COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Pic din Ubaidullah ne da kakinsa na sojoji yayi matuƙar kyau duk da fuskarsa a pic din babu murmushi, dan guntun tsaki tayi dan ta tsani mutum wanda baya murmushi ya fiye haɗe rai ita ana zubin kenan.
Sake ɗaga kai tayi ta ga wanda sukayi ga Mama da Anty Ummu dasu Hafiza nan ta ga yayi murmushi sai da fararen teeth dinsa suka bayyana, itama murmushin tayi ta ce.
“Yauwa jarumin maza ko kai fa anan kafi kyau”
Gefe ta sake kalla ta gansu su biyu da kaki, a zuciyarta ta ce to wannan kuma fa ko shi da waye, bata san a fili ta faɗa ba sai ji tayi Na’ila ta ce.
“Shi da Babban amininsa ne dukkan su Sojoji ne” da sauri Abiatu ta juyo ta kallesu su na mata dariya taji kunya ya kamata ta ce.
“Lah kuyi hakuri ” ta juya da sauri Na’ila ta riƙota ta ce.
“A’a Anty tsaya ki gani, kinga wancan pic din” tayi mata nuni da wani pic a sama wanda bata ma gansa ba sai yanzu, a gefen pic din ta ƙasa anyi rubutu da jan alkalami R,I,P FATHER, gaban Abi’atu ya bada dam! Ta juya tana kallon su, taga su na share hawaye, Na’ila ta ci gaba da magana.
“Baban mu ne, shi ma kuma soja ne Allah ya masa rasuwa a bakin aikinsa na soja, kinga wannan pic din kuma, da Mama da Babbar Yayarmu Sunanta Anty Ummu, sai Yayanmu sunansa Ubaidullah sai Sismie sai ni, yanzu haka Yayan namu yana aikin sojansa a garin Abuja, wannan pic din kuma shi da Abokinsa ne wanda suka taso tare, gobe kuma idan Allah ya kaimu zaizo”
Sosai Abi’atu taji familyn ya burgeta taji kuma tana son ganin Ubaidullah ido da ido amma daga ganinsa za ayi ji da kai da miskilanci.
Hafiza ta ce.
“Muje muyi sallah fa kar Mama ta fito”
Bedroom suka shiga bayan sunyi Sallah Hafiza ta fita domin kawowa Abiatu abinci.
Abiatu ta kalli Naila ta ce.
“Sis amma Yayan kun nan yana da ji da kai ko naga baya dariya?”
Murmushi Naila tayi ta gyara zama gami da cewa.
“Yayanmu baya da ji da kai, amma ya kasance baya son hayaniya da magana, kuma yana da miskilanci, ga zuciya, amma yana da saukin kai ga wa inda suka fahimcesa suka san halinsa, yana da dadin zama domin kuwa yafi karfin Yaya shi ɗin Ubana a wajanmu har ma ga Mama dan itama da bakinta take fadi, Yayanmu yana yaƙi da abubuwa dayawa a rayuwarsa,duk yanda muka zama nagari da taimakonsa ne”
Dan murmushi Abi’atu tayi kafin ta tabe baki zata yi magana taji Hafiza na magana a bayansu wanda ta shigo dakin yanzu hannunta da tray din abinci.
“Tabbas haka ne duk abun da Naila ta faɗa miki akan Yayanmu,ba shi da girman kai, amma kuma duk wanda basu fahimcesa ba kallon mai girman kai suke masa kamar yanda ke ma yanzu na tabbata haka kike masa”
“Aa to kuyi hakuri karku min taron dangi dan da alama kuna son Yayan kun nan sosai” ta fada ta ciro wayarta ta danna video recording.
Murmushi Na’ila tayi ta ce.
“Idan har muna son shi sosai to shi kaunar mu yake, kuma ba da zuciyarsa yake sonmu ba, da ranshi yake sonmu, to idan har ya so mu da ranshi mu da me zamu so shi?”
Dariya Abi’atu tayi ta ce.
“To ai na bada hakuri, nace ayi hakuri kar a mun taron dangi a dakeni”
A tare suka sa dariya.
“Ah haba dai Anty Abi’atu taya zamu miki taron dangi mu da muke so ma idan yazo gobe ku dai-daita ayi yar gida, ko ba haka bane Hafiza?”
Hafiza wacce take dariya itama ta ce.
“Hakane kam wallahi dan sun dace”
Na’ila tana dariya ta ce.
“Allah yasa zanga bikin wayyo ni a ranar zan sha rawa bikin Yayana”
Nan dai suka ci gaba da hira kamar wanda sun jima da sanin juna, sai da akayi sallar isha’i kafin Yayan Abi’atu mai sunan Safwan yazo suka tafi gida.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
A bangaren Ubaidullah da Zaidu da KB kuka suka sha ba kaɗan ba suka taya Ubaidullah haɗa kayansa,tun a daren ya sa kayansa a booth.
Da washe gari misalin karfi goma A babban filin taro na barracks, dandazon Sojoji ne birjik yayinda, da ka ɗaga kai kaki ne ke kashe maka ido.
Ubaidullah tsaye akan Munbarin taro sanye yake da Baƙin wandon jeans da farin t-shart, fuskarsa fayau ba zaka iya gano me fuskarsa da zuciyarsa suka kunsa ba,cike da natsuwa da izza da jarumta ya fara magana cikin harshen turanci.
” Assalamu alaykum da farko ina gaida manya na, tare da abokan aiki ina yiwa kowa fatan Alkhairi, sannan ina neman gafarar wa inda na batawa a barracks din nan, ni na yafewa kowa daga ciki kuwa har wa inda suka kulla min sharri, mahaifina yasha faɗamun lokacin ina yaro kafin yabar duniya,cewa duk wanda ya min sharri na saka masa da alkairi, da babu wanda ya isa yayiwa wani abun da Allah bai masa ba, sai dai idan ya fito acikin littafin kaddararsa, dan haka na dauki kaddarata, kuma na yankewa kaina hukunci, ba lallai dole sai kun yarda dani ba, idan na faɗa kukaji ma ya biya bukata, BAZAN AURI RUMAISA BA, SABODA BANCI NANIN BA, NANIN BA ZATA CINI BA, A YAU KUMA NA AJIYE AIKINA NA SOJA.
Maganar da ya gigita su General kenan wanda ya saka su kallon Ubaidullah yayinda hankalin jami’ai sama da dubu ya tashi dan Ubaidullah garkuwa ne a barracks ba za a fahimci hakan ba sai baya nan.
Juyawa Ubaidullah yayi ya ajiye takardan a gaban General Of The Army gami da sara masa, sannan ya sarawa su Major, wa inda suke kasa dashi suka sara masa bai jira cewar kowa ba ya wuce da sauri ya bar filin taron take wasu suka fashe da kuka wasu kuma suka shiga ruɗani, wasu kuwa zuciyarsu fes.
Cikin ɗimauta Rumaisa ta miƙe da kuka, kamar ta faɗi gaskiya amma wani zuciyar ya haneta.
Zeey kuwa suman tsaye tayi na wucin gadi kafin ta juya da gudu tabi bayan Ubaidullah har ya shiga mota su Zaidu su na tsaye, da sauri ta sun kuyar da kanta ta glass tana hawaye ta ce.
“Captain am very very sorry for what happen,don’t worry i will try my best to find out true i promise, u will come back this barracks very soon”
Ta karasa, maganar tana hawaye, ta juya, Ubaidullah ya ce.
“Tnk u very much Zeey, but I don’t want to come back, don’t mind”
DA karfi ya figi Motar Sai ga Hawaye na bin fuskar Zaidu, Zeey ta ce.
“Captain Zaidu shin kuna tare dani? Zaku taimaka min mu haɗa guiwa mu gano gaskiya ko da Ubaidullah ba zai dawo ba, amma tabon da Rumaisa ta masa ya goge, shin zaku tayani?” Zaidu ya ce.
“Muna tare dake Zeey, nasan ma karya ne Ubaidullah yace bazai dawo ba dan yana son aikin soja, amma gaskiya bana tunanin ko zai dawo wannan barracks din, idan kuwa hakan ta kasance tabbas zan bar barrack din nan nima” ya na gama fadi ya juya da sauri KB ya bi bayansa Zeey ta kama gabanta domin ta fara bincike akan lamarin.
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Ta bangaren Ubaidullah kuwa yana fita ya kira Mama ya shaida mata cewa gashi nan ya taso Adduar Allah ya tsare hanya ta masa sannan sukayi sallama, ya kira Anty Ummu ya fada mata,itama ta mishi Allah ya kiyaye hanya.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Fitowa Mama tayi ta samu Hafiza zaune a Parlour ta ce.
“Hafiza wai nikam ina Na’ila ne kam tun safe ban ganta ba?”
“Wallahi nima Mama ban ganta ba ,dan tun da mukayi sallar asuba ta fice”
Salati Mama ta hauyi tana tafa hannu.
“Wato ita dai Naila ba zata taba shiryuwa ba kenan yanzu ina taje da safe dan Allah?”
Hafiza ta ce.
“Kiyi hakuri Mama bari naje gidansu Anty Abiatu na dubota” Hafiza ta saka hijab dinta ya fice.
Ko da taje Ummin Abiatu ta ce mata Naila tazo dazu amma ta tafi dan ko da tazo bata zauna ba, gida Hafiza ta dawo ta fadawa Mama, Mama ta kira Anty Ummu ko taje gidanta ne, Anty Ummu ta cewa Mama tazo amma bata jima ba ta tafi, Mama ta ce.
“To ai shikenan zanga ta inda zaki dawo ga Yayanku yana hanya idan da rabon ki sake cin wani na jakin a hannunsa ne to”