COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Na’ila ta kuma cewa.
“Yaya idan ma duka ne na yarda ka sake min in dai zaka huce ka daina fushi, kwata-kwata wannan zuwan kan Yaya baka kulamu ba, Yaya nasan nice na jawo saboda bana jin magana, Yaya ka dakeni ka huce amma ka daina fushi kayi hakuri” ta faɗa ta hau wanke fuskarta da mari.

Da sauri Ubaidullah ya rike hannunta,sannan ya rungumesu idonsa har sun kaɗa sunyi ja.

A hankali ya ce.
“Is ok, but karki sake, muje na ga abincin da my flowers sister’s dina suka min” ya fada yana smiling.

Sosai suka ji dadi.

Har parlour suka jera yana riƙe da hannun su, Mama tana ganinsu ta girgiza kai ba tare da ta kulasu ba.

Nan ya zauna ya fara ci su na hira kamar ba shi ba,yana santin abinci ya ce.

“Yanzu ku, ku ka girki wannan abinci mai dadi haka?”

Su na dariya cike da jin dadi suka amsa da eh, dan ba karamin dadi suka ji ba ganin Yayansu ya hakura.

Ko da ya gama cin abinci ya kwashesu suka yiwa Mama magana sun fita Mama ta ce, a dawo lafiya.

Gidan Anty Ummu yaje ya dauki Haidar da Sakina, sannan yaje gidan su Zaidu ya dauki Afnan da Manal da Nawaz (ƙannen Zaidu) yawo suka fita ya musu siyayya sannan suka koma gidan Anty Ummu, sai dare suka koma gida.

Da daddare suka gama shirin su dan gobe da safe zasu koma Abuja dan har General Of The Army yayi kira a waya.

   ~~~~~~~

Ina mai baku hakuri, kuma ku kara hakuri na rashin samun posting akan tym

Zazzabi ne ta sakoni gaba wallahi

COMMENTS
&
SHARE

BY MRS IS OK MOMYN AHLAN✍????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????


Kawata @⁨Nana Aisha⁩
Tawan @⁨Maman Twins⁩
My luv @⁨Khadija Jounalist⁩
Inayinku over Allah yabar ƙauna.

Dole na fara sa koku masoyan asali,

Doter @⁨Surayyah Dan Ango⁩
Antyn Ahlan @⁨6 Naphersarh⁩
Habibty @⁨احلم فطمة⁩
@⁨Samira Bint Abdallah????????⁩
@⁨Maryam Mrs M Lawal⁩
Doter @⁨Doter Fareesat⁩
Dear @⁨Fatima Bintu Sagir⁩
@⁨????‍⚕Dr,Herpsert????‍⚕⁩
@⁨Mrs M,j (Fans)⁩
@⁨Mrs Faruq????⁩
@⁨MAMAN ZAHRA⁩
@⁨Mummy jidda⁩
@⁨Maman Basma⁩
@⁨Aisha Ibrahim Ummi????⁩
@⁨Firdausi Hussain Namad????????⁩

~IYAKAR WA INDA NA GANI KENAN~

WANNAN PAGE DIN TAKU CE MY PPLS

~KO BA WUYA ANA TSABTAR TARE~????


Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

________________________

page°°°°17&18

Washe gari da safe suka shirya tsaf cikin kakin su na sojoji, sosai suka yi ɗamara, yayinda kakin ya karb’esu, barin ma Ubaidullah yayi masa kyau sai kace a jikinsa aka halicci kakin.

Fitowa suka yi a tare da Mama, da Anty Ummu, Hafiza,Na’ila.

Ubaidullah yana tsakiyar su, Mama da Anty Ummu su na ta kwararo masa addua, sai amsawa yake yi da amin, yana so ya mai dasu barracks amma Mama ba zata yarda ta koma Abuja ba, duk ma ba wannan ba,da kunya ya ɗauki Mama ya kaita barracks saboda kajinan da suke bibiyar rayuwarsa ,ko wacce take kawo masa hari.

Su na isowa bakin mota Zaidu ya fito ya duƙa ya gaishe da Mama ta amsa, sannan ya gaishe da Anty Ummu ta amsa tana dariya, su Hafiza da Na’ila suka gaishesa ya amsa, Anty Ummu ta ce.

“To surkina dan Allah a kula sosai, Allah ya kaiku lafiya Allah yabaku sa’a a tafiyar da zaku yi, Allah ya ɗaura ku akan maƙiya tare da mahassada”

“Amin ya Rabbi Allah, Big Anty mun gode da wannan adduar taki Allah ya saka da Alkairi”

Anty Ummu tayi murmushi ta ce. “Ba komai ƙannena a kula dai da kyau dan Allah”

Zaidu ya ce.
“In sha Allah Big Anty zamu kula”

Kallon su Mama tayi a lokacin da suka iso gaban mota ta ce.

“Duk abun da ya kamata ace Uwa tana gayawa ɗanta a lokacin da zai fita neman halak dinsa Ubaidullahi ban rage ko guda daga ciki ba, na faɗa maka yanzu ma kuma zan ƙara nanata maka wasu daga cikin kalaman masu hatsirin gaske, Ubaidullah Zaidullah?” Mama ta kira sunan su a tare, suka amsa kansu duƙe su na kallon ƙasa.

“Zan ƙara yi muku tuni akan cewa ku gujewa haram, karku yi tunani da cewa ai kadan ce sam Allah ba ruwansa da wannan ,kuna samun rufin asirinku dai-dai gwargwado, na tabbata da ace baku riƙe gaskiya ba, da ba zaku taka matsayin da kuke dashi a yanzu ba, dan haka ku guji abun haram karku fito a cikin hadisin Manzon Allah sallallahu alayhi wa’sallam da yake cewa ( لايدخل اجانةجسدغذي بااحارام)
Wato dukkan gangar jikin da aka ginasa da haramun bazai shiga Aljanna ba, amma abun da zai baku mamaki a wannan zamanin da muke ciki bamu dauki haram a bakin komai ba,mun maida haram abincin mu, ruwan shan mu, gadon baccin mu, wajan zaman mu,komai namu, gabaki daya shagalar tai mana yawa, mun bar koyarwar Allah da Manzon S,A,W, mun bar hadisai mun bi ruɗin duniya da son zuciya da kyale-kyalen banza, wanda zata kai mu ga halaka, jin dadi duniya ƙadan ne wato (ADDUNYA MATA’UN ƘALILAN) dan haka Ubaidullah Zaidullah kuji tsoron Allah a duk in da ku ka kasance, karku biyewa neman mata kamar yadda aka yiwa sojoji ittifaƙin neman matan banza, ku ɗauke idanun ku ,ku yiwa idonku hijabi wajan kallon haram, abin da nake nufi shine abun da bai zama halaliyarku ba, idan kuma aure ne ga mata a gari da yaran yan uwa da abokan arziƙi, sai ku duba a ciki mu sha biki, maganganun basu kare ba, amma karna saka ku makara kuje Allah ya kaiku lafiya Allah yaba da sa’a Allah ya ƙare ku, gabanku da bayanku dama da hagunku, Allah yasa kuje aikin da aka tura ku lafiya ku dawo lafiya tare da manyan nasarori, Allah ya muku Albarka gaba’ɗayan ku”

Sosai jikinsu ya sake yin sanyi duk da sun saba da nasihan iyayen nasu, amsawa su Ubaidullah suka yi da amin, sannan suka ƙara da cewa.
“In sha Allah zamu kiyaye Mama, mun gade Allah ya ƙara girma da nisan kwana”

Mama ta amsa da amin tana murmushin karfin hali dan hawaye ne ya cika tam a idonta, juyawa tayi zata koma cikin gida, ta ji muryan Ubaidullah, “MAMA”
ya kira sunanta, tsak Mama ta tsaye amma bata juyo ba.

Takowa Ubaidullah yayi yazo gabanta sannan ya rungumeta idonsa yayi ja sosai,baya so ya kashe mata jiki gashi dama tana fama da hawan jini so yake ya ce mata, ta yafesa idan har yayi mata wani laifi amma yaga alamunta ma hawaye take son yi dan haka ya canza akalar maganar ta hanyar cewa.

“I gonna miss Mama”

Nan ma murmushi tayi ta shafo fuskarsa, “miss u more son Allah ya maka albarka kuje yanzu kam, karku makara uhum?”

Ɗaga kai Ubaidullah yayi, sannan ya saki Mama ya juya ya koma wajan su Anty Ummu da suke tsaye, Anty Ummu tana yiwa Zaidu tsiya , sai dariya yake yi yana sun kuyar da kai ƙasa yana satar kallon Na’ila, wacce suka takure waja daya ita da yar uwarta wanda da kaga alamun su kasan ƙiris suke jira su saka kuka, dama sun saba duk zuwan Yayan nasu idan zai koma sai sun masa kuka tun da yana shafe watanni kafin yazo idan kuma yazo baya wani jimawa zai koma ,idan har ya jima shine yayi 1week ya koma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button