COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko da su Zeey suke yiwa Hafiza sallama da ido kawai take bin su dashi, kamar bata taba ganin su ba.

Har waje Ubaidullah ya rako su, a tare su ukun suka rungume juna cike da kewa da bakin ciki, suka shiga mota Ubaidullah yana ɗaga musu hannu har suka fita gate din gidan.

Su na fita ya koma part dinsa ya kwanta a parlour kan doguwar kujera yana tunanin da ya zame masa jiki kullum.

Mama kullum cikin addua take Allah ya sassauta mata, dan wani lokacin idan tana tunanin Na’ilah ganin abun take tamƙar ta saka film ne ya kare.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Ba su suka isa Abuja ba sai gefen magriba su na isowa Hanan ce farkon wacce ta fara taro su, tana tambayar su lafiyar Ubaidullah da kuma karin hakuri.

KB da Zeey ne kadai suka iya tsayawa bata amsa amma har yanzu Zaidu baya cikin hayyacinsa dan ji yake yanzu son Na’ilah yake sake shiga zuciyarsa, babu yadda ya iya dole ya yi hakuri ya roƙi Allah ya masa sassauci.

Sun yi waya da Ubaidullah sun isa lafiya, Allah huta gajiya Ubaidullah ya musu.

Zeey kuwa wa inda ta saka su din ga bibiyar Rumaisa da wani shiga da ficenta, direct ta wuce take tambayar su yayinda suke bata jawabi dalla-dalla.

Murmushin Nasara Zeey tayi ta ce.
“Rumaisa kin kusan ki shigo hannuna, dadin abun ma shi ciki ba a karyarsa idan tana nan dole ta bayyana idan kuma babu duk zamu gani, Captain ka kusan dawowa soon In sha Allahu” ta fada tana murmushi dan idan Zeey ta saka abu a gabanta sai ta ga karshensa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zaune suke su biyu a parlour sun yi jigum babu mai yiwa dan uwansa Magana, Ubaidullah ne ya yi sallama ya shigo amma Abi’atu ce kawai ta amsa, sab’anin Hafiza da ta bisa da ido.

Zama ya zo ya yi kusa da ita ya ce.
“Kanwata tashi mu fita muje mu ga gari ko? Kema ki zo muje” ya fada yana dan kallon gefen da Abi’atu take zaune.

Tashi tayi ba tare da tayi magana ba, ta shiga ɗaki domin ta ɗauko musu hijab din su, shi kuma Ubaidullah dakin Mama ya wuce ya same ta zaune a bakin gado, ga carbi a hannunta tana lazimi tana kallon kasan dakin.

A hankali Ubaidullah yayi sallama yazo ya duƙa a gaban mahaifiyarsa ya kamo hannunta ya ce.
“My Momma ki zo mu fita.”

“Mu fita kuma? Muje ina.?”

“Momma mu dan fita shan iska ne kawai.”

Murmushin yaƙe Mama tayi wanda yafi Kuka ciwo, ta lura Ubaidullah yana so ne ya kwantar musu da hankali ko da kuwa shi zai kasance cikin tashin hankali, ko ba komai Ubaidullah ɗana wanda kowace uwa zata yi fatan samunsa a matsayin ɗanta domin ya zama garkuwa ga familynsa.

” a’a Yaya Babba idan kuna so ku fita ne kawai kuje abun ku “

Shagwabe fuska Ubaidullah ya yi sai kace karamin yaro duk saboda Mama ta saki jiki ta zo su fita.

“Ni dai ni dai Mommana ki zo mu tafi kawai Hafiza da wannan yarinyar miye ma sunanta? Su na parlour har sun shirya dan Allah Momma karki ce a’a kizo mu fita yau kawai plssss!”

Riƙe baki Mama tayi ta dan dungure keyarsa ta ce.
“Kai Ubaidullah mai hali dai baya fasa halinsa wallahi, yanzu ƴar tawa ce baka ma san sunanta ba? Ai da a gabanta ka faɗa da naji kunya, to sunanta ABI’ATU saura kuma ka ce ka manta, duk irin kokarin da take yi a gidan nan kace baka san sunanta ba, kullum fa anan gidan take wuni tare da Hafiza.”

Dan tabe baki Ubaidullah ya yi, ya mike tsaye ya ce.
“To Mama bazan manta ba ki fito muje” yana gama fadi ya fice daga dakin ya koma parlour ya same su duk sun saka hijab su na zaman jiransa.

Fitowarsa da mintu biyu Mama ta fito itama nan suka yi waje, Ubaidullah ya kira mai gadi ya shaida masa zasu fita.

Abi’atu ta bude bayan mota zata shiga Mama ta dakatar da ita da cewa.
“A’a ƴata ki shiga gaba da Yayan ku ni da Hafiza zamu zauna a baya” ba dan Abi’atu ta so ba tayi abun da Mama ta ce dan ta lura Ubaidullah din nan dan rainin wayo ne.

Shi ma Ubaidullah din wani kallo ya aika mata da gefen ido ta tabe baki.

Mama kuwa burin da yake ranta shi ne Ubaidullah ya auri Abi’atu dan duk wanda ya samu Abi’atu a matsayin sirka yayi sa’a.

Ita kuma Abi’atu a rayuwarta ta tsani mutum mai fadin rai da daure fuska sai kace wanda ake masa wahayi da mutuwa kullum, duk da yanzu mutuwar aka yi musu, amma tun can da daga ganinsa haka yake.

Shi kuma Ubaidullah a nasa ban garen, ya tsani yarinya karama da iyayin tsiya dan a ɗan zaman da suka yi ya fahimci kamar tana da iyayi, dan shi kallon yar shekara sha uku yake mata, Abi’atu kuwa shakararta 19 ne ,kawai karamin jiki gareta sosai.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
_KUNAAAA INAAAA NEEEE ????️????️????️????️????️????️????️????️????️ MASOYANA NA HAKIKA WANDA SUKE SONA DA ZUCIYARSU BA DA BAKIN SU BA ????️????️????️????️????️ MAZA-MAZA KU HANZARTO KU GARZAYO KU NUNA MIN KAUNA, A WANNAN KARON ZAN TANTANCE MASU SONA DA GASKIYA DA KUMA SON LITATTAFAINA, GA WATA SABUWA MAI TAKEN ITA CE ZUCIYATA DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA KU NUNA MIN KAUNA TA HANYAR SIYAN WANNAN BUK DIN NAWA KU MIN KARA, AKAN FARASHI MAI SAUKI #200 HAKIKA WANNAN KARON ZAN FAHIMCI MASU SO NA DA GASKIYA ????????‍♀️????????‍♀️ KARKU MANCE NICE DAI TAKU UWAR AHLAN DA NA KAWO MUKU FITATTUN BUKS DINA KAMAR GUDU A JEJI DA KUMA SHUHADA GA KUMA WANDA KUKE KAUNA INA KAN TYPA MUKU SHI COLONEL UBAIDULLAH MASOYANA KARKU BANI KUNYA ????️????️????️ GA MAI BUKATA SAI YA TUNTUBENI TA NUMB WAYATA KAMAR HAKA 08165550116 MOMYN AHLAN KIRA KO WHATSAPP, SAI NA JIKI MASOYA NA HAKIKA????????‍♀️

Comments

   &


     Share

MOMYN AHLAN TAKU CE????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

KYAUTAR PAGE GAREKU, MY DOTER MA’EESHART AND MMN SON FADEELARH, WITH ANTYN AHLAN BLOODY SISMIETA INA YINKU SIS’S????

INSHA ALLAH MY COLONEL UBAIDULLAH FANS ZAKU JI SUNAN KU A PAGE NA GAMA IDAN NA SAMU NATSUWA KOMAI YA DAIDAITA MIN,
KYAUTA CE GARE KU MASOYANA INAYINKU DAMA SAURAN WASU GRPS DIN.????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

page°°°°°56&60

Buɗe gaban motar tayi ta shiga ta dauke kanta ta juya masa ƙeya tana kallon window mota.

Ubaidullah ji ya yi kamar ya dungure ƙeyar tata amma sai ya fuske ya ja motar suka bar gidan.

Wajan shakawata ya kai su yana riƙe da hannun Hafiza yana nunnuna mata abubuwa, wani lokaci kuma ya tambayeta kina son wannan, amma sai dai kawai ta kallesa, dan fitar da suka yin ma sake tuna mata da yar uwarta ya yi, tun da yawancin fita irin haka tare suke yi.

Yawo sosai Ubaidullah yake yi da Mama da Hafiza Abi’atu, sai wajan karfe uku ya wuce dasu gidan Anty Ummu.

Sosai Anty Ummu taji dadin ganin su sai murna take yi, Mama da Anty Ummu sun sha hira sosai yayinda Mama take faɗawa Ummu ƙudirinta na son haɗa Ubaidullah da Abi’atu aure, nan take Anty Ummu ta bada goyon bayanta ɗari bisa ɗari dan kuwa itama ta yaba da hankalin Abi’atu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button