COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

yayin da major general yake jawabi cikin harshen turanci, akan jaruman da barracks ke ji dasu za a tura ,amma kafin nan za,ayi ƙarin girma ga wa’inda suka je yaƙin maiduguri,
Lieutenant general ne ya karbi jawabin daga hannun major general ya ɗora,da nasa akai.
Mutum na farko daya lashe takwabin girma mai tambari shine…!!ehem ehem! first lieutenant Ubaidullah wanda a yanzu zai karbi matsayin, CAPTAIN UBAIDULLAH,nan jami’ai, aka hau tafa masa ji kake rab! rab! bayan anyi wa Ubaidullah ƙarin girma, shima Zaidu matsayin captain aka bashi, K,B kuma a tym din aka basa ,matsayin first lieutenant ,daga nan aka cigaba da rabon muƙamai.
Ba a watse ba kuwa, sai da aka kira sallar magriba tukunna musulmai sukayi masallaci sai da suka idar, yan’9ja barracks suka koma.
A gajiye suka shiga part dinsu.
” Zaidu yace oh Allah ƙarin girma babu gayyata sai dai kawai gayyar sojoji? ai da an bari iyayen mu da yan uwanmu sunzo kafin ayi mana ko dan bamu da mata ne? Ko kuma,mu bamu kawo iyalan mu barracks ba?”
K,B ya kwashe da dry yace “Zaidu kenan yanzu kai a tunanin ka, ka kai aure ?”
” ai abun ne yazo ba shiri shiyasa kuma kaga nan da wata daya ne zamu tafi border gashi naji major general yace gobe zamu fara sabon training,amma kusan Allah commander victor bai so wannan ƙarin girma da a kayi ba, daka kalli kwayar idonsa zaka hango baƙin ciki da hassada ƙarara.”
“Wlh K,B ka kiyaye ni! Cewar Zaidu, ni zaka kalla kace ban isa aure ba?” Wani dry Ubaidullah ya kwashe dashi,sai da suka dan tsorata su na kallon sa.
“Ubaidullah wannan dry haka?” cewar Zaidu.
K,B yace “ina kuwa lafiya mutum sai kace mai iskokai.”
“No wlh hirar taku ce ta ban dry ,kunsan ai ni dry bata cikin manner dina “
Zaidu yace “dama kai kam dryr ka ,sai dai kana gida,ko kuma kana tare damu.”
“But nifa wlh hassadar commander victor bai dame ni ba,tunda hassada a barracks ba yau farau ba,and bazai zama karshe ba, so just 4get about this matter,mu fuskanci yin gaban kanmu dan yanzu mun sake zama manya, captain ai ba wasa ba,muna tafiya yaran mu su na bin mu a baya.”
Ubaidullah yace “b4 mu tafi i need to go home,I want to see my momma and my lovely sister’s.”
Zaidu yace ” ok when are u going?”
A takaice Ubaidullah yace, “next week In’sha Allah.”
“When did u come back?”
Sai da ya ɗauki som minute kafin yace “5days.”
Zaidu yace ” zan bika mu tafi tare sai mu dawo, but kasan fa, sai mun samu permission daga wajan, GENERAL OF THE ARMY.”
Ubaidullah yace
“eh nasani.”
K,B ne yace.
” kenan ni kadai zaku barni?”
“Hahaha my guy kaima ka shirya kawai kaje ganin gida,amma seriously da mun dawo aure nake so wlh.”
Girgiza kai Ubaidullah yayi, yace mayan aure kawai,ku tashi muje sallah, tashi sukayi suka fito atare,sukayi hanyar ma sallaci
WANENE UBAIDULLAH?
×××××××××××××
Sharhin ku ne zai sa mu cigaba ko mu dakata……!!!! Domin fahimtar littafin ya muku ko bai muku ba
COMMENTS
&
SHARE
BY MOMYN AHLAN✍????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????
Alhamdulillah! ina qara godewa Allah a ko da yaushe, salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W, da iyalan gidansa da sahabban sa, da ma goya baya har izuwa ranar sakamako.????????
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy.????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
page°°°°3&4
UBAIDULLAH ABDULLAHI GALADIMA.
Shine asalin cikakken sunansa, haifaffen garin Bauchi ne, ya kasance maraya Mahaifinsa tsohon Soja ne.”
Ubaidullah tun yana yaro yake sha’awan aikin soja, sakamakon ganin yanda mahaifinsa yake ɗebi ba ɗaɗi da yan ta’adda.
Su hudu ne rak awajan Mama mahaifiyarsu, Ubaidullah shi ka
ɗai ne namiji, shi ne na biyu, Anty Ummu ita ce babba, sai ,Ubaidullah,Hafiza,Na’ila.
“Tun Ubaidullah yana da shekara goma a duniya Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, a wani yaƙin garin jos da a kayi, aka kashe mahaifinsu, sunyi kukan rashi a lokacin da aka shigo musu da gawar Baba, wanda a lokacin yake riƙe da matsayin commander na sojoji, Baba ya taka muƙamai da dama a aikin soja, bayan rasuwar Baba komai ya dagule musu, domin a lokacin sun ga jarabawan rayuwa.
Abinci ma gagararsu yake yi, Mama tayi kuka harta godewa Allah, a lokacin kuma su hafiza su na yara, dan Hafiza shekararta biyar Na’ila kuma tana da shekara hudu, Ummu kuma tana da shekara goma sha takwas. Dan tsakanin Ubaidullah da Ummu ratan shekara takwas ne, Ubaidullah kuma yana bawa Hafiza shekara biyar harda rabi,
tsakanin Hafiza da Na’ila kuma ratan shekara daya ne, shiyasa suka taso kansu daya.
Sun sha matukar wahala kafin Mama data ga zaman ba zai yuwu ba, ta koma toya kosai a bakin kofar gida, domin a cikin dangin Ubansu Ubaidullah babu mai taimaka musu, a lokacin da Baba yake raye kuma kullum zaka gansu sunzo suna bin su, su na jan su a jiki kamar da gaske, amma tun da ƙasa ya rufewa baba ido shikenan suka ɗauke kafarsu, babu wanda ya sake tako kafarsa izuwa cikin gidan balle ya kawo musu ko da ƙwayar marasa ce.
Mama tasha wuya ba ka ɗan ba wajan kula da yaranta, Ubaidullah ganin burinsa bazai cika bane ya sa shi zuwa wajan ƙanin mahaifinsa domin ya taimaka masa, amma abun mamaki sai ya koreshi, Ubaidullah yana da matuƙar zuciya tun a lokacin yaci Alwashi akan burinsa, sannan ko zasu mutu bazai sake taka kafarsa ba izuwa wajan dangin mahaifinsa ba.
Da wannan Alwashin Ubaidullah ya ba zama neman aiki, yana ɗan shekara goma a lokacin amma ba labari, dan haka ya fara aikin cire yashi sai ya siyar, da haka ya koma makaranta, a wajen ne kuma suka hadu da amininsa Zaidu.
Ya na da shekara goma shabiyu ya koma aikin karfi wato buga block, tun Ubaidullah yana ƙarami amma ɗamtsensa duk sun fito sakamakon aikin karfin da yake yi.
Rayuwa kenan har Ubaidullah ya zo ya hana Mama toya Kosai, har ya fara biyawa ƙannansa kudin makaranta, ya biya nasa ya biya nasu.
A lokacin da aka tashi bikin Anty Ummu, Mama tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda ba kudin da zata yiwa ‘yarta kayan ɗaki, inda a karshe Mama taci bashin kudi har dubu ishirin awajan wata mata, ashe kudin nan zai zama tashin hankali.
Bayan biki mata ta dinga rashin kirki wa Mama tana gaya mata baƙaƙen maganganu, ran Ubaidullah ya baci dan ya tsani abun da zai batawa mahaifiyarsa rai, dan tun bayan rayuwar Baba Mama ta kamu da cutar hawan jini.
Kudinsa daya tara zai biya kudin makaranta ya ɗauka ya bayar,dan bazai jure ganin hakan ba.
“Ubaidullah yana da shekara sha biyar a lokacin kuma yana ɗan zuwa training jikinsa duk ya murɗe, wata ranar laraba suka buga ma wani babban mutum block sannan suka masa aiki, nan ya mai dasu kamar yaransa, sosai kuma yake jindadin aiki dasu.