COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

” Captain Ubaidullah , you slap me?”

“Rumaisa get out right now!”

“Humm Captain Ubaidullah, i wiil, but u will pay for this” sannan ta dauki wayarta akan dress’mirror tasa kai ta fice.

Kallonsa Zaidu yayi yace.
“wai meya faru ne kam Ubaidullah? Meya haɗaka da Rumaisa kuma?”

Kasa magana Ubaidullah yayi ban da jikinsa dake rawa kamar mazari, a haka KB ya dawo ya same su, Ubaidullah zaune bakin gado ,Zaidu na tsaye daure da towel a kugunsa, da kallon tuhuma KB ya bisu dashi , ya ce.

“Lafiya kuwa meya faru?”

“Rumaisa”

Zaidu ya bawa KB amsa da haka.

KB ya ce.
“Rumaisa dai? To meya hada su da Ubaidun?”

“Nima wallahi ban sani ba, kuma kasan yanzu ko sama da kasa zasu haɗe Ubaidullah bazai yi magana ba, mu bari ya sauko tukunna”

Cike da mamaki KB ya ce.
“Kamar ya bazai yi magana ba?”

Murmushi Zaidu yayi ya ce.
“Nasan Ubaidullah fiya da yanda nasan gadon bacci na, mutum daya ce zata iya sa Ubaidullah ya sauko MAMA ita ma sai tayi da kyar kafin ya huce”

Nan KB ya ajiye abinci tare da lemon da ya kawo musu, ya nemi guri gefe daya ya zauna, Zaidu kuma ya hau shafa mai, bayan ya gama ya saka jallabiyya shima ya zauna suka zubawa Ubaidullah ido.

har yanzu idanunsa bai washe yayi haske ba, jijjiyoyin jikinsa ma basu koma ba, babu abun da yake masa gizo sama da kirjin da Rumaisa ta bude masa, nan ya sake rintsa idonsa da karfi cike da takaicin kallon haramun da Rumaisa ta saka shi yi.

Zaidu gajiya yayi da jiran Ubaidullah ya dawo normal dan haka a sab’ule ya mike ya dauki ruwa mai kankara a karamin freezer din dake dakin nasu, ya shiga toilet ya dau karamin bowl tare da karamin towel yazo gaban Ubaidullah ya watsa masa ruwan, amma ko gizau Ubaidullah bai yiba sai kace ba ma shi bama aka watsa wa ruwan.

Sai da Zaidu ya watsa wa Ubaidullah kusan sau uku kafin ya bude baki ya saki ajiyar zuciya bakinsa yana fitar da hayaki, cike da tsoro da mamaki KB ya ware idanunsa yana kallon Ubaidullah ya ce.

“Tabɗijam tashin hankali Captain Ubaidullah anya akwai macen da zata iya zama da kai kuwa? Irin wannan zuciya haka ,harta maza na firgita inaga mata?”

Murmushi Zaidu yayi ya ce.
“Wallahi mace kadarace mai tsadar gaske duk zafin zuciyar namijin zaki da yazo gaban mace zai koma ɗan tsaƙo, kuma zaka ce na gaya maka,ai su mata matsayin su da darajar su daban yake domin su hijabai ne kuma rufin asiri garemu wawayen maza ne kawai basu san da haka ba, suka mai da mata bayi marasa daraja da galihu, to wannan idan ka duba rayuwar su bata wani albarka”

Jinjina kai KB yayi, ya ce.
“Haka ne wallahi maganar ka, gashi maza yanzu sun ƙaro wulakanci da an tabasu
Sai su ce matan sunyi yawa yo ai su ma mazan sunyi yawa tunda dayawar su su na so suyi aure amma babu halin yi”

Dariya suka kwashe dashi yayinda Ubaidullah ya buga tsaki ya tashi ya shige toilet, kusan 20mnts ya fito jikansa sharkaf da ruwa, towel ya dauka ya koma toilet din, da kallon Zaid da KB suka bi bayansa, Zaid ya girgiza kai a ransa ya ce.
“Allah ya kyauta ya sauƙaƙa maka wannan zafin zuciyar”

Bayan 5mnts ya sake fitowa ,jallabiyya shima ya saka ya kwanta ba tare da ya kulasu ba.

Zama Zaid yayi ya ce.
” am very very hungry wallahi”

KB ya ce.
“Yo to ba ga abinci a gabanka ba ai saika sunkuya”

murmushi yayi ya juya yana kallon Ubaidulllah wanda idonsa yake rufe gam kamar mai baccin wuya, amma ba baccin yake yiba kalaman Rumaisa ne yake masa guɗa a kunne, haka kawai yaji kalaman sun samu matsuguni a zuciyarsa.

Zaidu ganin yana cikin yanayin wani irin hali ne sai ya sa jikinsa sanyi, tashi yayi ya matso kusa da shi cikin sanyin murya ya fara magana.

“Haba My Man bai kamata ace mace ta firgita ka haka ba duk abin da Rumaisa ta maka zaka iya hukuntata a matsayinka na ɗa namiji, duk da bansan me ya haɗaku ba”

Sosai Zaidu ya dinga dannar Ubaidullah har ya sake,amma ba sosai ba, sai da aka kira sallar magriba tukunna suka fita izuwa masallaci bayan sun dawo suka saka kakin su na sojoji suka dauki hanyar Office din General Of The Army, da sallama suka shiga bayan sara musu da sojoji suka dinga yi.

Bayan sunyi sallama ne, Ubaidullah shine a gaba, ba zato zaji sunyi karo da wata, tayi baya baya zata fadi da sauri ya tarota da ta faɗo faffaɗen ƙirjinsa take ta sauke ajiyar zuciya ba kowa bace face Hanan yar gidan Ganeral of the army
Da sauri Ubaidullah ya matsar da ita daga kirjinsa ya gyara mata tsayuwarta bisa kafafunta, sannan ya haɗe ran nan tamau, gefe ta koma Ubaidullah da Zaidu suka ƙame su na sarawa Shugaban su, sosai General yaji dadin ya hau tambayarsu ya hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya lau, nan ya sake musu ban gajiya gami da tuna musu yau saura 1wk kacal suyi tafiya suka amsa masa da cewa eh su na sane, kafin suka yi masa sallama har sunje bakin kofa, General of the army ya ce.

“Captain Ubaidullah zan aikeka Abacha Barracks gobe wajan major Salihu”
Da ok sir Ubaidullah ya amsa suka fita da Zaidu a hanya suka haɗu da Raihana ita ma sai da ta ƙunsawa Ubaidullah haushi kafin ta kama gabanta.

Kafin su Ubaidullah su koma part dinsu sai da suka yi sallar isha’i kafin suka koma part dinsu, wayarsa ya dauka ya kira Mama suka sha hira kafin ya kira Anty Ummu suka dan taba hira sama -sama sannan sukayi sallama.

Duk yanda Zaidu da KB suka so yin hira Ubaidullah yaki dan haka suka kyalesa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Washe gari da safe bayan Ubaidullah ya shirya cikin kakinsa wanda suke matukar yiwa jikinsa kyau, ya fito ya nufi office din Ganeral ya karba sakon a hanya suka hadu da wani shi da Rumaisa bisa alamu kuma sabon Ma’aikaci ne, kuma ba musulmi bane, dan a jikin rigarsa an rubuta Sergeant Ema kallo daya Ubaidullah ya musu ya dauke kai, yayinda S Ema ya ga Ubaidullah duk sai ya sake masa kwarjini, tabbas yanda ake fadinsa yafi haka, haka kawai yaji baya kaunar Ubaidulllah.

Aiken da aka yiwa Ubaidullah Abacha Barracks direct ya wuce sai yamma ya dawo suka ci gaba da aikin su.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

After 6days

da dawowar su Ubaidullah gobe ne kuma suke shirin tafiyar su, a wannan kwana shidda Ubaidullah yayi mari yafi a ƙirga, barin ma Rumaisa, da Raihana, ita kuma Zeey bata nan sun tafi wani Course a America, gashi yanzu yan matan sun kara yawa harda wa inda ba musulmai ba duk hari suke kawo masa, a daren ana gobe zasu tafi Rumaisa ta cewa Ubaidullah.

“You know what Captain? Humm ina so ka tara hankalinka waje guda domin dawowarka daga tafiyan nan babu alƙairi a ciki za kuma ka gani”

Kasa magana Ubaidullah yayi banda uwar kallon da yake bin Rumaisa dashi har ta fice daga parlourn.

Tambayar kansa yayi wai me Rumaisa take nufi dashi ne kam.?

   @@@@@

Daga wannan page din na tsaida littafin nan zuwa nan da sati biyu.

CMMENTS

    &


         Share

By

MAMYN AHLAN MRS IS OK✍????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button