie! Ubaidullah he can’t do this” amma babu wanda ya saurare su, Zeey kuwa mikewa tayi idonta jajur ta bar wajan, tashin hankalin da Zaidu da KB suka shiga kuwa bazai misaltu ba, dan suman tsaye suka yi,duk wannan budirin sun kasa yin katabus,
Sai da suka ji General yana umarta kama Ubaidullah a tafi dashi guardroom tukunna suka fara roƙon General amma ina bai saurare su ba, sojojin da zasu kama Ubaidullah cikin tsoro da shakkarsa suka kamasa, dan Ogansu ne, uwa uba kuma mai karfi ne,dan su na jin tsoro karya zubar dasu ya ja musu kwanciyar asibiti.

Rumaisa hankalinta ne ya tashi dan ita ba haka ta so ba, taso ace General dasu Major su bawa Ubaidullah Umarnin ya aureta ne, amma bawai a kullesa ba, tunani ta shiga yi, yanzu ya za tayi,Da sauri ta miƙe tabar filin wajan ta dauki wani hanya,tana tafiya hankalinta baya gabanta, batayi auni ba ta ji saukar naushi a bayanta take ta faɗi kasa, dagowar da zatayi taga Zeey tsaye a saman kanta fuskarta tayi ja.

Cikin zafin rai Rumaisa ta miƙe zata rama naushin da Zeey ta mata, dan dama sun saba in dai dambatuwa ne,ta kaiwa Zeey naushi Zeey ta riƙe hannunta ta murɗeshi ta baya ta shaƙo wuyanta, ta fara magana cikin bacin rai, da tsawa.

“Makaryaciya! ashe son da kike ikirari kina masa duk karya ne! Wallahi Rumaisa baki son Captain tun da har zaki iya zubar masa da mutunci a filin jama’ar da sun kai Fiye da dubu, Rumaisa karya kike kice son shi kike,tun da gashi kinci zarafinsa kinsa an kullesa a guardroom”

“Rumaisa me Captain ya miki da zaki saka masa da ƙazafin ZINA? Haba Rumaisa! Haba Rumaisa! Wallahi ko rantsuwa dubu zanyi idan na karyata ki ba zanyi kaffara ba,saboda nasan halin Captain kema kuma kinsan halinsa, Rumaisa idan ma karya kike akan cewa kina da ciki alhalin babu, to saina miki la’anannan duka ta yanda sai ciki ya shiga jikinki, idan kuma akwaita na wani dan iskan ne a cikin barracks din nan kikeso ki liƙawa Captain to sai na miki kafurin duka ta yanda sai kin haifi cikin nan baki shirya ba”

Nan Zeey ta rufe Rumaisa da ƙazamin duka dan ranta yayi mugun baci, tana cikin jibgarta kenan sai ga Hanan yar gidan General Of The Army da Doratie da Raihana, su ma sun biyo bayan Rumaisa su lakaɗa mata duka ne, amma me nan suka ci karo da Zeey dake jibgar Rumaisa kamar zata kasheta dan Zeey mugun karfi gareta, dan harta mazan barracks wasu shakkar Zeey suke saboda ba ƙaramin abu ne a wajanta duk dan iskan da ya taƙaleta ta nuƙuskushesa, ta ƙara gaba abunta.

Hanan ganin Zeey tana shirin kai Rumaisa lahira nan suka shiga kokuwar kwatar Rumaisa daga hannun Zeey, da kyar da suɗin goshi suka kwaceta amma kafin nan sai da su ma sukaci duka.

Gefe Zeey ta koma tana huci, yatsar hannunta manuniya ta nuna Rumaisa dashi gami da cewa.
“Wallahi!Wallahi!Wallahi! Rumaisa kinji na miki rantsuwa uku ko, idan har baki je kin warware kullin da kika yiwa Captain ba, sai na miki LAHANI sai na miki ILLA sai dai duk abun da zai faru ya faru” tana gama faɗi tayi gaba kamar zata tashi sama.

Cirko-cirko su Hanan suka Tsaya su na kallon juna, ga Rumaisa kwance a kasa tana sauke numfashi da kyar, Doratie ce ta kalli Rumaisa cikin hausarta da bata iya sosai ba ta ce.
“Shame! Kinji kunya! Rumaisa, kince kina son Captain Ubaidullah for what reason zaki masa sharri? Sanin kowa ne a barracks din nan Captain Ubaidullah baya kula mata, infact har mazan ma baya shiga Hidimar su amma zaki masa wannan sharri! Walahi kinci sa’a amma kinga zugan mun nan, dama mun zo ne mu lallasaki sai kuma muka samu maiyi da gaske ta tumurmusheki, dan haka ki kiyayi gaba.

   **********

Da sauri KB da Zaidu suka bi General su na magayi, amma ya dakatar dasu, dan shima ya shiga cikin zullumi.

Haka suka juya ba dan sun so ba, wajan Major suka je Zaidu ya ce.
“Sir a duba lamarin Ubaidullah na miskilanci da rashin magana da kula mutane, ta ya wani mu’amala zai shiga tsakanin su da Rumaisa har ya mata ciki? Sir, idan mafaɗin magana wawa ne ai majiyinta mai hankali ne, pls Sir a duba lamarin” Zaidu ya karasa maganar kamar zaiyi kuka saboda tashin hankali.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da babu gwara ba dadi ko my ppls?????

COMMENTE

AND

SHARE

BY

MOMYN AHLAN✍????
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

HAHAHA MASHA ALLAHU, IDAN KAJI WANE KO WANCE BA BANZA BA, KUNA INA MASOYAN KUNGIYAR NAN ƊAYA TAMƘAR DA DUBU, WATO KAINUWA WRITERS ASSOCIATION? WANDA SUKA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI DAƊA ƊA, MAZA MAZA KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU, A YAU KUNGIYAR TAYI SURFE DA DAKA, TA TANKAƊE TA RAIRAYE, TA REGE TA BUSHAR, TA ZAƘULO MUKU JIGA-JIGAI HAZIƘAI NAGARTATTU MASHAHURAI,BASIRARRU, A YAYINDA ZASU GWANGWAJE KU DA FASAHAR SU, DAMA SUN SABA ILMANTAR DAKU NISHAƊANTAR DA KU GAMI DA FAƊAKAR DAKU, KU DAI KU KASANCE DA WAINNAN FASIHAN MARUBUTAN GUDA BAKWAI DUK A CIKIN LITATTAFANSU MAI TAKEN SUNA ( ????ℍ????ℍ????ℝ????ℝℝ???? ???????????????????????? ) AKAN FARASHI MAI SAUKI DA RAHUSA #500 KACAL YAN UWA, KU DAI KARKU BARI A BARKU A BAYA, NI UWAR AHLAN INA GAYA MUKU NE DAN KU HANZARTO KU GARZAYO, KU NEMI NAKU, KU SHA KARATU, A ISO LAFIA.

????????????????????????????????????????

page°°°°°31&36

Major ya ce.
“Ok Captain Zaidu kuje zanyi magana da General Of The Army idan yaso a tara meeting sai asan abunyi” Zaidu ya ce.
“Tnk u Sir Allah ya kara girma, but pls kar abar Captain Ubaidullah ya kwana a guardroom “ya karasa maganar cikin roƙo da kasa da murya gamj da kwantar da kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button