COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Naila bata dawo gida ba sai shabiyun Rana da dariyarta da shiga da sallama, Mama da Hafiza su na zaune jigum-jigum, Mama ɗago ta rufe Naila da faɗa.
“Yanzu ke Naila ba zaki yi hankali ba? Da za adinga miki magana amma ba zaki ji ba? Ace kullum a tayiwa mutum magana akan abu daya? Naila so kike sai kin kasheni da rashin jin maganarki ko? Ko maganar da kika daukowa Yayanki dani kwanaki ne bai isheki ba? Naila ina miki faɗa ne dan ki gyaru tun ina da raina kafin na mutu ki rasa wanda zai miki, kum….” maganar da Mama bata karasa ba kenan Naila ta rungumeta ta fashe da Kuka.
“Dan Allah Mama kiyi hakuri, wallahi ba yawo naje ba tun da nayiwa Yaya Alƙawari na daina ai ban sake ba, Mama ban fita a gidan nan ba fa sai wajan karfe tara, ina part din Yaya ne ina gyara masa,Idan ma baki yarda ba muje ki gani, ko kuma ki tambayi mai gadi, ko da na fita gidansu Umma naje na fada mata yau Yayanmu zaizo take tambayata akan cewa bata san da zancan zuwansu ba, nan muka sha hira dasu afnan, dana tashi shine naje gidansu Anty Abi’atu na fada mata Yayana zaizo yau, daga nan na wuce gidan Big Anty na gaya mata take cemin ta sani, to shine fa naje yelwa tsohuwar unguwarmu na fadawa Gwaggo Ladi Yaya Ubaidulllah zaizo, amma dan Allah Mama kiyi hakuri bazan sake ba” tana maganar tana kuka harda sheshsheƙ.
Mama ta ce.
“To naji kukan ya isa haka, ni dai so nake ki zama ta kwarai Naila kinga yau ace na mutu bana raye idan ba Ummu da sauran mutanen kwarai ba, babu wanda zai zaunar dake ya faɗa miki gaskiya”
“Mama dan Allah ki daina fadin zaki mutu, baba ya mutu kema kina zancan mutuwa to ina zamu saka kanmu?”
Murmushi Mama tayi ta ce.
“Ai mutuwa ta zama dole Naila ki saka hakan aranki, kullu nafsin za’ikatil maut”
Naila ta share hawayenta ta ce.
“To In sha Allahu ma zan rigaki Mutuwa Mama,dan ba zaki mutu kibarni ba” ta karasa maganar tana shiga kitchen Hafiza tabi bayanta, Mama kuwa tabisu da kallo duk tana hawaye ga faduwar gaba tana fama dashi.
Hafiza ta ce.
“Sismie yanzu dame -dame zamu fara yi?”
Juyowa Naila tayi ta kalleta sai kuma ta fashe da dariya ta rungumeta tana cewa.
“Wallahi ina sonki yar uwata Anty Hafizata” tureta Hafiza tayi tana dariya ta ce.
“Allah ya shiryeki Ke kam Naila” aikin suka fara su kwaba wannan su ajiye su hada wancan su ajiye, su na cikin yi Abiatu tazo ta hau tayasu, suka gama haɗa komai nasu, sauran kuma suka ce saiya kusan isowa tukunna sai su haɗa.
Wanka sukayi kafin suka yi sallar azahar suka fito parlour, Abiatu tayi musu sallama ta wuce gida su kuma suka zauna su na kallo Mama ta fito ta kallesu ta ce.
“Naila gashi wannan karba ki kaiwa Babanku( kanin Baban wanda unguwarsu ɗaya) Hafiza kuje ku dawo,har sun mike a tare Naila ta ce.
“Sismiena shanyawa Yayana ƙananan kayansa wa inda na wanke ki kwashe ki goge masa sannan ki shiga masa da shoes dinsa wa inda na goge bari na kai sakon na dawo yanzu saina tayaki muyi a tare”
Hafiza ta amsa da to.
Hijab dinta ta saka harta kai kofar parlour ta juyo ta kalli Mama tana dariya ta ce.
“Mamana ina sonki ki yafemin kinji? Hafiza ke ma ki yafemin”
Hafiza ta ce.
“Ke kam sai kinyi kamar zakiyi hankali sai ki sake karkacewa, ni bani hanya na wuce”
Mama ma girgiza kai tana, Naila kuwa dariya ta tuntsire dashi har sai da hakorinta suka bayyana duka sannan ta fice da gudu, Mama ta ce.
“Allahu ya shirya min ke Naila”
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Ubaidullah a hanya motarsa ta lalace da kyar aka gyara masa, yau ga wani Uban goslow a hanya sai kace haɗin baki.
Haka dai yake ta fama ya lallaba ya samu ya isa bauchi amma ina har wajan karfe uku kafin ya fita daga cikin garin jos da kyar.
A gida kuwa tun fitar Naila har izuwa yanzu bata dawo ba,Mama ta hau mita tana cewa.
“Tun karfe daya da minti ashrin na aiki yarinyar nan amma gashi yanzu har uku bata dawo ba,nan nan da gidan Baban ku?” Hafiza tace bari taje ta duba dan ita har ta gama aikin dakin Yayan nasu wanda Naila tace bari taje ta dawo suyi tare.
Ko da Hafiza taje gidan Baban nasu nan ya shaida mata da cewa shi ko mai kama da Naila bai gani ba, kafin Hafiza ta dawo sai da ta biya gidan kawayen Naila, amma wasu ma kam cewa sukayi rabon da su ganta sun kai sati, ita kuma Hafiza bata so Yayansu ya dawo ya samu Naila bata nan shiyasa ta dage da nemanta.
Gajiya da nemanta Hafiza tayi dan har gidan Anty Ummu taje da gidansu Umma(gidansu Zaidu) amma maganar ɗaya ne Naila bata zo ba,amma tazo da safe nan hankalin Hafiza ya tashi ta hau kuka.
Da kuka ta dawo gida zata shiga gate sai ga Abiatu tana tambayarta.
” ina Nailan” cikin kuka ta ce.
“Ban ganta ba duk inda ya kamata ace na duba ta ban ganta ba”
Dafe ƙirji Abiatu tayi tace muje mu faɗawa Mama asan abunyi.
Ko da suka faɗawa Mama cewa tayi.
“Naila ce fa ko kin manta halinta ne Hafiza”
Cikin kuka Hafiza ta hau girgiza kai.
“Aa Mama wallahi Naila ta canza,Duk gidansu kawayenta naje amma bata nan wasu ma kam wai sun kai sati basu ganta ba, Mama Naila ba zataje wani waje ba, bayan tasan yau Yaya zai dawo” shuru Mama tayi tana nazarin maganar Hafiza kafin taji ƙirjinta ya bada dam!dam!dam!.
Ai nan Mama ta dauki hijab suka fita neman Naila har kasuwa amma basu ganta ba, har akayi sallar la’asar amma ba Naila, nan su Afnan dasu Umma da Inna suka zo domin su ji ko Naila ta dawo amma bata dawo ba,kafin wannan lokacin Mama ta fara fita hayyacinta, ta kira Ummu ta ce tazo yanzu, nan aka sake bazama neman Naila amma shuru har da yan gidan su Abi’atu.
Ubaidullah bai shigo bauchi ba, sai karfe shidda saura,a lokacin su na tsaye jingum-jingum Ummi mahaifiyar Abi’atu tana tambayarsa shin yaga lokacin da Naila ta fita, mai gami ya ce shi bai gani ba, zata sake yi masa tambaya sukaji ihun Safwan a wajen gate, da gudu suka fito har su na tutture juna, me zasu gani.?
Wata motace baƙaƙirim ta juya da mugun gudu tabar layin motar tana shan kwana ta Ubaidullah ta yanko kwana.
A kasa kuwa Naila ce kwance jikinta ya baci da jini ko motsi batayi wani razanarniyar ƙara Hafiza ta sake, yayinda Mama tayi baya-baya tangal-tangal zata fadi ko ka ba aduba ba Naila kam fyaɗe aka yi mata, da sauri itama Anty Ummu ta saki Ihu nan unguwa ta rikice, Su Umma(mahaifiyar Zaidu) da Inna sukayi kan Naila wacce take yashe akasa wanwar.
Hannunta Inna ta kama ta ɗaga ta saki hannun ya koma nan take Inna ta fashe da kuka tana cewa.
“INNALILLAHI WAINNA ILAYHIRRAJIUN! ai babu ita ta rasu”
Jin haka ya sanya Hafiza ihun da sai da Ubaidullah yaji, shi da bai kai ga ƙarasowa gate din ba,dan shi hankalinsa yana can akan abun da ya barota a barrack ashe zaizo ya ci karo da wanda ya fita ɗimauta, da sauri ya ɗago kai yana kallo jama’a akan layin nasu, bai karaso ba ya samu gefe yayi parking, dan babu inda zai wuce da mota saboda mutane, kuma ko ba a fada masa ba ihun kanwarsa yaji Hafiza.
Cikin hanzari da tashin hankali ya parka motar ya fito.
Hafiza kuwa ihun da ta sake ta zube kasa sumammiya, Mama zubewa ƙasa tayi sharab dan ji take komai na jikinta ya daina aiki.
Abi’atu itama kan gawar Naila tayi tana ihu tana kuka yayinda Anty Ummu ta rumgume Naila gam a kirjinta tana cewa ki tashi kanwata.
Faduwan gaban Ubaidullah ne ya tsananta jin muryoyin yan uwansa gashi kuma jama’ar da suke tsaye a kofar gidan su ne, haka ya dinga kotsa kai har ya samu ya shige, turus ya tsaya yana kallon Mama tana zaune sharab jingine da gate ga Hafiza sume a ƙasa ga Naila rungume a hannun Anty Ummu da wata yarinyar da bai san taba (ABI’ATU) su na Kuka.