COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Yana katse wayar suka hau rige-rigen tambayarsa.
“Ubaidullah me kake nufi da zaka koma gida gobe? Aikin naka kuma fa? Dan Allah karkayi haka,hakika al’umma su na bukatarka a cikin jami’an Sojoji ,dan Allah Ubaidullah karka aikata abun da kake shirin aikatawa, barracks tana bukatarka”
A hasale Ubaidullah ya ce.
“Karya ne! Barracks bata bukatata Zaidu KB karku yaudari kanku, dukkanmu abun da muka sanine a fili zai biyo baya gobe dan ko sama da kasa zasu hade ne na rantse da Allah bazan auri Rumaisa ba, idan kuwa haka ne,gwanda tun da sauran ɗan guntun mutunci ne na ajiye aikin da kaina kafin amin koran kare, wanda idan hakan ta faru zan tsani aikin soja, kuma ni bazan so na tsani aikin soja ba, saboda burinane tun ina ɗan karamin yaro na gaji mahaifina, ko ba komai alhamdulillah na cika burina na aikin soja, nayi yaƙi da jinina da lafiyata , hakan ma na godewa Allah, wannan jarabawatace ina adduar Allah ya bani ikon cinyeta, ku tayani da Addua Allah ya baiyanar da gaskiya dan bana so na mutu da tabon zargi a idon mutanen dake wannan nahiyar” Kawai Ubaidullah ya fashe da kuka,nan take shima KB ya fashe da kuka,cikin ɗauriya Zaidu ya ce.
“Ubaidullah u mean gobe zaka tafi bauchi?” Ubaidullah ya jinjina kai alamun eh,a zabure Zaidu ya miƙe kamar wanda aka tsikara da allura, nan suka bisa da ido wardrope Zaidu ya bude yaja akwatinsa ya hau zuba kayansa a ciki, da sauri, Ubaidullah ya mike yana riko gami da tambayarsa me yake shirin aikatawa, me zaiyi yake tattare kayansa,amma sam Zaidu ya ƙi sauraron Ubaidullah tamƙar mahaukaci haka Zaidu ya koma yana kwashe kayansa.
Da karfi Ubaidullah ya fizgosa gami da daka masa tsawa.
“What’s wrong with you Zaidu!!?”
Ɗago idonsa Zaidu yayi wanda yake cike da kwalla ya kaɗa yayi ja ya ce.
“Tafiya zamuyi Ubaidullah, ba zaka tafi kabarni ni kaɗaina ba anan, yanda muka zo tare haka zamu koma tare”ya karasa maganar yana shirin fizge hannunsa daga na Ubaidulllah zai ci gaba da kwasar kayansa, Ubaidullah ya sake fizgosa gami da cewa.
“No Zaidu karkayi haka,tabbas na san tare muka zo,amma ita aiki tamƙar rai ce ,bai zama lallai dole mu mutu tare ko lokaci ɗaya ba, dan haka ni kwanan nawa aikin ne ya kare, nasan kai din amininane na gasken-gaske, amma bazan tabbatar da kana sona tsakani da Allah ba, har sai kamin alƙawarin bazaka taba kabar aikinka ba Aminina” nan take suka fashe da kuka suka rungumi juna, Shima KB kuka yakeyi yazo ya rungumesu duka.
“Kafi gaban haka Abokina, nayi maka Alkawarin babu inda zani tunda haka kakeso amma inaso kasani rayuwar aikin soja wajan Zaidu ba zatayi dadi ba indai ba Ubaidu a tare dashi domin Ubaidu shine garkuwan Zaidu”
Murmushin Ubaidullah yayi ya ce.
“Karka damu aboki ne komai zaiyi Normal zaka saba In sha Allah, kuma ma ai ga KB ne” ya fada yana kaiwa KB naushin wasa a kafaɗa, KB ya share hawaye dan ya kasa magana, haka ranar suka zauna a bedroom su ja jimami.
Ta bangaren Mama kuwa faɗawa su Hafiza da Na’ila tayi akan cewa Yayansu Zaizo gobe, Murna suka hauyi su na tsalle,Na’ila ta ce.
“Mama ki bamu kuɗi muje nan Jahun muyi siyayyar kayan abun da zamu girkawa Yaya gobe” Hafiza ta ce.
“Eh kuma hakane Sismie kin kawo shawara Mama bamu kuɗin muje”
Murmushi Mama tayi ta ce.
“Wannan yara, to kuje ku buɗe jakata ku ɗauki kuɗin yadda zai muku” suka amsa da to suka miƙe da sauri,Hafiza taje ɗauko kudin, Na’ila kuma taje ɗauko musu hijabansu.
Mama ta ce.
“Karku jima fa kunga yamma tayi, dama kun bari sai gobe ne tun da babu makaranta”
” a’a Mama tun da mun ɗauko kudi bari muje mu dawo kawai” cewar Hafiza.
Mama ta ce .
“to a dawo lafiya driver ne zai kai ku?”
“A’a nan da Jahun din da zamu ɗan taka kawai”
“To ai Hafiza naga yamma tayi ne ai”
“Karki damu Mama yanzu zamu dawo In sha Allahu”
“To Allahu yasha adawi lafiya” suka amsa da ameen suka fice.
Tsaye take akan titi fara ce amma ba zaka ce mata sol ba domin kuwa boyeyyan haske gareta,tana da ƙaramin jiki sosai bata da tsayi kuma ba zaka ce mata gajera ba,gashi bata da ƙiba kuma ba zaka sakata alayin ramanmu ba, idan ka kalli fuskata zaka ita karantar yanayin fuskarta,tana da son fara’a dan ko a yanzu fuskarta dauke yake da murmushi ga wani farin tabarau da ta saka a idonta tamƙar doctor.
Su Hafiza ne suka zo wucewa, handbag din hannun Hafiza wani Almajiri ya fizge yana shirin ya zunduma da gudu yazo giftawa ta gaban wannan budurwan take ta saka masa kafa ya fadi sannan tayi hanzarin ɗaukar jakar yayinda Hafiza da Naila suka saka kururuwa a cikin jama’a nan aka taro akan wannan almajiri ana shirin a masa rufdugu, kuka ya fara yana bada hakuri akan cewa ba halinsa bane sata yunwace ta saka shi haka.
Nan Hafiza ta hana a dakesa sannan ta ciro dubu 2 a cikin jakar tata ta miƙawa almajirin ya karba ya mata godiya,wannan budurwan ta ce.
“Kai gaskiya kasarmu ta lalace , innalillahi wainna ilayhirrajiun! Ba dole yara kanana su fara sata ba saboda wahala Allah ya kyauta amma dole nayi rubutu na buga akan hakan” jama’ar wajan suka amsa da ameen, kafin ta mai da kallonta kan su Hafiza nan ta hango tsananin kamannin da suke da juna,murmushi ta sakar musu,haɗa baki sukayi gami da cewa.
“Mun gode Anty”
Dariya tayi ta ce.
“Sunana ABI’ATU“
Su ma dariyar sukayi.
“To Anty Abi’atu”
Ta ce.
“No ku daina cemin Anty kawai ku kirani da Sunana, baku ga tsawon mu daya ba?”
Murmushi Hafiza tayi ta ce.
“Eh hakane amma ai kin girme mu”
Ita dai murmushin tayi dan ɗabiar fuskarta ce murmushi ta ce.
“To shikenan baku faɗamin sunayen ku ba?” ta fada maganar tana kallon Hafiza.
Hafiza ta ce.
“Sunana Hafiza sismie kuma sunanta Na’ila”
Murmushi tayi ta ce.
“Nyc to meet urs, ni bakuwa ce a wannan unguwar gidan mu yana can wajan bayan masallacin sallar Jumma’a yanzu kuma na fito siyayya ne amma fa kun burgeni ku twins ne?”
“Aa mu ba twins bane ,amma ratan dake tsakaninmu ba yawa, muma gidanmu yana can wajan masallacin”
Ta ce.
“Da gaske?” suka jinjina mata kai, nan ta ce.
“To muje mu gama sai naje naga gidan ku kuma ku ga namu ko za’adinga gaisawa ko?” suka amsa da to.
Bayan sun gama siyayyar tasu sai da suka fara biyawa gidan su Abi’atun wanda gida hudu ne ma kawai a tsakaninsu kafin suka wuce gida daf da magriba.
Da sallama suka shiga parlorn Mama ta rufe su da faɗa kan cewa sai yanzu suka dawo, Abi’atu kuwa tun da ta ga Mama taji wani bala’in kunyar Mama ya kamata wanda bata san dalilin hakan ba, ga kwarniji da Mama ta mata.
Hakuri suka bata sannan suka bata labarin abun da ya faru da suka fita ,har haduwar su da Abi’atu da zuwa gidan su da sukayi yanzu.
Sai a lokacin tukunna Mama ta lura da Abi’atu wacce ra rakub’e a gefen kofar parlour, Mama ta ce.
“Sannu ko ƴata ya kike da Mamar taki?”
Zubewa kasa Abi’atu tayi tana dukar da kai kasa ta gaishe da Mama.
Take Mama taji yarinyar ta kwanta mata a rai.
Na’ila ta ce.
“Mama wannan gidan da aka ginasa kwanan nan, wanda gida hudu ne a tsakanin mu na wancan kwanar shine fa ashe gidansu”
Mama ta ce.
“Ayyo ai kuwa ranar da zanje gidan su Umma mun haɗu da Mamanki mun gaisa”ita dai Abi’atu kanta a sun kuye ta kasa sakewa.
Mama ta ce.
” ku tashi ku shiga ciki kuyi sallar magriba, sai ku kawo mata abinci da abun sha, ku kwashe wannan kayan kuma ku kaisu kitchen” suka amsa da to,sannan suka ɗibi kayan sukayi kitchen, sai da Abi’atu ta ga Mama ta shiga bedroom kafin ta sauke ajiyar zuciya, kamar ance ɗaga kanki nan ta hango ɗan wani lungu tsakiyar TV wanda lungu anyisa dan ajiye pictures, pic din da ta fara tozali dashi wanda ya haifar mata da faduwar gaba wanda harta miƙe taja gaban pic din tana kallo tana shafawa a hankali.