COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Ta bangaren Rumaisa kuwa hankalinta ya tash da maganganun da Zeey ta faɗa mata, kuma tasan halin Zeey zata iya sarai, kuma ko a muƙami mahaifin Zeey yafi mahaifin Rumaisa Muƙami dan shi matsayin Second Lieutenant ne, gashi ita kuma Zeey CBI ce ita wato jami’ar bincike, shiyasa Rumaisa tasha jinin jikinta gashi taci mugun duka, dan ba karamin horo Zeey ta samu ba daga wajan margayi commander Shafi’u, Uncle dinta ne kuma, Commander Shafi’u ya bawa Jami’an Sojoji ingantacciyar horo ta yanda zasu zama na kwarai su kare kansu da kasar su, dan sai mutum yasan matakin kare kansa kafin ya kare wani, a wajan wani yaƙi aka kashesa lokacin da sukaje yaƙin maiduguri nan yan boko haram suka yi masa kisan wulakanci, tun daga lokacin ba a sake samu wani jarumin Commander ba kamar shi, kuma ba a sake samun cikakken mai tsayuwa da kafarsa da zuciyarsa yayi yaƙi ba har sai da Ubaidullah yazo shi barracks din, da wannan tunanin Rumaisa ta rarrafa da kyar ta tashi tana jan kafafunta da gangar jikinta wanda suke mata tsami.
Wajan Babanta ta wuce ta same shi a office dinsa,tasa masa kuka ita ba so take a kulle Ubaidullah ba, ita so take a saka shi ya aureta idan kuma ya ƙi asan abun da za ayi masa amma a buɗesa daga guardroom.
Baban Rumaisa duk da yaga jikin ƴar tasa duk a fashe amma bai damu ya tambayeta ba, dan yasan ba zata faɗa masa ba, ya ce.
“To shaleleta je ki abunki bari naje na samu General”ya faɗa yana mai ficewa daga office din yabarta tsaye a wajan.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Ta bangaren su Zaidu kuwa sun samu Major Usman sunyi masa bayani abun da ya faru dalla-dalla kuma sosai ya fahimta ya ce.
“Gaskiya banji dadin abun General ya aikata ba, duk da Captain shi ma yayi ba dai-dai ba,but ba komai ku tashi muje can din”
Fitowa sukayi yana gaba su ba binsa a baya, kafin suje kuma an sake kirawo Ubaidullah, a secret meeting room,wanda manya ne kawai a wajan kamar su General Of The Army, General, Major General, sai Brigadier da Colonel da Lieutenant Colonel, ga Uban Rumaisa a gefe da ita Rumaisan, ga Kuma Ubaidullah Zaune a gefe.
Ko da su Zaidu suka iso bayan Major Usman ya kira General Of The Army yake gaya masa akan cewa gashi nan yazo ganinsa ne akan case din Ubaidullah,General Of The Army yake cewa Major ai gasu nan yanzu suka shiga secret meeting room su same su acan.
Su na zuwa Sojoji suka saka musu gami da bude musu kofa suka shige,sara musu Major da su Zaidu suka yi kafin suka samu wajan zama suka zauna.
General Ayuba shine wanda ya fara gyaran murya alaman zaiyi magana.
“Amm Ubaidullah am not happy with ur action,dan takanka zan fara, da hankalinka taya ka bari har hakan ta faru tsakaninka da Rumaisa,ni nasan ba akan ka aka fara wannan abun ba, but am very surprised ta yanda naka ya baza barracks din nan, yau aka fara yiwa yara fyade ne? Ko kuma yau ne mace ta fara yin ciki a barracks iye? this is the not the first time da hakan take faruwa, wasu ma basu kai Captain Ubaidullah stars ba, amma ba’a saka su a guardroom ba,duk da ba’a barsu haka ba an hukunta su, gaskiya Sir banji dadi da kuma faruwan hakan ba”
Nan Major Usman shima ya karbe maganar daga wajan General Ayuba.
“Eh tabbas maganarka haka ne Sir Ayuba bai kamat ayiwa Captain haka ba,domin shi mutum ne mai matukar amfani a wajan mu”
Brigadier Rashid ya ce.
“Duk wa innan maganganun ma basu taso ba, ya kamata muji ta bakin Ubaidullah shin da gaske ne shi yayi mata ciki ko ba shi ya mata ba, na biyu idan ma shi ya mata cikin fyaɗe ya mata ko kuma ason ranta ya kusanceta, ya kamata a dinga bawa kowa hakkinsa, dazu da abun ua faru bana nan ne da duk bata kai ga haka ba”
Lieutenant Colonel Aliyu ya ce.
“Captain Ubaidullah akwai wata alaƙa ko mu’amala tsakaninka da Rumaisa ne?”
Ubaidullah wanda tun zamansa kansa yake duƙe yana jin maganar kowa yana shiga kansa a hankalin, idonsa kamar anyi b’arin jini,ko ɗigon fari babu a idanunsa, ya ma kasa magana sai girgiza kai kawai da yake yi, ganin haka yasa Zaidu riƙe hannunsa gam ba tare da wani ya gani ba.
Tattaunawa akeyi yayinda kowa yake tofa albarkacin bakinsa,duk wata tambayar da za ayiwa Ubaidullah da kai yake amsawa,Rumasa kuwa da an tambayeta zaia karkata baki ta shankaɗa karya da ƙarairaki dan duk abun da take faɗi babu gaskiya ko ɗigo a ciki.
A karshe dai hukuncin da aka yanke shiya girgiza Ubaidullah bama shi kadai ba, harta Abokansa na Amana sun girgiza, hukuncin kuwa shine wai Ubaidullah YA AURI RUMAISA maganar da ta doki dodon kunnensa,a zabure ya miƙe yana girgiza kai gami da cewa.
“Noooo! Naverrrrr! and Everrrrr! Impossible na aureki Rumaisa wallahi bazan aureki ba!”
Nan Baban Rumaisa ya fashe da kukan munafurci yana cewa.
“To me kake Sir Captain? Kana nufin shikenan kaci banza kenan? Ka kyatawa yarinyata budurcinta kaƙi aurenta? Dan kaga ka fini muƙami? Sai ka zalunceni” ya ci gama da kukan gulma,ran Ubaidullah ya gama baci matuƙar baci, wani wawan camuƙa ya kaiwa Uban Rumaisa.
“Ni zaka yiwa Sharri !!! Yaushe nake mu’amala da yarka da har zan mata ciki!?” da kyar su Major da General da Brigadier suka banbare Baban Rumaisa daga hannun Ubaidullah.
A fusace General Of The Army ya miƙe dan Abun da yake haɗa shi da Ubaidullah kenan saurin zuciya duk da hakan shine dai-dai a matsayinsa na Soja magana yake cikin bacin rai, kuma yawancin mutane an yarda da Baban Rumaisa da ƴarsa ga kuma wani Video wanda aka haɗa Ubaidullah da Rumaisan da wanda tayi ranar da ya wanketa da mari,shi har ga Allah bai san lokacin da tayi wannan video ba.
” Captain Ubaidullah ya zama dole ka auri Rumaisa, idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci mai tsanani gobe idan Allah ya kaimu” General Of The Army yana gama fadi ya fice, yayinda Brigadier ya bada Umarnin kar a sake a mai da Captain guardroom, da haka kowa ya watse, tashi Ubaidullah yayi da Sauri Zaidu da KB suka bi bayansa.
Bai tsaya a ko ina ba sai part dinsa, gashi duk inda yasa kafarsa sai an nunasa da tsaya ana gulmarsa, da ya juyo kuma kowa zai kama bakinsa,wannan ne ya saka hassala shi,ganin yanda lokaci ɗaya mutuncinsa ta zube.
Zubewa yayi akan gadonsa ya kifa kansa da pilo ya lumshe ido sai hawaye shar-shar, tabbas army shine burinsa amma ya zama dole ya ajiyeta idan ba haka ba Allah ne kadai yasan kalar abun da za a masa gobe, a haka Zaidu suka shigo suka samesa su ma hankalinsu a matuƙar tashe.
Zama sukayi gami fa dafasa amma sai ya miƙe ya nufi toilet ya watsa ruwa yayi alwala sukayi jam’in sallar la’asar bayan sun idar ya ɗaga wayarsa ya dannawa Mama kira, cikin sanyin jiki Mama ta ɗaga wayar saboda haka yau ta wuni bata jin dadi ga mummunar faduwan da gabanta keyi, gashi bata saba baccin rana ba, amma sai da tayisa yau, tare da mummunar mafarki.
Sallama Ubaidullah ya mata ta amsa lokacin Hafiza da Na’ila su na zaune a gefenta, Mama ta ce.
“Ubaidullah fatan lafiya kake ko?”
Da kyar ya tattaro jarumta yayi murmushi mai sauti ya ce.
“Eh My Momma am fyn,ina nan dawowa gida gobe idan Allah ya kaimu”
Dam!dam! Gaban Mama da Zaidu da KB suka bada ware ido sukayi su na kallon Ubaidullahi.
“Lafiya kuwa zaka dawo gida Ubaidullah?”
“Eh My Momma lafiya sai nazo” ya katse wayar.