COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana fitowa yayi tozali da Zeey ta sakar masa murmushi, a zuciyarsa ya ce.
“Another trouble don come back,Oh Allah ni Ubaidullah”
Sai da yazo gaban General Tukunna ya dan sakin murmushin gefen baki, hajiya Jamila matar General sai yamutsa fuska take, Hanan kuwa ta gama mutuwa akan Ubaidullah bata san ta inda zata fara tunkarar mahaifinta ko Ubaidullah ba, ta rasa ya zatayi da Soyayyar Ubaidullah wanda kullum kara ruruwa yake a cikin Zuciyarta, gashi ta fuskanci Ubaidullah dan ji da kai da shan kamshi ne, dan duk yanda take da ji da kai Ubaidullah ubanta ne.
Nan General Of The Army ya jinjinawa kwazo da jarumta irin na su Ubaidullah sannan suka mika masa lambar yabon da suka samu daga shugaban rundunar sojojin Niger.
Sosai jama’a aka tayasu murna, masu tayasu bakin ciki ma duk sun musu,kafin suka wuce part dinsu, Zeey taso tayiwa Ubaidullah magana amma ina bata samu damar hakan ba.
Sai da suka watsa ruwa sukayi sallan Isha’i, kafin KB da Zaidu suka nemi waje suka kwanta,a lokacin Ubaidullah na tsaye jikin mirror juyowa ya yi ya kallesu yaja tsaki.
“Nifa lokaci ya yi da zaku barmin part dina ku koma naku especially kai Zaidu Mijin yarinya” ya fada maganar yana nuna Zaidu da yatsa.
Zaidu dake kwance ya tashi ya zauna yana zubawa Ubaidullah harara ya ce.
“Bazan koma ba Yaya Captain sai kazo ka mai dani”
Me KB zaiyi in ba dariya ba yana kallon draman su.
“Mtswwww! To nikam na gaji da ajiye ku a part dina, haba kowanne ku fa da nashi part din amma duk kunbi kun tare a nawa,abun haushin ma, ku kama, ku wani haye min bed dina ku barni akan kujera, tun da kunsan ni bana iya kwanciya da mutane bana son naji motsi kusa dani”
Miƙewa tsaye KB ya yi yana cewa.
“Gaskiya Ubaidu halinka akwai gyara baka son kaji motsi kusa da kai, idan kayi aure kuma fa,ko me kake nufi?”
Zaidu ya ce.
“Tambaye shi kam”
“To sai aka ce muku ni mayen mata ne kamar ku?”
“To mu ma kuma sai aka ce maka mayun matan ne?” cewar Zaidu yana haɗa rai.
Murmushin gefen baki Ubaidullah ya yi ya ce.
“Yes of course especially ma kai
Dan kafi kowa son aure da maganar aure”
Duk haɗa ran Zaidu sai da ya dara, dan maganar Ubaidullah ya basa dariya, ba kadan ba, kallonsa ya yi ya ce.
“To wa ka taba ganina da ita a barrack din nan uhum? Da sauki ai tun da aure naso kaga kuwa alamun ni lafiyayye ne”ya karasa maganar da sakin dariya shi da KB, iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya ƙulu, da haka ya fatantake su a bedroom din ya kulle yana cewa.
“Wallahi sai dai ku kwana a parlour”
Su na dariya suka wuce part dinsu, amma duk ƙura dole ce tasa suka dawo suka kwanta a parlourn Ubaidullah da niyyar gobe zasu sa a gyara nasu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da washe gari misalin karfe tara na safe Ubaidullah bayan ya dawo daga training, dan ya zame masa jiki da yayi sallan Asuba zai fita judging shiyasa jikinsa duk ya murmuɗe da ka gansa sai kayi tunani wani ɗan shekara 30 ne, amma bai kai ba.
Yana isowa kofar part dinsa ya ga su Zaidu tsaye cirko-cirko da wasu sojoji fuskar su dauke da tashin hankali, shi ma Ubaidullah a kiɗime yake tambayar su. “Meya faru?” da kyar Zaidu ya yi karfin halin cewa.
” Ubaidullah muje ana nemanka a filin taro, barracks meeting yanzun nan”
Duk faduwar da gaban Ubaidullah keyi ba shi ya hanasa juyawa cike da karfin hali da kwarin guiwa ba, dan shi dai yasan bai aikata komai ba.
Jiki a sanyaye KB da Zaidu suka rufa musu baya.
Yana isa ya samu General Of The Army tsaye fuskarsa ba annuri ya haɗe rai ,ya rikiɗe ya koma asalin sojan, a gefensa kuwa Major Shehu ne shima ransa bace,a takaice dai dik manyan sojoji fuskar su ba walwala.
Gefe ya kalla ya ga sergeant first class Ƙasimu, (mahaifin Rumaisa) a ɗayan gefen Rumaisa ce zaune sai kuka take kanta a sun kuye, cike da Jarumta Ubaidulllah ya sara musu amma babu wanda ya kallesa, dama mahaifin Rumaisa haushin Ubaidullah yake ji saboda daga zuwansa Allah ya daukaka shi, yanzu kuma ga abun da ya faru ga abun da yayiwa ƴarsa, ai dole ya wulakanta Ubaidullah ya tozarta shi.
Cikin Tsawa da ɗaga Murya General Of The Army ya juya ga Ubaidullah yana masifa yana nunasa da yatsa.
“Kaban Mamaki Captain Ubaidullah! Kayi mugun bani Mamaki! Ban taba tunanin haka daga gareka ba, kai da kake yaƙi da wanda suke yiwa Yan mata fyaɗe amma ace yau kaine kayiwa Rumaisa fyaɗe har ka mata ciki!!!”
Maganar General sai da ya girgiza duniyar Ubaidullah, ya kasa tantance a wace duniyar yake, shi yaushe ya taba kama mace ya runguma balle har ya kusanceta har ya mata ciki? Macen ma kuma Rumaisa wanda ko ɗaura masa ita akayi a kafa zai kunceta ya jefar balle har wata tarayya ya shiga tsakaninsu ya mata ciki? Innalillahi wainna ilayhirrajiun!” shine kalman da Ubaidullah yake iya nanatawa kenan ya kasa magana.
Kallonsa Lieutenant General Musbahu ya yi gami da cewa.
“Captain Ubaidullah shin da gaske kaine kayiwa Yar gidan Sergeant first class Ƙasimu ciki? Dan tace kaine Saurayinta kuma da kai take mu’amala.
Ban da juyin da kwakwalwar Ubaidullah keyi, amma ya kasa katabus, juyawa yayi yaga sojojin da suke tsaye da zaune ga Rumaisa dake kukan munafurci har yanzu, kafin kace mai Idon Ubaidullah ya rikiɗe ya koma jajur ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe tsantsaye.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
YA ALLAH MUN TUBA ALLAH KA YAFE MANA ZUNUBANMU ALLAH KA YAYE MANA CUTAT COVID19 ALLAH KASA MU GAMA DA WANNAN DUNIYAR LAFIYA AMEEN????????????????
MASOYA BOOK DIN COLONEL UBAIDULLAH,INA MAI BAKU HAKURI NA RASHIN JINA TSAWON SATITTIKA, NGD DA KAUNAR DA KUKE NUNAWA WNN BUK DIN NAWA????????????????
COMMENTS
AND
SHARE
MOMYN AHLAN✍????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
page°°°°°26&30
Jikinsa sai kyarma yake yi, Alluran Soja ya miƙe dama ya lafiyar giwa balle tayi hauka, gadan-gadan yayi kan Rumaisa yana shirin kai mata cafka, da sauri Babanta ya tare Ubaidullah ya kai masa naushi a baki nan take bakinsa ya fashe sai ga jini tare da haƙorinsa biyu sun faɗo.
Hannu Ubaidullah ya kuma kaiwa zai kamo Rumaisa Commander Victor ya sha gabansa gami da kaiwa Ubaidullah duka a ciki, zafi sosai Ubaidullah yaji amadadin ya duƙa sai ya rufe Commander Victor da duka, nan fa fili ya rikiɗe tamƙar filin yaƙi nan aka shiga kokarin riƙe Ubaidullah amma duk wanda ya tabasa zai zubar dashi kasa, hakanne ma yasa wasu sojojin suka samawa kansu lafiya ta hanyar komawa gefe suyi kallo,cakwakiya tayi cakwakiya dan Ubaidullah ya zubar da sojoji sun kai ɗari da wani abu a kasa sai kace yaje filin yaƙi, cikin zafin rai ya fara magana.
“Ni za kiyi wa Sharri! Rumaisa? Ni za kice nayi miki ciki ? Ni zaki tozarta Rumaisa? Mena tare maki da zaki min ƙazafi? Nace mai na tare miki!” yana maganar yana kai duka yana tunkarota tana ja da baya.