COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Hakan kuwa akayi Ubaidullah ya juya ya kalli Abi’atu dake tsaye wacce itama kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin hayyacinta, ya ce.
“Idan har zaki iya driving motata tana can gefe akwai key a jiki, ki tuƙa kuzo dashi” ba ta iya ta amsa masa ba illa gyaɗa masa kai da tayi alamun to, sannan Safwan ya figi motar da karfin tsiya suka dauki hanyar Specialist hospital.

Da kyar itama Abi’atu taje suka shiga taja motar Ubaidullah suka mara musu baya, amma me kafin su bisu sun bace musu Abi’atu ta ce.
“Ban san fa wani asibiti suka nufa ba gashi sun bace mana”

Inna ta ce.
“To banda abunki ƴarnan ba bature ya kawo mana sauki ba, ina salularki, maza ki kira Umminki ki tambayeta kiji, haka kuwa akayi, ta kira Mamanta ta faɗa mata asibitin da suka nufa.

Cikin gaggawa aka fara karban Na’ila, kafin akazo itama aka karbi Hafiza duk akayi emergency dasu.

Ban da zirya babu abun da Ubaidullah yake yi, Adduarsa ɗaya Allah yasa kanwarsa tana raye bata mutu ba, sannan ta faɗa masa suwaye suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Baban su Safwan ne ya dafa Ubaidullah dan a lokacin har kusan karfe takwass da wani abu ya ce.
“Ɗana ba muyi Sallar magriba bafa ga kuma Isha’i, Safwan kuzo muje muyi Sallah” ya juya ga su Umma Ummi(mahaifiyar su Abi’atu) da Inna da Mama ya ce.
“Ku ma ku tashi ku kai farali sannan muyi wa yaran nan addua tun da har yanzu likitoci basu fito ba, balle mu san halin da yaran suke ciki” da to suka amsa sannan suka fita dan yin sallah mazan kuma sukayi masallacin dake cikin hospital din.

Bayan sun idar da Sallah Ubaidullah ya jima yana kwararo addua inda a karshe ya sake fashewa da kuka dan ya kasa control din zuciyarsa.

Har ila yau dai Baban su Safwan ne ya ci gaba da lallashinsa, ɗago kai Ubaidullah yayi ya kallesa ya ce.
“Alhaji ban sanka ba amma naji dadin kulawarka a garemu Allah ya saka da alkhairi”

Ɗan Murmushi yayi ya ce.
“Ba komai ɗana amma karka sake kirana da Alhaji ka kirani da Abba dan haka yarana suke kirana, kuma ina ganinka naji ka shiga raina, ba lokacin da zaka san ko ni waye bane, bari komai ya dawo dai-dai, but still ya kamata ka sani, ni maƙocine gare ku, ban jima da dawowa unguwar ba” jinjina kai kawai Ubaidullah yayi, dan ko ba komai da yayi sallah yayi addua sai yaji sauki a ransa.

Da haka suka tashi suka koma cikin asibitin har yanzu su Mama su na zaune jingum-jingum, Mama Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki gashi itama ba lafiyar gareta sosai ba, tunda hawan jini gareta.

Sai wajan karfe goma kafin wani likita ya fito ya cire marks din face dinsa yana sharbe gumi ya ce.
“Alhamdulillah mun samu damar ceto rayuwar dayan yarinyar kuma munyi mata allura, za a fito da ita nan da wani ƙanƙanin lokaci zata farka In sha Allah, amma ɗayar gaski……” sai yayi shuru bai karasa maganarsa ba yayinda Mama ta rintse idanunta gam zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.

Abba( mahaifin su Safwan) ya ce.
“Likita ka faɗamin halin da ƴata take ciki dan Allah?” Ubaidullah tamƙar shuka haka ya tsaya ya kasa katabus, Anty Ummu kuwa ta fashe da kuka tana cewa.
“Dan Allah likita karka ce min kanwata rasuwa tayi na roƙe ka!” cike da tashin hankali ta karasa maganar Umma itama hawaye take yi tana lallashin Anty Ummu yayinda Inna take dannar Mama, Abi’atu kuwa can gefe ta rakub’e tana kuka mai cin zuciya.

Likita yayi gyaran murya cike da tausayin ganin halin da suke ciki ya ce.
“Kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, bata mutu ba, tana raye adduar ku take bukata pls ba kuka ba, amm Alhaji ina son ganinka a office dina kai da wannan” ya nuna Ubaidullah da Safwan tun da yaga sune maza.

Da sauri kuwa suka bi likita office dinsa, cikin harzari Ubaidullah ya ce.
” na roƙeka doctor ka fadamin gaskia a wani halin kanwata take ciki karka boye min?” yana magana hawaye na ambaliya a fuskarsa dan bai san adadin kaunar da yake yiwa yan uwansa ba.

Cike da damuwa likita ya fara koro jawabi.
“A gaskiya sai dai kuyi hakuri, dan yarinyar nan fyaɗe aka yi mata, dan gaskiya idan zata rayu to sai dai wani ikon Allah ,dan gabaki ɗayan gabanta yayi damager, and a iyakar binciken mu ba Namiji ɗaya bane ya danneta mazan da suka hau kanta zasu kai biyar and she’s to young ace maza biyar sun danneta a lokaci ɗaya gata virgin ce, babbar mace ko a first nyt tana shan wahala tun da ranar da aka fara buɗata kenan, namiji ɗaya, to balle ita wannan yarinya ce karama, kuma da karfi suka shigeta, duk sun dagargaza mat…..” maganar da Ubaidullah bai jira likita ya karasa ba ya saki ihu ya kwanta kasa yana birgima.

Da sauri Abba da Safwan suka yo kansa, kuka yake yana toshe kunnuwansa dan ji yake sun gaza daukar jawabin likita.

Da kyar Abba da Safwan da likita suka ɗago Ubaidullah wanda duk ilahirin jikinsa rawa take ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe a tsaye kiƙam kana ganin su zara-zara, Abba ya share hawaye ya ce.

“Doctor yanzu miye abun yi”

Girgiza kai yayi ya ce.
“Gaskiya bazan boye muku ba, mu munyi iya yinmu sai kuma ta Allah” doctor yana gama fadi ya fice.

Haka suka tashi Abba yana riƙe da Ubaidullah, room din suka shiga tana kwance an rufeta da farin yadin asibiti fuskarta ce kawai a buɗe, wajan kasanta kuma an saka mata wani abu an rufe wajan dashi, kasa jurewa Mama tayi ta juya ta fice tana kuka.

Ubaidullah ne ya karasa jikin gadon ya kamo hannunta ya fara magana da muryarsa da bata fita.

“Na roƙe ki kanwata ki tashi ki faɗamin suwaye suka miki! ” wata norse ce ta shigo ta ce musu.
“Pls ban da hayaniya dan anyi mata alluran hutu” tana gama faɗi ta fice abunta.

Umma da Inna da Ummi suka fice, suka yi dakin da aka kwantar da Hafiza, itama an ɗaura mata ruwa, anan suka zauna aka bar Ubaidullah da Abi’atu Anty Ummu da Abba da Safwan, Abba ya ce.
“Ɗana ku zo muje gida idan yaso mu kawo abun bukata” girgiza kai Yayi alamun A’a baza shi ba, babu yanda Abba bai yiba amma Ubaidullah ya ƙi sam, Abi’atu ma tazo suje ita ma tace sam ba zata je ba, haka Abba da Safwan suka baro asibitin da sunan zasu dawo da asuba.

Haka suka zauna cirko-cirko abinci kuwa babu wanda yayi tunaninta ko ya bi ta kanta.

Da asuba da kyar Ubaidullah ya tashi ya tafi masallaci, itama Abi’atu da Anty Ummu suka nufi dakin da aka kwantar da Hafiza nan sukayi Sallar asuba aka ɗan gaggaisa sama-sama.

Ubaidullah ya dawo kenan daga masallaci zai shiga ya duba Hafiza sai yaji yo ihun Na’ila da karfi take furta kalmar.

“Innalillahi wainna ilayhirrajiun!innalillahi wainna ilayhirrajun! Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Yayana!! Mamana!! Hafizata!! Anty Ummuna!! zasu kashe! zan mutu! Wayyoo Anty Abi’atu! Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!””

Da mugun gudu Ubaidullah yayi dakin da Na’ila ke zunduma ihu ,
Duk da ihun muryarta a dashe yake, ga wani baƙin azaban da take ji yana tashi a kasanta tamƙar ana hura mata wutar dalma.

A ɗari da saba’in Ubaidullah ya shigo ɗakin ya ɗagota cikin ɗimauta ya hau mata magana.

“Kan..kanwata! Gani gani! Gani a kusa dake” Mama da Anty Ummu matsowa sukayi suka kama hannunta gam.

Sai juyin azaba take a jikin Yayanta, tambayarta ya kuma akan cewa su waye suka aikata mata haka, amma azaban da take ji ya hanata magana.

Cikin dauriya da fizgar magana ta fara magana.
“Mam..Mamana..ina Hafizata?” kasa bata amsa akayi ta ci gaba da magana, tana fizge-fizgen azaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button