COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

domin shiga shafinmu na Bakandamiya, danne nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

page°°°°°21&25

“Wai me kike nufi dani ne kam Rumaisa? Mena tare miki? Ya Allah ka kawo min sauki cikin lamarina, Allah ka shiga tsakanina da wa innan bayin naka,Ya Allah na kawo ƙaransu gareka,Duk abun da kike nufi ya koma kanki Rumaisa, aniyarki ta biki” cewar Ubaidullah, ya zube a kujeran parlour yana sauke ajiyar zuciya, KB da Zaidu ne suka shigo da sallama, a haka suka samu Ubaidullah cikin damuwa, zama sukayi kusa dashi Zaidu ya ce.

“My Man what’s wrong with you?”
Dogon numfashi Ubaidullah ya sauke gami da sauke ajiyar zuciya ya ce.
“Nothing !
am just feeling bad, that’s why”

Girgiza kai Zaidu yayi gami da cewa.
“No ba halin soja bane,ina lura da kai tun abun da ya shiga tsakaninka da Rumaisa na fahimci kana cikin damuwa, Ubaidullah ka sha faɗamin akan cewa duk wanda zai saka tsoro da fargaba a cikin zuciyarsa baya zama gwani haka ne?”

Lumshe ido Ubaidullah yayi gami da cewa.
“Eh hakane matsoraci baya zama gwani, Amma kaidin mata yafi kaidin shaiɗan ina yawan faɗuwan gaba wanda nima bansan dalilin hakan ba Zaidu”

numfasawa Zaidu ya yi, a tare suka dafa kafadarsa shi da KB ya ce.
“Kaƙi ka faɗa mana meya haɗaku da Rumaisa”

Sai da Ubaidullah ya gama shaƙar iska kafin ya fara basu labarin yanda sukayi da Rumaisa, riƙe baki KB yayi ya ce.
“Dole kaji ɗari-ɗari a cikin ranka amma inaso ka sani duk ba zata haifa maka ɗa mai ido ba, Ubaidullah kana tare da Albarkan Mama, Rumaisa bata isa tayi maka abun da Allah bai maka ba, sai dai idan ya fito a cikin littafin kaddaranka, to wannan babu yanda ka iya dole ka karbi kaddararka hannu bibbiyu, amma zamu tayaka da addua In sha Allahu ma babu abin da zai faru”

Jinjina kai Ubaidullah ya yi, ba tare da ya sake furta ko da kalma daya bane, KB da Zaidu ne suke hiransu amma babu bakin Ubaidullah a ciki, dan shi haka yake magana bata damesa ba, karshe ma da suka ishesa tashi yayi ya basu waje ya shige bedroom.

Zaidu ya bisa da kallo ya girgiza kai ya ce.
“Mutum sai kace mai iskokai, ga uban canza kala sai kace hawainiya, nidai bazan fasa fadi ba zanga kalar macen da zata iya zama da kai”

KB ya kwashe da dariya ya ce.
“Kai fa kace min tsab mace zata gyara Ubaidullah ya dawo saiti shine kuma yanzu kake wannan maganar? Ko kamanta kace min mace kadara ce mai tsada?”

Dariya shi ma Zaidu yayi ya ce.
“Ban manta ba, amma lamarin Abokina sai shi wallahi” nan dai suka ci gaba da hirarsu.

Ko da Ubaidullah ya shiga ya kwanta ba jimawa bacci ya kwashesa ba tare da yasani ba, su ma da suka gama abun da sukeyi suka wuce bedroom dinsu kasancewar gobe asubanci zasuyi.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Tun kiran sallar farko suka farka, wa inda basu sallah har sun shirya, nan ma sai da akayi daru da Ubaidullah shi da commander Victor wai sai dai su Ubaidullah su tafi ba tare da sunyi Sallan asuba ba sai suyi a hanya, Ubaidullah ya ce.
“Sam bai jiba bai gani ba, ko da General Of The Army ne yazo akan cewa su tafi ba tare da yayi sallah ba, wallahi sai dai a tafi abarsa, a fasa tafiyar nan dashi.

Haka kuwa suka hakura bayan sun gama shiryawa, ga barracks bus yayinda sojoji suke tsaye sun ƙame waje guda General Of The Army yana musu addua tare da tuni abun da zai kaisu kwana uku kacal ake bukata suyi su dawo, sara masa sukayi sannan suka shiga bus, General ya ce musu.
“Goodlock.”

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Tafiya suke ana hira amma ban da Ubaidullah, wanda fuskarsa jiya iyau, karshe ma wayarsa ya ɗaga ya kira Mama a lokacin karfe 9:00am sun ɗanyi nisa tun da sun fita daga garin Abuja, airpiece ya saka Mama da ta idar da Sallan walha tana lazimi taji wayarta na neman agaji, a hankali ta janyo wayar dan tasan bazai wuce ɗanta Ubaidullah bane, tana dubawa taga shine, ɗagawa tayi, tun kafin tayi magana ya ce.

“Assalamu alaykum My Momma fatan kin tashi cikin koshin lafiya? Yasu Sister’s?”

“Lafiyar mu kalau Alhamdulillah Yaya Babba Soja mazan fama, har kun kama hanya ko?”

Lumshe idonsa yayi domin idan yana waya da mahaifiyarsa, har wani farin ciki da Annushuwa yake tsintar kansa a ciki, yakan manta da damuwar da take damunsa ya fuskanci mahaifiyarsa su sha hiransu abun sha’awa da birgewa.

“Eh My Momma dan har ma munyi ɗan nisa tun da gamu nan a jos yanzu haka”

“To masha Allah Ubaidullah ya Zaidu da wanda muke gaisawa dashi din nan ma? Ubaidullah ya ce.
“KB”

“Yauwa Eh shi fatan su na lafiya ko?”

“Eh lafiyar kalau Mama ba kiji, suturun su ba?”

Mama ta ce.
“Aifa dai kam akwai surutai kala-kala dan bana ma jin maganarka sosai saboda hawaniya”

Dogon tsaki Ubaidullah yaja gami da juyawa ya kalli KB da Zaidu wanda suke zaune kusa dashi, a hasale ya ce.
“Malamai ku sararamin dan Allah, surutunku yayi over, waya nake amma saboda maganganunku yasa bana jin abun da Mama take cewa”ya karasa maganar yana mai kara jan tsaki.

Girgiza kai Mama tayi ta ce.
“Ubaidullah Allah ya shiryeka, dan Allah ka dinga sassautawa zuciyarka kana saka mata salama kaji?”

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
“To Mama In Sha Allahu ki dinga tayani da Addua”

“Addua Ubaidullah kullum a cikin yi muku nake,Allah ya shirya min ku ya muku Albarka” da ameen ya amsa yana tambayarta su Hafiza da Na’ila, Mama ta ce.
“Sunje makaranta” hira suka dan taba kafin sukayi sallama.

Anty Ummu ya kira suka sha hira, bayan sun gama ya kira Umma (mahaifiyar Zaidu) nan yaji muryan Inna sai sababi take ita dasu Afnan wanda basu gida su na makaranta abun da suka mata tun kafin su tafi shine take ta mitansa har yanzu, Girgiza kai Ubaidullah yayi a cikin zuciyarsa yace wannan tsohuwa ba dai jaraba ba, ita kullum masifa ko gajiya bata yi.

Addua Umma tayi musu dan Ubaidullah ya faɗa mata gasu a hanya, kuma dama tasan da tafiyar tasu, tun da Zaidu ya sanar da ita, bayan sun gama wayar ne Ubaidullah ya lumshe idonsa gami da jinginuwa da sit, Zaidu kallon Ubaidullah yake saboda kirkinsa, duk ji da kai irin na Ubaidullah yana son jama’a amma miskilancinsa ne yake hanasa sakin fuska, Uwa Uba zafin rai, da haka kowa ya ci gaba da hidimarsa a cikin bus babu mai kula wani, tun bayan da Ubaidullah ya daka tsawa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Ba su Ubaidullah da isa bordern Niger ba sai karfe tara na dare, su na isa ba tare da bata lokaci ba suka kai wa yan ta’addan da suka zo kamawa farmaki, yayinda suke kokarin guduwa su kuma ,amma cikin ikon Allah suka kamasu sannan suka damƙasu a hannun jami’an tsoron bakin border din.

Rundunar sojojin bakin bordern Niger sunji dadi sosai ganin aikin da suka kasa tsawon wata daya amma a ɗan kankanin lokacin da bai wuce awa biyu ba rundunar sojojin Murtala barracks na garin Abuja suka kamasu, sannan suka damƙa musu masu laifin, hakan ne yasa shugaban rundunar sojojin Niger ya bawa su Ubaidullah masauki mai rai da kuma lafiya.

Kwanansu Ubaidullah biyu a Niger sannan suka kama hanyar dawowa Abuja.

Asubanci sukayi, dan haka ana sallan isha’i suka shigo Abuja saboda gudun da suka dinga shararawa akan titi.

Masha Allah sun iso lafiya, yayinda sojoji aka taro domin tarbansu, daga ciki kuwa harda General Of The Army da matarsa da Yarsa Hanan.

San da su Ubaidullah suke fitowa a mota daya bayan ɗaya kowa sai ya sara musu, Ubaidullah shine karshen fitowa a mota, da kyar yake iya ɗaga kafarsa fuskar nan babu walwala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button