COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Major ya ce.
“Kuje zan san yanda za ayi” sara masa sukayi, sannan suka sa kai suka fice daga office din Major.

Su na barin office din Major hanyar guardroom suka nufa kai tsaye, su na tafiya su na tattauna lamarin, KB ya ce.
“Amma dai gaskiya wallahi Rumaisa ta cika babbar makira, ban taba tsammanin zata yiwa Ubaidullah wannan ɗanyen aikin ba”

“Hummm KB kenan wasu matan kam ai sai a hankali, kai a tsammaninka Ubaidullah zai kyaleta ne? Tab Ubaidullah bazai barta ba, sai ya koya mata hankali, shiyasa dazu da yake kokarin cafkota banyi tunanin katse masa hanzari ba, so nayi yayi mata shegiyar duka, amma sai wannan tsautsayin ta gitta, ko ba komai naji dadi da Ubaidullah ya fasawa Ubanta baki har yayiwa hakorinsa biyu sanadin zubewa kasa a cikin jama’a, kuma kasan sergeant first class Ƙasimu(mahaifin Rumaisa) ba kaunar Ubaidullah yake ba”

KB ya ce.
“Yes i know, ai naji dadi da Ubaidullah ya jibgi Commander Victor, dan kasan ba kaunarsa yake ba shima, ni na rasa me Ubaidullah ya tare musu”

“Ai na lura wa inda basu son Ubaidullah a barracks din nan su na da yawa, gashi da mahassada kuma shi ba ɗan siyasa ba, da sunan shi Soja, kai gaskiya abun yana damuna”

KB ya ce.
“Hummm Zaidu kenan sai kace baka san halin RAYUWAR BARRACKS ba? Duk nan ne fa ma tattarin HASSADA, KYASHI NUNA FIFFIKO barin ma idan mutum ya fika muƙami, ga SHARRI ga GA BA

Zaidu ya ce.
“In dai sharri ne kam na shaida tun da ga Abokina a kulle” ya faɗa maganar su na shiga wajan Ubaidullah dake tsaye ƙiƙam sai kace bishiyar itace, sallama suka masa amma da kyar ya iya amsa sallamar a cikin zuciyarsa.

Rungumansa Zaidu yayi yana buga bayansa,Ubaidullah ya fizge jikinsa,dan ransa yayi ƙololuwar wajan baci, dan ko a mafarki bai taba tunanin zai shiga halin da ya shiga a halin yanzu ba, wai yau Ubaidullah shine a guardroom? Bama zaman guardroom din bane ya harzuƙa shi ba, ƙazafin zinan da Rumaisa ta ɗora masa shine yake sake ingiza zuciyarsa ta sake dulmiyawa cikin tashin hankalin da bai misaltuwa, dan shi ya tsani zina a rayuwarsa, hawaye ne maƙale a cikin idonsa amma fir yaƙi yarda su zubo kasa, rimtse idanunsa yayi mutanen da suke filin barracks yake tunawa a gaban su Rumaisa taci mutuncinsa.

Mama zaune a bakin Gado ta ga yau Ubaidullah bai kirata ba kamar yanda ya saba kullum, dan ya kan kira mahaifiyarsa kusan sau goma a rana,hakan ma idan yana busy ne,dan shi baya haɗa Mama da kowa, dan ita ce haske kuma farin cikin rayuwarsa.

Sosai gaban Mama yake faɗuwa wanda ta rasa dalilin hakan, ga kuma wayar a hannunta tana so ta kirasa amma kuma ta kasa, saboda faduwar da gaban ƙirjinta ke yi, sai jujjuya wayar take a hannunta tana kallon wayar, zuwa can anjima tayi jahadi ta dannawa layin Ubaidullah din kira,a lokacin su Zaidu su na tsaye su na kan bawa Ubaidullah baki amma ko gizau bai yiba.

Kiran Mama ne ya shigo, wayar yana hannun Zaidu yana dubawa ya ga Mama ne,Ubaidullah kuwa daga ringingtone ya fahimci mahaifiyarsa ce, dan yasa mata ringing daban na waƙar larabawa, wanda ake cewa, HAYATI YA MAMA.

Gaban Zaidu ne faɗi ganin Mama tana kiran Ubaidullah dan bai san me zai cewa Mama ba, gashi ita ba lafiya gareta ba, yanzu ciwonta zai tashi idan tasan halin da Ubaidullah yake ciki, kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Zaidu da KB, wannan ya kalli wannan.

Har sai da Mama ta yiwa Ubaidullah 3 miss call, ana 4 ne Zaidu yayi karfin halin ɗagawa kafin nan kuma hankalin Mama ya tashi ganin Ubaidullah bai kirata ba ita tana ta kiransa bai ɗaga ba, ta shiga zullumin meya samu ɗanta.

Zaidu na ɗagawa Mama ta sauke ajiyar zuciya wanda har sai da Ubaidullah yaji, dan Zaidu ya saka wayar a hands’free ne.

Ubaidullah jin yanda mahaifiyarsa ta sauke a jiyar zuciya, yasan hankalinta a tashe yake, dan haka ya wafce wayarsa daga hannun Zaidu yasa a kunne cikin sanyin Murya Mama ta ce.

“Assalamu Alaykum, Ubaidullah fatan dai kana lafiya ko? Lafiyarka kalau?”

Hawayen da Ubaidullah yake maƙale su nan take suka zubo da yaji muryan Mama.

“Ubaidullah wai meya same ka ne kam? Ka faɗamin mana? Yanzu Ubaidu idan baka faɗamin damuwarka ba kana da wanda zaka faɗa mata sama da nine? ” duk wannan maganar cikin damuwa Mama tayi su kasancewar tasan halin ɗanta.

Kusan 10mnts su na tsaye a haka ban da Ajiyar zuciyar da yake saukewa, karban wayar Zaidu yayi yasa a kunnensa yayi sallama, Mama ta amsa suka gaisa,nan Mama ta shiga tambayar Zaidu me ya faru da Ubaidullah, cikin in’ina da inda-inda Zaidu ya ce.

“Amm Uhum humm dama Mama ba wani abu bane, matsala aka samu shiyasa,amma ba komai ki tayamu da addua komai zai zo mana da sauki”

“Adduata kullum kuna tare da ita Zaidu,sannan dan Allah ka dinga tausasan Abokinka kasan dai halinsa”

“In sha Allahu Mama, karki damu, a gaida Na’ila da Hafiza” Mama ta amsa da “zasu ji” da ga haka sukayi sallama.

Hannu Ubaidullah ya miƙawa Zaidu alamun ya basa wayarsa, ba musu Zaidu ya miƙa masa wayar ya karba,KB ya ce.
Zaid muje musan abunyi dan gaskiya bai kamata Ubaidu ya kwana a nan wajan ba shi ba mai laifi ba” Zaidu ya jinjina kai alamun eh haka ne, juyawa sukayi zasu fita KB ya waigo ya ce.
“Am Ubaidullah kawo wayarka Mu tafi dashi kasan ba a zama da waya a guardroom”

Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki da kyar yayi magana cikin kakkausar muryarsa wanda yake a dashe cikin tsawa.

“Duk Uban da ya isa yazo ya karbe min wayata daga hannuna!” ai da gudu KB ya fice yana sauke ajiyar zuciya, shima Zaidu fita yayi yana dariya ganin yanda KB ya arce da gudu.

Waje ya samesa yana tsaye dariya sosai Zaidu ke yi har yana riƙe ciki, cikin dariya ya ce.

“Haba Soja kana matsayin First Lieutenant Amma shine dan Captain ya maka muzurai shine ka fece da gudu sai kace walƙiya?”

“Uhm uhm Zaidu Ubaidullah ba kamar sauran mutane bane, ko hawainiya ba zata gwadawa Ubaidullah canza kala ba”

Nan ma Zaidu ya sake fashewa da dariya ya ce.
“Muje ko?”

“Ina yanzu zamu je to?”

“Eh to nima dai yanzu ban san inda muka nufa ba,amma inaji kawai muje Abacha Barracks wajen Major Usman muyi magana dashi ko ya kace?”
KB ya ce.
“Eh hakan ma yayi ka kawo shawara muje din kawai”

Wajan da motar su yake suka nufa zasu shiga daga bayan su suka ji kira, juyowa suka yi a tare, Raihana Hanan da Doratie ne ,tsayawa Zaidu da KB sukayi har suka iso.

Hanan yar gidan Shugaban sojoji ita ce ta fara magana.

“Captain Zaidu yanzu ya za’ayi da case din Captain Ubaidulllah? Naje na samu dadyna amma ya ƙi ya saurareni at oll,now I don’t know what can do to protect Ubaidullah” ta karasa maganar tana hawaye dan soyayyar Ubaidullah ya mata mugun kamu.

Zaidu ya ce.
“Don’t worry Hanan everything will be better OK?” ta jinjina kai, Raihana ta ce.
“Yanzu Zeey ta gama dukan Rumaisa har bata iya motsi da kyau.

KB ne ya kwashe da dariya ya ce.
“Kai Dan Allah fa? da gaske?”

Doratie ta ce.
“Seriously Rumaisa ta daku a hannun Zeey, u know Zeey She’s very strong woman”

Cikin dariya KB ya ce.
“Yes I know She’s very strong, wow gaskiya Zeey bata taba burgeni irin ta yau ba,ya zama dole nayi mata kyauta”

Doratie ta ce.
“gaskiya kam ta cancanci kyauta daga wajan Captain and First Lieutenant”

Murmushi Zaidu da KB sukayi kana suka bude mota KB na cewa.
“Bari muje Abacha barracks zamuyi magana da Major Usman ne” da ok suka amsa sannan su ma suka ci gaba da neman solution ta yadda Captain Ubaidullah zai fita a guardroom.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button