COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai gadi yana ganinta ya saki murmushi, nan suka gaisa shima ya sake yi musu ta’aziyya.

Sai da Hafiza ta shiga tayi sallama Ummi ta fito daga bedroom dinta zata shiga kitchen ta ga Hafiza na Sallama, tsantsan farin ciki Ummi kasa amsa sallamar tayi da saurin tazo ta rungumi Hafiza tana cewa.

“Hafiza ke ce?” gyaɗa kai Hafiza tayi ta duka ta gaisheta, Ummi ta amsa cike da farin ciki da jin dadi.

“Ummi ni da Yayana ne mu ka zo, yace na rakosa wajan Anty Abi’atu zasu yi magana.”

Da mamaki Ummi take kallon Hafiza ta ce.
“Tooo! Ina Yayan naki yake ,shine bai shigo ba? Sai kace wani bako ai da nan da gidanku duk ɗaya ne”

Murmushi gefen baki Hafiza tayi tana kashe ido ɗaya ita kadai tasan plan din da tayi, yar uwarta ce ta fado mata a rai ana gobe zata rasu da suke hira akan cewa idan Yayansu yazo sai sun san yanda suka yi suka haɗa shi aure da Anty Abi’atu dan kuwa sun dace.

“Allah sarki! Rayuwa baki da tabbas, Sismieta nayi alƙawari ko babu ke ni saina cika wannan burin In’sha Allahu” duk wannan maganar a zuciyarta take fadi a fili kuma ta ce.

“Am uhum Ummi wai kunyarki yake ji” rike baki Ummi tayi gami da cewa.

“Lallai kam ai sai ki ce masa ya shiga ƙaramin parlour, sannan ki zo ki kira Abi’atu tana daki, dan tun jiya na kasa gane mata bansan meke damunta ba” Hafiza ta amsa da to, sannan ta fita ta kai Yayanta karamin parlour, ta dawo da sallama ta shiga bedroom din Abi’atu.

Abi’atu kwance ta lumshe ido kamar wata mai bacci, kamar a mafarki ta ji muryar Hafiza da sauri ta bude ido ta ga Hafiza a gabanta tana tsaye tana dan murmushi kaɗan-kaɗan, sake mutsintsike idonta Abi’atu tayi ta ce.

“Ko dai gizo take min ne?”

Hafiza ta ce.
“A’a My Anty In-law ba gizo bane ni ce Hafiza ce” wani ihu Abi’atu ta saka wanda harta Ummi dake kitchen sai da ta tsorata, dirowa a gadon Abi’atu tayi ta zo ta rungume Hafiza har da kwallanta na farin ciki, Ummi ta shigo da sauri tana cewa.

“Abi’atu lafiya kuwa? wannan wani irin ihu ne haka? Duk kin cika gida?”

“Ummi wallahi ita ce ta fara magana.”

“Mtsww! Amma dai ke kam Allah ya shiryeki maimakon kiyi hamdala sai ki saki wannan kara haka, ai mun fara gaisawa da ita kafin ta shigo wajanki, hamdala za ki yi ba ihu ba”

“Wallahi Ummi bansan nayi ihun ba, murna ce ta saka ni yi” Ummi tayi murmushi ta fice tana cewa idan kun gama dai karku manta kun bar mutum a parlour.

Zama suka yi Hafiza ta ce.
“Shine kika gudu ko?”

Shuru Abi’atu tayi ta ce.
“Aa ba guduwa nayi ba , akwai aikin da nake yi ne shiyasa baki ganni nazo ba”

“To tashi muje Yayana ne yace na rakosa wajanki.”

Zare ido Abi’atu tayi da mugun Mamaki take kallon Hafiza, ganin haka yasa Hafiza ta miƙe ta ce.

“Ki kawo masa abun sha ki same mu a ƙaramin parlour” tana gama fadi ta fice, Abi’atu jiki ba kwari ta tashi ita ma tayi hanyar kitchen.

Da sauri Hafiza tayi wajan Yayanta, dan karya kwafsa mata dan tasan zai aika, a yau kuma bata son tayi missing din plan dinta.

“Am Yaya ga Anty Abi’atun zuwa, Yaya karka bani kunya, karka bawa Mama kunya ka ji?” guntun tsaki Ubaidullah ya ja ba tare da Hafiza ta ji ba ya ce.

“To na ji” ya fada a takaice dan yan halin sun fara tashi.

“Am Yaya idan tazo zan tashi na baku waje sai ka bata hakurin a sirrince” da mamaki yake kallon Hafiza, shi kenan ta koyawa Hafiza kisisina.

“Um” shine abun da ya iya fadi, Hafiza zata sake magana Abi’atu tayi sallama cikin zazzaƙar muryarta wanda sai da ya daki dodon kunnen Ubaidullah, wani kamshi yaji na tashi wanda sai da ya sanya idanunsa kaɗawa suka koma ja, da sauri ya tamƙe idonsa, yana so su washe dan yanda ya ji sunyi masa ya tabbata yanzu kam sun yi ja.

Abi’atu tana shigowa Hafiza ta mike da sauri ta fice dan kar ma Abi’atu ta tsaidata.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

kun matsa ne amma banyi niyyar sakin page din ba, saboda page din baya na samu korafi ta pc akan cewa yy kadan na kara, kuma na fada muku cewa bani da tym din typing buk biyu lokaci daya

Momyn Ahlan Taku Ce????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

CIKIYA CIKIYA CIKIYA, DAN ALLAH WANDA YAKE DA BUK DINA (HALITTA DAGA ALLAH NE) PLS A TAIMAKA MIN A TURO TA MY NUMBER WLH NA RASA SHI NE SABIDA WAYATA DA TA SAMU MATSALA KWANAKI, 08165550116 PLS.

Kacokar wannan page din na mallaka muku shi halak malak, yan COLONEL UBAIDULLAH FANS, idan kun so ku hana wasu grps din karantawa ???????? ni dai ba ruwana har da yan Wattpad ma

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

page°°°°°66&70

Fitan Hafiza da yan mintuna su na zaune babu wanda ya cewa kowa komai, Abi’atu ganin darajan Mama tayi a idonta sannan ta ga girman Anty Ummu, sai kuma Ubaidullah din da ta gansa kamar Yayanta Safwan dan haka ta daure a takaice tana kau da kanta gefe tana tabe baki ta ce.
“Ina wuni?”

Yadda tayi masa gaisuwan ne ya tsaya kallonta yana jinjina iyayinta, sai da ya ɗibi kusan minti sha’biyar,har ta fidda ran zai amsa, kafin ya amsa a takaice shi ma.
“Lafiya”

Daga haka ko wanne yaja baki ya yi shuru, Ubaidullah wayarsa ya ci gaba da dannawa Abi’atu tana zaune tana jira ta ji meya kawosa, har tsawon minti talatin su na zaune ba tare da sunyi wata magana ba tun bayan gaisawar da suka yi.

    @@@@@

Hafiza kuwa parlour ta koma ta zauna tana addua Allah yasa haƙanta ya cimma ruwa, tun da burin Mama, fatan Anty Ummu ne.

Ko da Ummi ta fito daga kitchen ta ga Hafiza zaune ta ce.

“Ah Hafiza ya na ganki anan kuma? Ina Abi’atu da Ubaidullah din?”

“Su na karamin parlour Ummi, cewa ya yi na tashi na fita magana mai mahimmanci zasu yi shiyasa na dawo nan na zauna”

Jinjina kai Ummi tayi tana tunanin dama akwai abu tsakanin Abi’atu da Ubaidullah ne.

Hafiza tana nan zaune har Safwan ya shigo ya ganta ya yi mata magana, ga mamakinsa sai ya ji ta amsa ta gaishesa, shi ma farin ciki ya yi, daga haka ya zauna yana dan janta da hira tana amsa shi sama-sama har Abba ya dawo ya gan su a haka, har kasa Hafiza ta sauko ta gaishesa dan kuwa Abba maƙoci ne na gari dan ya musu halacci da rasuwar Na’ilah.

Cike da fara’a Abba ya amsa gaisuwar yana tambayarta ya jikinta ta amsa da sauki ya ce.
“ina Abi’atun taki?”

“Su na tare da Yayana a ƙaramin parlour shi ya ce na rakosa wajanta” Safwan yasa dariya cikin wasa ya ce.

“Ah Alhamdulillah! Ashe dai maganata zata zama gaskiya kenan, ga Journalist ga Army” itama Hafiza murmushi tayi Abba ya ce.

“To Allah ya sanya alkairi mu bamu da ta cewa” Ummi ta ce.

“Wallahi kam, ameen” daga haka Ummi suka wuce ita da Abba, shi ma Safwan mikewa ya yi ya ce.

“Hafiza nima zan shiga ciki na watsa ruwa.”

“To Yaya Safwan a fito lafiya” daga haka Safwan ya shige part dinsa.

Hafiza ta juya tana kalle-kalle a ranta ta ce.

“To yana ji su shuru haka? Ba dai Yaya tafiya ya yi ba? Dan zai aika, to ko naje na duba ne? Kai A’a bari na kara musu lokaci kadan mu gani tun da, da ya tafi dole Anty Abi’atu ta dawo” da wannan tunanin Hafiza ta koma ta zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button