COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallon su Ubaidullah yayi sannan ya bude bakinsa ya hankalin ya kira sunan su. “My flowers” sannan ya bude musu hannayensa da gudu suka rungumesa suka sa kuka, ita ma Anty Ummu bata san lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, hawaye ta hau yi, Ubaidullah ya sake su Hafiza ya juya yana kallon Anty Ummu girgiza mata kai yayi alamun tayi shuru, sannan yasa hannu ya goge mata hawayen,da sauri ya shige mota Zaidu ma ya shiga yaja su Anty Ummu dasu Hafiza su na ɗaga musu hannu , mai gadi ya bude musu gate suka bar gidan suka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja.

   ~~~~~~~~~

Sallah ce kaɗai ya tsaida su Ubaidullah a hanya.

Sai karfe 4:30pm su Ubaidullah motar su tayi parking a 9JA BARRACKS ABUJA.

da K,B suka fara haduwa nan Zaidu ya fito da sauri suka rungumi juna,amma kafin Ubaidullah ya fito sai da ya gama shan kamshinsa tukunna har K,B yana cewa. “wai ina guy din nan yake ne,ko bai dawo bane shi?”

Murmushi Zaidu yayi sannan ya ce.
“Amma dai inaji K,B ka manta da waye Ubaidullah ko? shiyasa bai fito a mota ba kake tambaya idan bai shaƙi kamshi ba kafin ya fito taya za a gane cewa Captain Ubaidullah Abdullahi ya dawo?”

Suka sa dariya su na tafawa, dai dai nan Ubaidullah ya zuro kafafunsa ƙasa ,fuskar nan tamau ba annuri, K,B yazo suka rungumi juna Ubaidullah yayi wani miskilin murmushi sannan suka jera har part dinsu.

Bathroom Ubaidullah ya wuce direct domin yayi fresh up bcox a gajiye yake, ya kwashi kusan 30mnts kafin ya fito daure da towel a kugunsa, juyawa yayi ya kalli Zaidu wanda ya baje a bisa katifa ya ce.

“Hey guy oya get’up kaje kayi fresh up ka samu relief, dan ni yanzu ji nake babu wanda ya fini jin dadi da nayi wanka.”

Dariya K,B yayi ya ce.
“To nifa na kasa ganewa, Abokina ai na ɗauka zaka dawo da mata amma kuma sai na ganka daga kai sai jakarka, ya haka to?”

“Mtssww hummm don’t wast u tym , ashe duk karyan banza ce da yake cewa zai yi aure yanzu”

Cike da rashin fahimta K,B yake bin su da kallo daga Ubaidun har Zaidu.

“My guy ban gane ba, fahimtar dani kamar ya karyan banza?”

“Ba gashi nan a gabanka ba, kuma yana da baki ya fada maka da kansa”

Juyawa K,B yayi yana kallon Zaidu wanda yake kwance yana aikawa da Ubaidullah harara.

K,B ya ce.
“Ni dai yanzu ka bar wannan hararan nasa ka bani labari hararan kayi masa anjima, meya faru?”

A hasale Zaidu ya miƙe zaune ya ce.
“Wallahi Yaya Captain ka kiyayeni dan ma ka samu yanzu zan dinga kiranka da suna Yaya shine kake min tsiya?”

“To ƙanina Captain Zaidu yanzu hakuri kake so na baka ko miye?”

Tashi Zaidu yayi ya nufi hanyar toilet ba tare da ya kula Ubaidullah ko K,B ba.

K,B ya ce.
“Ni fa tambaya nake yi.”

Juyowa Zaidu yayi ya ce.
“Subhanallahi wai miye haka ne kam K,B mun dawo ko gaisuwa bamu yi ba, baka je ka nemo mana abinci ba balle ruwan sha, amma zaka wani tsareni da tambayar gulma kana soja,a sojan ma first lieutenant, gaskiya na yarda da batun nan da ake cewa gulma ya koma kan maza” ya fada yana shigewa toilet, tashi K,B yayi yana dariya yana cewa.
“Ah haba dai Captain kace min yunwa ka kwaso, ai dole naje nemo muku abinci tun da Allah yasa baka dawo da matar ba balle ta girka mana muci duka kaga daga nan ma idan ka koshi kaban labari”

Murmushi Ubaidullah yayi ganin sun haɗa kansu abotan su yana birgesa, ba bakin ciki ba hassada balle kuma ƙyashi.

K,B na fita da yan mintina ƙalilan sai ga Rumaisa kamar an jefota daga sama, kafin Ubaidullah yayi wani yunkuri ta shige jikinsa tana sauke a jiyar zuciya, wani dadi ne ya ratsata a duk wani sansa na gangar jikinta, a hankalin ta hau furta kalman.
“I miss u i miss u over my lyf, pls say u miss me too?”

Da iyakacin karfinsa Ubaidullah ya ban gaje Rumaisa ta fadi kasa, sai huci yake yi shikenan ai yanzu kam ya dawo, zasu ɗaura daga inda suka tsaya.

“Oya get out!of this room Rumaisa b4 i open my eyes leave now!”

Smiling tayi kafin ta miƙe tsaye ta ce. ” never” ta sake shigewa jikinsa tana ƙokarin haɗe bakinta da nasa, sosai suka shiga kacaniya ita dashi harta kaisu ga zubewa bisa gado sannan ta kashe masa ido daya ta ce.
“Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne ka zuba idonsa ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa…”

    ~~~~~~~~

To fa mai Rumaisa take nufi da kalamanta masu zafi ga Ubaidullah?

MAH FANS ALLAH YABAKU IKON GYARAWA IDAN KUMA BA HAKA BA WANNAN SHINE LAST POSTING DINA????????

COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍????????????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: I just published “part 19&20” of my story “COLONEL UBAIDULLAH”. https://my.w.tt/jFpvO64SS4

follow me on my wattpad pls

COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????


Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

________________________

page°°°°19&20

Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne,ka zuba idonka ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa…”

Maganar da Ubaidullah yake ta nanatawa kenan a cikin ransa zuciyarsa tana masa suya, yana tunanin me Rumaisa ta shirya masa, da har take masa bazarana da kalamanta?”

tambayar da yake ta yiwa kansa kenan amma ya rasa amsarta ,wani ban gare na zuciyarsa ya ce masa. “Haba Captain Ubaidullah jarumin soja abin alfahari, karka tsorata, tsoro baya cikin ɗabi’unka, duk wata sharrinta zai koma kanta ne.”

Da wannan karfin guiwar Ubaidullah ya sake ture Rumaisa kasa wacce take kwance a jikinsa tana faman shafa masa jiki.

Ko da ya tureta bata saduda ba, ta sake tsalle ta haye jikinsa, zip din rigarta ta gaba, ta zugesa kasa take ƙirjinta ta bayyana, da karfi Ubaidullah ya rintse idonsa gami da cewa.

“Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Subhnallahi! A’zubillahi Minash’shaiɗanirrajim! Allah ka shiga tsakani da wa innan bayin naka”

A zafafe ya mike ya ware hannayensa, a lokacin Rumaisa tana shirin rungumarsa, da iya karfin ya taska mata marin da sai da ta kifu da baki ,dai-dai nan Zaidu ya fito yana fadin.

“Subhanallah My Man me zan gani haka meya faru wannan mari haka?lafiya me Rumaisan ta maka?”

Mikewa Rumaisa tayi taja zip din rigarta.

Da kyau Zaidu yake dubanta yana son gano wani abu, sannan ya juya yana kallon Abokinsa wanda ilahirin jijiyoyin jikinsa sun miƙe sun fito raɗa-raɗa, kunnensa yayi ja, saboda bacin rai da tashin hankalin.

Rumaisa ta shafo bakinta wanda yake fitar da jini tayi wata killer smiling, gefen idonta kuwa ya taro da jini, ta kallesa a fakaice ta ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button